BAKAR WASIKANOVELS

BAKAR WASIKA 14

BATURIYA POV.

Bayan ta gama zazzagawa Alhaji Sule rashin mutunci ta shiga tai wanka. Ta shirya cikin farin lace sai aikin gogawa fuskarta powder take, can kuma ta mike tsaye tana kallon kanta a madubi, sai ta ji ana kwankwasa gidanta, jiki na rawa ta aje soson hodar dake hannunta ta fice daga dakin da sauri taje ta bude gidan domin ta san da zuwan Ramlee.
Rumgume juna sukai ita da Ramlee kowa ne na murnar ganin wani kamar wadanda suka shekara basu saka junan a ido ba.

“No no ba dai lace din nan kika saka ba? Ai yanzu kuma kin wuce saka kananan kaya”

Ramlee ta fada tana yatsina fuska

“Ke mai tsada ne fa, yayata ta ba ni shi, mai kudi take aure fa”

“Baturiya kenan yanzu ai kin wuce wata ta kwance ta baki ki daura, sai dai ke ki kwance ki bawa wata ta saka, ga wata abaya nan na zo miki da ita kamin mu fara zuwa siyayen tufafi masu tsada”

Ta karashe tana mika mata jakar dake dauke da abayar, wani irin tsalle Rafi’a tai ta dire tana murna.

“Amman Wallahi kina da zuciya mai kyau, kamar kin san ina mararin abaya”

Ta karba da sauri ta nufi cikin dakinta sai Ramlee ta bi bayanta tana murmushi, a falo ta zauna har sai da Rafi’a ta canja tufafin jikinta daga lace zuwa sabuwar abaya, ita kanta ta yaba yadda bakar abayar tai mata kyau kasancewarta fara, cikin zumudi ta nufo falo.

“Allah ya miki sura Baturiya Wallahi kina da kyau”

Ramlee ta fara tana kallonta.

“Wallahi zaki sha kudi, manyan masu kudin nan suna son fararen mata amsu kananan shekaru”

“Da gaske?”

“Uhm har sai na rantse miki ma, a ciki ma zaki samu wanda zai ce miki aurenki yake so, ko ma be ce ba idan kin ga ya miki sai mu bada sunansa kawai a kama mana shi, dube ki gani fa Wallahi ke matar manya ce Baturiya”

Baturiya ta yi murmushi tana jin wani irin dadi, sannan ta koma ciki ta dauko. Jakarta da karamar wayarta da makulli ta fito.

“Ina Sultan”

“Tun dazun na tura shi makota”

“Aiko kin kyauta, domin yara akwai sa ido zai iya fadawa Babansa na zo”

Suka yi dariya sannan suka fito daga falon kamin su fita daga gidan gaba daya Baturiya ta kulle gidan. Sannan suka nufi bakin titi inda motar Ramlee take, front seat Baturiya ta shiga Ramlee kuma ta ja motar suka kama hanya, suna tafe suna hira har suka shigo cikin gari, gaban wani katon shagon siyar da wayoyi Ramlee ta faka motar, kusan a tare suka fito ita da Baturiya, tana kokarin rufe motar ta hango Alhaji Garba jikin mota yana waya.

“Ramlee bari na gaisa da mijin yayata ga shi can”

“Ba zai ce wani abu ba?”

“Zan ce ke na rako ai, ban sani ba ko zai ba ni wani abun yana da alheri ai”

“Shikenan bari na jira ki daga ciki”

Kai ta daga mata sannan ta nufi gurin da yake tsaye jikin motarsa yana waya, ganinta yasa yai hanzarin yanke wayar da yake ya kalleta yana murmushi.

“Baturiya ina kika fito?”

“Ai kai zan tambaya na sani ko wata budurwa ka rako”

Yayi dariya.

“Zaki bari ne? Ai kin tare kowa ya gida ya kowa ina mijinki?”

“Kowa lafiya kalau, ina Anty”

“Lafiya Kalau take, me kika zo yi nan?”

“Wallahi wayata ta bata kwanan baya shi ne na zo siyen karama”

“Oh haka fa, Yayarki ta fada min Allah maida alheri, ai da na san da zuwanki da na riko miki wani abu gashi bani da enough a mota”

“Uhm Alhajina kenan ai kai babba ne, kuna da kudi sai dai idan ba ayi niyar ba mu ba, tun da alherin zuwa zuwa ne”

Ya sake yin dariya yana kallonta.

