NAJEEB 38

Ibtisam bayan fitan Dr kwanciya tayi Tana tunani, tana nan kwance aka kawo mata abinci, wanda yasa ta tashi ta amsa ta Fara ci domin tana jin yunwa Sosai, gaba d’aya jin abincin tayi babu dad’i babu komai a ranta sai ba’kin cikin abunda najeeb ya aikata, lokaci d’aya ta saki kuka mai cin rai….. Gaba d’aya ajiye abincin tayi domin kwata kwata ya fitan mata a rai….
Dare ya tsala inda dukan wani rai ke bacci domin hutawa, ba’ajin k’aran komai sai na tsuntsaye da sauran dabbobi masu k’aran sauti, domin lokaci ne da duk wani Bil’adama yake bacci Amma banda zu’kata biyu Wanda wannan daren ya Zame musu Mai tsawo gaba d’aya Sun kasa bacci ganin lokaci suke kaman baya gudu ta gefen najeeb ba komai bane a ransa face tunanin ibtisam dana abunda Malam ya fara fad’a mishi
Gaba d’aya najeeb sai juyi yake domin tunani yake akan halin da ibtisam take ciki a halin yanzu ita da abunda ke cikin cikinta, lallai in wani abu ya samu wannan cikin bai San yanda zaiji ba, tunda yake bai taba jin son abu ba kaman yanda yake son wannan cikin na jikin ibtisam, gaba d’aya Abun yana bashi mamaki domin shidai ba mutum bane Mai son yara amma sai gashi tun Kafin a haifi abun dake cikin Nata gashi ya kwallafa rai yana son Abun, lallai dole ya saka mata ido domin muddin ta zubar Mai da wannan cikin….. Ido ya lumshe gaba d’aya ji yayi yana bukatar sanin halin da take ciki, gashi babu dama…..
Gefen ibtisam kam, babu abunda ke ranta kaman ta ganta a Nigeria ta fad’a musu sakin da yayi mata tare da abun daya aikata Bayan ya saketa, sannan ta cire wannan cikin kaman yanda ta kudiri aniyar yin hakan, sai kuma abunda ke damunta Wanda yake mata yawo akai shine yanda gaba d’aya ganin najeeb da Najwa yake ta mata yawo a ido da kuma kwakwalwarta, lallai najeeb ya cuceni, mutun mazinaci baiyi ba,….. Lokaci d’aya tace Innalillahi’wa inna ilaihirajiun, Allah yasa bai goga min wata cutar ba, sai kuma ta saki kuka tare da furta I hate you najeeb I hate you….. Ibtisam yanda taga dare haka taga Safiya domin batai bacci ba dan ta kasa yi ita
Washe gari kaman yanda Dr yace hakan akayi inda NAJEEB direct ya tafi airport gaba d’aya ya d’aukan Mata kayanta da phone d’inta, ya tafi dasu.
ibtisam kam daka asibti aka tafi da ita, kai tsaye akai cikin jirgi da ita ba tare da bata lokaci ba, kowa ya shiga jirgi inda ibtisam na zaune saiga NAJEEB wanda zai zauna kusa da ita
Zama yayi tare da kallonta
Fuskanta d’aure babu alaman dariya balle yai zaton zatai Mai magana
Najeeb yace ya jikin ki??
Banza dashi tayi ba tare da tace mishi komai ba, sai ido data lumshe wanda take shak’an kamshin turarenshi Wanda take mutuwar so
Najeeb ganin bata kulashi ba yasa ya kyaleta ba tare daya kuma ce mata komai ba
Jirgi ya d’aga inda ya sauka a garin Abuja.
Tun kafin su k’arasa mum ta turo musu driver inda suna sauka sukai Mota Bayan ansa musu kayansu a cikin motar
Kai tsaye gida sukayi inda suka tarar da family Dr d’insu na jiransu domin yaga ibtisam din, ya dubata ya gani, in hspt ya kamata taje in kuma a gida zata zauna
Mum duka kallonsu take cikin mamaki ko wanne idonshi yayi cirko cirko ya kumbura, Abun yaba Mum mamaki amma batai magana, ta daiyi shuru ta barsu
Bayan sun gaisa da mum inda Dr ya duba ibtisam yace zata iya zama a gida but Karta dinga yin aikin komai ta zauna waje d’aya ta nutsu, sannan yace maganin da aka bata a can Sun isa.
