NAFEESAT Page 1 to 10

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*
*JIKAR LAWALI CE*
*Wattpad: UmmuDahirah*????
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA’S FAMILY*_
*NATSUWA A SALLAH*
_Manzon Allah mai tsira da aminci, ya ce, “sallah ba kome ba ce illa miƙa wuya da tawali’u…” Kuma ya ƙara da cewa, “Bawa bai samun ladan sallar sa sai gwargwadon abinda ya hankalta daga sallar.” Watau, gwargwadon natsuwar mutum cikin sallah gwargwadon darajar da yake samu gun Allah. Don haka ne ma ma’aikin Allah ya ce, “Allah ba ya juya wa Bawa baya yana cikin sallah matuƙar bai waiwaya ba; idan ya waiwaya kuwa, sai Allah ya bijire masa.”_
_Babu abin da yake kawo waiwayo cikin sallah kuwa sai gafalar Bawa da muƙamin Ubangijin sa, watau ya zama tamkar wanda ya tsaya yana ganawa da Ubangijin sa alhali zuciyar sa tana shagale da wani abin dabam. A kan wannan matsala ne Allah yake ce wa Manzon sa, da al’ummar sa ma, a cikin suratul A’ARAF aya ta 205:_
_”Kada ka kasance daga gafalallu.”_
_In muka lura sai mu ga cewa ta ya ya kuwa gafalalle zai iya tunawa da muƙamin Ubangijin sa yana cikin wannan hali na rashin kula har wani abin tsoro ya auku? Bugu da ƙari, daman can ga shi Allah ya yi umarni a cikin suratul Ɗ.H., aya ta 14 da cewa:_
_”Kuma ka tsayar da Sallah domin tuna Ni”._
_In mutum ya Yi haka, ana fata ya rabban ta._
_Allah yasa mu dace._
*EPISODE four*
Babban haraban asibitin cike yake da mutane bila adadin, mutane ne kamar tsaki kama daga yara manya masu kuɗi da manyan likitoci duk an gayyace su, har ta da gwamna Malam Nasiru El Rufa’i sai da aka gayyace shi wajen, komi ana yinsa ne akan tsari gunun sha’awa
Ɗahira, Shakira, Yusra da Fadila can na hango su wajen zaman su daban, sosai su kayi kyau cikin shigan su na material fari ƙal da akayi masa ɗige-ɗigen Coffee colour, ɗinkin doguwan riga akayi musu fitted, sai suka yane kan su da Goldeen Veil tare da sanya Hill shoes shima Golden, sosai su kayi matuƙar kyau kamar ka sace su ka gudu sai faman haskawa suke yi kamar taurari
Nan akayi ta gabatar da komi cikin girma da arziƙi, daga ƙarshe aka gabatar dasu a matsiyin waɗanda ake taya murna tare da sauran sabbin ma’aikata da za’a ɗiba.
Wata kyakykyawar Farar mota ce ta shigo haraban asibitin, a hankali motar take tafiya har zuwa inda sauran motocin suke fake, tsawon mintuna 5 kafin aka buɗe motan ya zuro kyawawan ƙafafun sa kana ya fito a hankali yana rufe motan, kyakykyawar saurayi ne da aƙalla bazai wuce 32yrs ba, fari ne tarrr kamar kalatsa shi jini ya fito don har wani ɗaukan idanu yake yi, yana sanye da Milk ɗin riga me gajeren hannu da ya matse sa sosai, sai Blue Jeans tare da sanya Combat a ƙafafun sa shima blue, yana da yalwan gashin kai kwantacce baƙi siɗik tare da ɗan siririn sajen sa, Kallo ɗaya idan kayi wa Guy ɗin zaka tabbatar da ya haɗu ne tako ina, *USMAN NOOR AL’AMEEN* kenan, *(The Younger Doctor)* yaro kyakykyawa me Izza da Son nuna shi wani ne, ma’aboci Son gayu da son hutu
A hankali ya taka ya soma tafiya cike da taƙama ya nufi inda su Big Dady suke.
