Labarai

Tun bayan haihuwar jakin da ta yi, mutane sun daina siyan abincinta

Matar da ta haifi jaki a farkon makon nan ta fara fuskantar kalubale iri-iri tun bayan aukuwar mummunan lamarin nan.

Dama sana’arta siyar da abinci don ta samu ta rufa wa kanta asiri, yaranta 11 kuma mijinta ba karfi gare shi ba.

Labarin haihuwar jakin ya yawata ko ina, har wasu suke tausaya mata suna taimaka mata, saidai a dayan bangaren, wasu sun fara kyamarta.

Wakilin LabarunHausa ya so tattaunawa da ita akan wannan kalubalen da ta fara fuskanta, sai dai kuma abin zai yi kama da cin fuska, hakan yasa ya tattauna da makusantanta don jin halin da take ciki.

Kamar yadda wata majiya, wacce ta bukaci a sakaya sunanta ya shaida, yanzu haka dai bata samun ciniki kamar da.

A cewarta:

“Wasu mutane sun fara kyamarta. Wasu suna ganin matsalar zata taba abincin da take siyarwa ko kuma wanda ya yi mata asirin ya yi akan kayan abincinta.

“Wannan dalilin ne yasa suka dakata da siyan abincin.”

Akwai wacce muka tattauna da ita kuma a baya kusan kullum sai ta siya abincinta, amma sai ta kada baki tace:

“Tabdijam! Jaki fa ta haifa! Ni dai gaskiya tun daga ranar da ta haifi jaki na ji ba zan samu natsuwa ba, ko da na siya abinci a wurinta.

“Saboda ina tsoron abinda zai faru da ni. Kada ya zo abinda take magana akan cewa an tura mata ya fada kan abincin da take siyarwa.”

Ta ci gaba da bayyana cewa ko wani ta ji zai siya sai ta bashi shawarar kada ya siya don gudun abinda zai kai ya dawo.

To, Allah dai yasa mu dace, ya kuma kiyaye gaba. Ameen.

 

 

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button