Nan Mum tayi mishi godiya sannan ya tafi
Najeeb tashi yayi tare da shiga part d’inshi kai tsaye
Bayan NAJEEB ya tashi Mum ta kalli ibtisam tace lafiya naga idonki haka?? Anya kinyi bacci kuwa?? Kodai yayi miki wani abu ne??
Ibtisam kuka ta Fara Sosai…..
Mum tace ibtisam bar kuka ki fad’amin maike faruwa, karki damu ki fad’amin komai Am with you…..
Ibtisam tace Mum NAJEEB ya sakeni…..
Mum tace what saki? Innalillahi’wa inna ilaihirajiun, garin yaya??
Nan ibtisam ta Fara bata Labarin abunda ya faru harda sex da yayi da ita Bayan ya saketa duk ta bata labari
Mum salati tai tayi tare da fad’in dama na fad’a najeeb yana shan alcohol amma Dad d’inshi yamin musu tare da yarda da k’aryan da yayi mishi
Dafo ibtisam dake kuka tayi tare da fad’in karki damu, insha Allah komai zai wuce, tashi muje kici abinci ki huta
Ibtisam tashi tayi dakyar inda suka nufi dinning mum ta zuba mata danwake Wanda tayi musamman saboda ibtisam din, Aiko nan ibtisam ta faraci kana kallon yanda takeci kasan tana jin dad’insa taci da yawa sannan ta tashi inda Mum ta kaita har d’akin zarah, saida tayi wanka sannan ta kwanta
Mum Bayan ta fita daka d’akin zarah direct d’akinta ta shiga inda ta kira Dad domin ta fad’a mishi abunda yake faruwa
Koda ta fad’a ma Dad shima Abun ya bashi mamaki tare da fad’in gobe su tawo Kano ita da ibtisam din, inda yace shima daka kaduna zai tawo ya samesu a can
Mum tace ibtisam bazata iya tafiya ba, coz cikinta zai iya fita Tana bed rest ne, sai dai in a privet jet zamu tafi
Dad yace OK, ku zauna zanyi waya da mama da kuma Umar can suje can gobe
Mum tace hakan yafi kam
Haka kam akayi kaman yanda dad ya fad’a ya kira Abba ya fad’a mishi cewa yana son ganinshi shida mama
Inda Abba yace lafiya kuwa?? Maiya faru??
Dad yace karya damu kawai sai sunzo
Najeeb tunda ya shiga part d’inshi babu abunda yake sai tunanin ibtisam, gaba d’aya magananta yake mishi yawo a Kai I hate you, I don’t want to see your face…. Da sauri yasa hannu a kunnenshi ya toshe domin baya son jin abunda kunnenshi keta jiyo mishi
Ya dad’e hannunshi na kan kunnenshi Kafin ya cire, inda ya fara tunanin abunda Malam ya fad’a mishi wanda ya samu number din malamin ne a TV sanda yake Wani lakca ana kira ana tambaya sai ya bada amsa a nan ne yaga abun ya burgeshi shine ya d’auki number d’in malamin, lallai Ina bukatar k’arin bayani akan abubuwa Sosai,…… Najeeb yana wannan tunanin bacci barawo yayi gaba dashi
Wajan karfe 9 na dare ibtisam taji tana son cin abinci dan haka dole ta tashi ta fito tare da nufin shiga kitchen ko kuma ta duba dinning
Ganin najeeb tayi zaune akan dinning ga abinci nan a gabansa amma ya kasa ci, sai juya spoon din yake, kallo d’aya ta mishi tare da kauda kanta gefe, kai tsaye dinning din ta nufa inda ta d’auki plate ta Fara k’okarin zuba abinci
Kallonta yayi tare da sauke wani irin ajiyan zuciya, yace ibtisam plz I need to talk to you
Banza dashi tayi tare da zuba abinci tayi gaba abunta
Da ido ya bita, saida ta bace mishi sannan ya lumshe ido tare da tashi ya nufi d’akin data shiga
Ganinta yayi a zaune tana tacin abinci, har zaiyi magana yayi shuru….
ita kam jin kamshin turaren da take so yasa ta d’aga kanta da sauri taga najeeb….
Wani irin tamke fuska tayi kaman bata San inda dariya yake ba
Najeeb karasowa yayi inda take, inda ya zauna a gefen gadon..