Har aka gama taron sannan kowa ya soma tafiya gida, sai yamma duk yawancin ƴan uwa suka soma watsewa sai gidan ya rage daga ƴaƴan Kaka sai jikokin shi suka rage waɗanda basu tafi ba, su ma ɗin a gobe duk za su watse su tafi
Washe gari ƙarfe 05:00pm. Na Yamma gaba ɗaya a halin gidan sun hallara a babban parlour bisa umarnin Kaka
Ɗahira ce tafito daga Part ɗin su don ita bata riga ta tafi ba, tana sanye da doguwar rigan atamfa kalan ja da ratsin Milk da ruwan ƙwai, rigan iyakan ta ƙwaurin ƙafafuwan ta kuma sosai tayi mata kyau ta sake fito da tsantsan kyawunta da kwarjinin ta, sai tayi Rolling da ɗan ƙaramin Veil da iyakan sa kafaɗun ta, Slippers ne a ƙafanta tana tafiya tana latsa waya, hira take yi da freinds ɗinta na Facebook sai faman doka murmushi take yi, gab da ta iso ƙofan da zata sada ta da General parlour taji tayi karo da mutum wanda hakan yasaka wayan ta ya zame ya faɗi ƙasa, a hankali ta ɗago kanta tana kallon sa
haka zalika shima ɗin dai-dai da sanda ya sauke nashi idanun cikin ƙwayan idanuwanta da yafi tsana cikin rayuwan sa
kallon sa kawai take yi babu ko ƙyafta idon
While shi kuma ya ɗaure fuska tamau yaja jikin sa ya wuce, gab da zai buɗe ƙofa ya tsinkayi zazzaƙan muryan ta tana cewa
“Ba ka ganin kayar min da waya ne?”
Cak ya tsaya yana juyowa ya kalle ta da tsananin mamaki da ya nuna a face ɗin sa, ita kuwa a lokacin kallon wayan nata da ya fashe take yi cike da tsananin baƙin ciki sannan ta ɗago kyawawan idanun ta tana kallon sa itama fuskarta a ɗaure
A hankali ya tako ya’iso gaban ta still yana ci gaba da kallon ta, duk da ya daɗe be ganta ba kuma tayi masa girma ainun but be yi tunanin cewa ta kai matsayin da har za tayi masa irin wannan maganar ba, shiru yayi yana ƙare mata kallo yayinda itama ɗin shi take kallo batare da ko alaman tsoro ya nuna a fuskarta ba, abinda ya ƙara ba shi matuƙar mamaki kenan, domin yasan ada babu wanda tafi tsoro sama dashi, idan har zata gan shi ko za taji sunan sa tsoro ne da fargaba suke kawo mata cafka, ko kaɗan bata haɗa hanya dashi bare magana ya haɗa su, duk inda akwai shi to ta haramta wa kanta wurin har sanda zai bar wajen
Kuma hakan ya samo asali ne tun sanda ta tashi da wayon ta take matuƙar tsoron sa, ba don komi ba sai tsananin azaban da yake gana mata da tsanar da yake nuna mata afili ko a ɓoye, shi kuwa tun sanda aka haife ta ya haɗa idanu da ita shikenan yaji ya matuƙar tsanar ta, ba don komi ba sai don ƙwayar idanun ta da ya kalla, sabida idan har zai kalle ta sai yaji faɗuwar gaba me tsanani tare da tsoro wanda hakan ne ya saka mishi muguwan tsanar ta cikin ran sa, sosai cikin ƙwayar idanun ta da suka kasance sky green suke bashi tsoro da fargaba, hakan yasa tun tana ƙarama ko ɗaukan ta ba ya yi, da zaran ya ganta duka ne abinda ke haɗa shi da ita, har zuwa kuwa girman ta da ta gane shi ɗin mugu ne, koda laifi sukayi ƴan gidan gaba ɗaya, to ita yake kamawa ya fanshe kaf dukan da zai yi musu akan ta, ko agaban waye babu wanda zai iya hana sa, kuma koda an hana sa sai ya san yanda yayi ya haɗu da ita ya gana mata azaba, Ɗahira ta tashi cikin tsoron sa matuƙa wanda ya haddasa mata tsanar sa fiye da wanda yake mata, kwata-kwata bata ƙaunar sa bata ƙaunar ganin sa koda jin sunan sa ne, ta saka wa kanta shi ɗin maƙiyin ta ne wanda babu wadda tafi tsana a duniya sama dashi
Wajen shekara 9-10years kenan babu shi a ƙasan, yana can ƙasar Turkey yana aiki acan, tun sanda ya tafi karatu ya zauna can sai dai yazo gaishe su, Ɗahira ta dena jin tsoron sa ne don kawai daɗewan da tayi ba ta ganin shi, and sai kuma girma da yazo mata, yanzu baza ta taɓa juran abinda yayi mata a baya ba, domin ita tana ganin ta wuce matsayin da zata zauna wani banza wanda ba iyayen ta ba ya duke ta bare har taji tsoron sa.
Sauke kansa yayi kan wayan yana kallo, sai kuma ya mayar da idanun sa kanta yana sake ɗaure fuska ya ɗaga ƙafan sa ɗaya ya ɗaura saman wayan ya soma murje ta da ƙaton takalmin sa da ya kasance tamkar irin na sojoji, babu abinda ake ji sai sautin ƙaran fashewan wayan