Da sauri ta tashi tsaye tare daja baya tana fad’in ka tashi ka fita, domin na tsani ganinka a r….
Janyota yayi tare dasa mata hannunshi a bakinta ya toshe mata baki, ya fara fad’in ibtisam you have to listen to me
Ibtisam tirje tirje take domin tana k’okarin ta kwaci kanta daka ri’kon da yayi mata
Ganin yanda takeyi yasa ya saketa domin tunawa da abunda Dr yace akan cikin zai iya fita
Bayan ya saketa hawaye ya Fara zuba a idonta inda ta Fara fad’in najeeb na tsaneka har abada bazan taba Sonka ba, wlh even for a minute ban son ganinka, plz am begging you just stay away from me…
Lokaci d’aya idonshi ya kad’e domin a duniya ya tsani wannan Kalman Nata, yanda take nuna Mai kiyayya, yace ibtisam am your husband so dole inzo inda kike
Tace you are not my husband, najeeb….. Sai kuma tayi shuru tana kuka…
Kokarin matsawa yayi ya kamota tace don’t touch me…..
Ido ya bita dashi tare da kallonta
Ibtisam tace najeeb am not your wife karka manta ka sakeni….. Oh na manta how will you knw that u divorce me?? Tunda kana cikin Maye…..
Ina tayaka murna ka rabu da enemy din’ka and Nima Ina taya kaina…… Kuka yaci karfinta
Shi kam NAJEEB gaba d’aya d’auke wuta yayi data furta Mai Kalman cewa ya saketa Bayan yasha giya, wani irin sarawa yaji kanshi yayi,…. Lokaci d’aya magananta ya fara mishi yawo a Kai wanda take fad’in am not your wife don’t touch me…… Kenan alcohol d’in da yasha last a America shine ya furta Kalman ya saketa?? Tunawa yayi a ranan ya ganta kaman bata da lafiya…..
Kallonta yayi tare da kamota ya rungumota yace ibtisam plz don’t tell anyone akan cewa na rabu dake bazan iya barin Uwar d’ana ta auri wani ba, plz just for our child keep this as Secret……
Da sauri ta tureshi tare da fad’in ni inada ilimi Nasan abunda nakeyi, sannan nasan abunda Allah ya hana da kuma wanda Allah yayi hani dashi, lallai Kai tarin laifin naka kullum k’aruwa yake Bayan manyan laifin da kake aikatawa shine kake Son k’ara wani? Lallai babu komai a ranka sai duniya baka tuna Allah inda kana tuna Allah Wlh bazaka fad’i haka ba, ni ba irin matan da kake bi bane, ni nasan abunda nakeyi kuma daka yau kar I…..
Yace enough ibtisam komai zai faru am still your husband and keep this on your mind yana fad’in haka ya fita Fuuuuu
Ibtisam kam ganin najeeb ya fita ranta wani irin tafarfasa yake mata, da sauri ta d’auko ledan maganinta Wanda aka bata a hspt ta bud’e su duka maganin suna da yawa ta watsa a bakinta ta shanye su duka, tana murmushi tare da fad’in nasan tunda nasha wannan maganan wannan cikin zai zube and daka ya zube shikenan kowa ya huta…….
Kabir ne zaune a office yana danna system d’inshi wayarshi ce tayi K’ara, alaman kira yana shigowa, d’auka yayi ya duba ganin Sunan hafsat yayi akan wayar
D’auka yayi tare da sawa a kunnenshi yace madam ya akayi??..
Ta gefenta tace lafiya, when zaka dawo??
Yace did you miss me ne??.
Murmushi tayi tare da fad’in alot I really miss you, and I cook your favorite food….
Tun kafin ta k’arasa yace oh I have told you, ki daina shiga kitchen kina bama kanki aiki, but baki ji abunda nace ba, kina son wahalar min da baby
Hafsat tace am sorry, kasan Mai irin Lalura na ana son ta dinga yin aiki yanda inta tashi haiyuwa zaizo mata da sau’ki
Yace but nidai banso, tunda baiyi kwari Sosai ba, and gani nan zuwa right now
Tace OK
Bayan sun kashe wayar kabir murmushi yayi domin duk wannan Abun da yakeyi yana yine domin kar Allah ya kamashi and yasan yanzu ibtisam tayi aure shima dole ya sauke hakkinshi dake kansa akan matarshi, amma so d’aya ne yaba ma ibtisam har yanzu yana Sonta Sosai, sai dai yakan ro’ki Allah akan ya cire Mai Sonta ya amshi tashi kaddaran amma Abun mamaki kullum kaman Sonta K’ara k’aruwa yake a cikin ranshi, har tausayin hafsat yake yanda take nuna Mai kulawa amma shi gaba d’aya zuciyarshi baya wajanta ko kad’an
Har yanzu zuciyarshi bata cire mishi cewan zai samu ibtisam ba, sau da yawa yakan k’okarin ya cire tunanin ta in yanayi amma ya kasa sai yasa yake keeping kanshi busy saboda baya son bata lokaci wajan tunani
Lokaci d’aya ya tashi tare da fita kai tsaye waje yayi inda ya nufi wajan motarshi ya shiga ya tada….. Tuk’i yake yana lafiya wani Mota ne yake ta mishi horn alaman ya tsaya
Kaman bazai tsaya ba, lokaci d’aya ya faka tare da fitowa, inda motar itama ta faka a gaban nashi
Wani mutumi ne ya fito cikin motar kiran golf inda ya nufi kabir din ya bashi hannu suka gaisa
Kabir yace lafiya??
Mutumin yace ai yau wajan kwana biyu inata so in ganka amma Allah baiyi ba, domin ina son fad’a maka wani abu mai muhimmanci tare da k’ara fad’a maka kayi a hankali akan mutanan da kake hulda dasu, and mutane ba Abun yarda bane, wanda bakai expecting ba sai yaci amanarka, wanda bakai tunani ba shine yaudaranka ya munafunceka….
Kabir ya Katseshi tare da fad’in wai maike faruwa ne plz fad’amin mai nene???
Mutumin yace nine wanda naje ranan daurin aurenka nace kana da HIV……
Kabir ru’ko mutumin yayi idonshi ya canza Kala….. Lokaci d’aya kuma ya saki mutumin tare da fad’in kasan Mai ka aikata kuwa!? Kasan irin laifin daka aikata kuwa?? Ka cuceni ka batamin rayuwa, har yau Ina fama da dakon son ibtisam……
Mutumin yace kayi hakuri KABIR Wlh nima sani akayi, ba komai bane ya kawo ni face in fad’a maka gaskiya domin Nima Wanda ya sani aikin ya yaudareni yaci amanata……
Yace KABIR wannan aikin ba kowa bane ya sani sai abokin ka Tahir
Kabir yace Tahir??
Wani irin kallo yama mutumin tare da fad’in karka kara mishi wannan k’azafin domin har abada Tahir bazai taba min wannan Abun ba…..
Mutumin yace Allah sarki, haka masu kyakyawan zuciya suke dama, kuna da saurin yarda, gashi ana saurin cin amanarku, Wlh Allah d’aya ne koh?? Toh Wlh Tahir yasa ni saboda yana son yarinyar, ya Turani inje ince kana da HIV domin in an fasa auren shi yace tunda hakane zai aureta sai akai rashin Sa’a go slow ya rik’eshi a hanya har aka d’aura auren yarinyar da wani
Wanda haushin wannan Abun yasa ya hanani sauran kud’in aiki na, da naga haka shine nace Zan fad’a maka gaskiya domin mu irin mu bamu da amana indai Mun ri’ke amana Toh ka bamu hakkin mu
Dan haka saika kiyaye dashi, yana fad’in haka mutumin yayi gaba abunsa
Kabir kam gaba d’aya wani irin dum yaji a kansa mamaki yake Tahir taya Tahir zai mishi haka!?? Lallai inko ya tabbata shi dinne yaci amanarshi, domin a yanda ya d’auki Tahir duk yanda yakai da son Abu Indai yace yana so zai bashi amma…… kai hannu ya d’aura a kanshi tare da lumshe ido yana jin wani irin jiri
Dakyar ya samu ya bud’e motarshi ya shiga inda ya figa da gudu Kai tsaye office din Tahir ya nufa koda ya shiga
Tahir yace a’a angon hafsat
Kabir zama yayi tare da kallon Tahir yace Mai yasa kamin haka Tahir??
Tahir yace mai ya faru??
Kabir yace Mai yasa ka zama silan da yasa aka fasa aurena da ibtisam??
Da sauri Tahir ya tashi ya fara in Ina…..
Kabir ganin haka yasa ya tabbatar shi dinne, dan haka yasa yace Tahir kaci amanar amintaka inda ka d’aukeni yanda na d’aukeka bazaka min haka ba, just saboda kana son ibtisam Wlh ni nasan Ina son ibtisam but a yanda nake jin abokantakar mu zan iya hakura, but kaci amanata but babu komai is part of experience
Tahir yace KABIR Dan Allah kayi hakuri Wlh Sharrin shedan ne, daka baya Nayi nadama, musamman da ni ban sameta ba kaima baka sameta ba, Nasan tun sanda na ganta naji Ina sonta Wlh Sharrin zuciya ne kawai tare da shaidan dan Allah kabir kayi hakuri kar wannan Abun yasa ya zama silan abunda zai had’a zumuncin mu….
Kabir yace babu komai haka Allah ya nufa nayi imani da kaddara Allah yasa ba tawa bace yana fad’in haka ya fita yabar office din Tahir
Shi kam Tahir babu komai a ranshi sai tarin nadama tare dayin dana sani da abunda ya aikata wanda bai taba jin kunya a duniya ba irin yau, lallai son zuciya ya kaishi ga halaka lallai ya biye ma zuciyarshi Wanda gashi ta kaishi dayin dana sani Innalillahi’wa inna ilaihirajiun
Shi kam kabir koda ya nufi gida kai tsaye d’akinsa ya fad’a hafsat ganin haka yasa taji wani iri domin tasan indai ya fad’a irin wannan halin to tasan yaji magana akan ibtisam ne, ido ta lumshe gaba d’aya kishin ibtisam yana cinta wanda take ganin itace tasa mijin Nata ya kasa bata wani kulawa
Kai tsaye ta tashi ta nufi d’akin kabir din amma Abun mamaki yasa ma kofar key ya rufe, alaman baya bukatar a shigo a damesa
Wani hawaye ne ya gangaro mata a ido tare da ba’kin cikin wannan rayuwa, yaushe mijinta zai cire wannan ibtisam din cikin ransa? yaushe zai daina tunaninta? yaushe zai bata cikakkiyar kulawa?
Lokaci d’aya tabar kofar d’akin tana kuka ta nufi d’akinta, lallai tana fama da son maso wani koshin wahala, ita Tana masifar son kabir amma shi ibtisam yake so
Ibtisam bayan tasha maganin duka, lokaci d’aya cikinta ya fara murdawa da ciwo Sosai kaman zata mutu, ihu ta Fara saki wanda bata san tanayi ba, domin irin azaban da takeji gaba d’aya bata san inda kanta yake ba ihu take Tana kuka hannunta nakan cikinta…..
Najeeb a tare da Mum suka zo d’akin da gudu
Koda suka k’araso tayi k’asa hannunta na kan cikinta tana kuka.
Da sauri NAJEEB ya dauketa sukai hspt da ita inda akai emergency da ita sai ihu take Tana kuka
Najeeb gaba d’aya ya kasa samun sukuni domin a furgice yake tare da fargaban mai ya sameta??
Itama Mum ta kasa zama gaba d’aya hankalinta a tashe yake
Dr dai yana ciki gaba d’aya jikin ibtisam yayi weak babu kwari
Dr yayi wajan 40 mnt sannan ya fito inda yake fad’a musu tasha magani over Wanda hakan yasa take wannan ciwon, daka duka alamu tana son zubar da cikin dake jikinta amma yanzu ku gode Allah komai normal but if she try again zata iya samun matsala domin kuwa wannan maganin da tasha yasa mahaifarta tayi weak, is better tayi hakuri harta haifi abunda ke cikin Nata….
Tunda Dr ya fara bayani idon NAJEEB ya kad’a yayi ja, lallai ya tabbatar da irin tsanar da take mishi lallai ya tabbatar tunda har Da gaske zatai yunkurin kashe abunda ke cikinta ya tabbatar zata iya kasheshi Fuuuuu ya fita daka hspt din mum na kiranshi amma ina kota ita bai bi ba Kai tsaye inda ake siyar da alcohol ya nufa inda ya siya wajan kwalba goma ya nufi gida
Koda ya k’arasa key yaba driver tare da fad’in ya koma hspt ya jira mum
D’akinshi ya shiga ranshi a bace har wani duhu duhu yake gani, bud’e bottle din alcohol d’in yayi yana k’okarin sawa a baki ya tuna da maganan ibtisam din I hate you duk wasu manya laifi ka had’a, you are drinker womanizer…. Ido ya lumshe tare da kafa kwalban a baki ya fara sha yana surutai yana fad’in even I, I hate you shan alcohol d’inshi yake kaman hauka yana surutai tare da jefar da bottle din ya fashe a d’akin a kalla yasha wajan bottle hud’u kuma duk ya fashe bottle din a d’akin lokaci d’aya ya fad’a kan bottle din a k’asa…….
Mum a asibti ta kwana ita da ibtisam wacce take a kwance har yanzu bata farka ba
Ibtisam sai wajan asuba ta farka tare da bud’e idonta Wanda yake a kumbure ta Fara kallon d’akin, ganinta a asibti ga Mum na sallah ta gane an kawo ta hospital ne, lokaci d’aya abunda ya faru ya fara dawo mata wani irin Abu taji yazo mata tare da fatan Allah yasa cikin ya zube tunda tasha magani da yawa…..
Jin muryan mum tayi tana fad’in kin tashi ne??
Ibtisam cikin dashewan murya tace eh
Ibtisam tashi tayi amma jikinta babu kwari, Mum tace Bari in taimaka miki kar abun drip din ya goce… Ko da yake bari in kira su domin naga ya kusa k’arewa ma, fita Mum tayi ibtisam taba cikinta tayi wanda ya dan Fara tashi saboda yawan cin abincin da takeyi sosai, jin alaman har yanzu yana nan yasa ta saki wani irin kuka tare da fad’in duk wannan wahalan da nasha?? Wannan wani irin jarabban ciki ne haka?? Wlh in bai fita ta sauk’i ba zanje a wanke shi ta yanda zai fita da hujja
Shigowan mum da nurse yasa tayi saurin goge hawayen idonta, nan nurse ta cire mata drip din Bayan mum ta tambaya ko akwai wanda za’a k’ara mata??
Nurse din tace a’a sai dai in dr yazo
Ibtisam toilet ta shiga inda tayi alwala tare dayin sallah, Bayan ta idar ta koma kan gadon ta kwanta wanda Tana tafiyan ne dakyar
Mum Tana zaune har Dr yazo ya duba ibtisam
Dr Ya kalli ibtisam yace ya jikin??
Tace da sau’ki
Yace ibtisam Mai yasa kika sha magani da yawa haka?? Kina son cikin ya zuba NE??
Ibtisam shuru tayi ba tare da tace komai ba, wanda ta tabbata Mum tasan komai wani irin kunya taji Sosai
Dr yace ina son in baki shawara Idan kika k’ara yunkurin yin hakan zaki iya samun matsala domin mahaifarki bata da kwari, so you have to be very careful Indai kina son rayuwarki
Nan Dr yace zata zauna na kwana biyu a nan, inda Mum tace bazasu iya tafiya gida ba
Dr yace zasu iya but tana bukatar hutu sosai, koda Kun koma Karta dinga aikin komai
Nan Mum tace shikenan inda Dr ya sallamesu suka koma Gida, koda suka isa Gida mum saida ta had’ama ibtisam ruwan dumi a cikin bath sannan tace taje tayi wanka
Bayan ibtisam ta shiga toilet mum direct d’akin NAJEEB ta shiga inda ta ganshi a k’asa ga jini dake zuba a jikinshi wani irin ihu ta saki mai firgitarwa da sauri ta nufeshi ta juyo dashi domin ta kife ya fad’i cikin mayen giyar da yasha inda ya fad’a akan kwalba Wanda ya sokeshi a cikin sa, Bayan ta juyo dashi ta Fara kuka ganin kwalba da sauri ta d’auki wayarta tana kuka lokaci d’aya ta kira Dr inda ta fad’a mishi yazo da kayan aiki kwalba ya sokar mata da a ciki
Ciki ta koma inda sai a sannan ta lura dako numfashi bayayi….. Wani irin ihu ta kurma mai ban tsoro wanda yasa ibtisam dake d’aki itama ta fito da sauri ta nufi gefen da taji ihun da yake a bud’e mum tabar kofar ibtisam itama shigowa tayi ganin halin da yake ciki yasa itama ta tsorata ganin jini a daskare Wanda da duka alama ya dad’e shine ya fara bushewa, Wanda ga wani shima yana zuba lokaci d’aya taji tana jin jiri ita dafa bangon d’akin tayi ta sulale tayi k’asa itama……..
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());