“Haka yayarki ta fada miki?”

“Aa yayata bata fada min komai ba, haka dai na gani da idona”

Ya bude motarsa yana dariya.

“Baturiya sarkin rigima ashe dai mijin naki yana fama”

“Kana dai fama zaka ce, ko ka bawa wani ne?”

Yayi dariya mai sauti.

“Zankadediyar mata irinki zan kyautar na dai ara masa shan miya, yanzu dai bari na siye bakin nan naki dan karki je ki fadawa yayarki kin gan ni a gurin siyen waya”

Ya fada bayan ya zauna cikin motar, sannan ya ciro bandir din yan dari dari 10k ya mika mata.

“Gashi na rufe bakin nan kar yayarki ta ji”

Murmushi tai ta karba.

“Karka damu Alhajin Allah, ai ko mutum ka yanke agabana ka bani wadannan ka rufe bakina babu wanda zai ji”

“Da gaske? Ashe za a iya siye ki da kudi?”

“Ba wai za a iya ba, ana ma yi ne”

Ta fada tana wani irin kashe masa ido kamar wata tsohuwar karuwa. Binta da kallon da shi kadai ya san manufarsa yana murmushi har ta shiga cikin gurin. A bakin kofa ta samu Ramlee tana jiranta.

“Yayarki tana da miji kamar wannan kike zaune a talauci?”

“Uhmm yan uwa yanzu ai babu ruwansu da son zumunci idan sun samu daga su sai yayansu”

“Shiyasa nake son ki gina kanki ki yi naki arzikin”

“Wallahi kuwa, babu abun da yake burge ni kamar katon gida da katuwar mota da kayan sakawa da na ci masu kyau masu tsada, Wallahi ko hoto ake turowa a group zaki ga ko wace shegiya da katon falo, haka nake ta ganin friends dina a gida masu kyau da sutura mai tsada, ki duba ko yan’uwana kowa tana auren mai rufin asiri amman ni kullum abushe ko abunda zamu ci wani lokacin gagararmu yake”

“Karki damu kin warke yarinya ke dai ki goge kawai ki iya dadin baki da kwarkwasa da jan hankali”

Haka suka cigaba da nisawa cikin shagon suna ta hira, an tsara shago gwanin sha’awa camera a ko’ina ga gilashi da haske gulob kamar ba rana ba,.kana ganin gurin kasan na manyan mutane ne.
A tare suka jera da Ramlee suka nufi gurin da aka jera wayoyin techno. Ramlee ce ta fara dubawa sannan ita ma ta kai hannu zata dauki wata sai ta ji an riko hannun nata, saurin kallon gefenta tai da tsoro sai tai arba da mutumen daya rage mata hanya a wacan lokacin da ta sauka tasha daga Kano, murmushi ta sakar masa kamar yadda yake mata murmushin shi ma, sai ta janye hannunta.

“Sarki alkawari”

Ta watsa masa wani irin kallon irin na masoya.

“Daman na yi alkawari?”

“Ba ki yi ba amman dai ai ya kamata ki ce min na isa gida lafiya ko?”

Ta yi murmushi, shi ma murmushin yai ya gabatar mata da yarinyar dake gefensa.

“Ku gaisa da kanwata, ya kamata ku san juna tun yanzu ai”

“Sannu”

Baturiya ta fada. Sai ita ma yarinyar dake kama da saurayin ta maido mata.

“Yauwa sannu, sunana Salima”

“Ni kuma Rafi’a amman anfi kirana Baturiya”

“Yeah kin fi turawan kyau ai”

Cewar saurayin sai duk suka yi dariya har shi.

“Me kika zo yi nan?”

“Waya na zo siya kasan wayata ta bata”

“Oh haka ne, amman kin san na tashi koma gidan nan sai kuma wata zuciyar ta bani hakuri ashe rabon zan hadu dake ne a nan, gaba daya na kasa samun natsuwa tun da muka rabu Wallahi nake ta mamarin ganinki har Hajiya na bawa labarinki”

Ta yi murmushi.

“Gashi yanzu, ai mun hadu katin daka bani ya bata ne”

“Ayyah”

Ya fada sai kuma ya kalli Ramlee dake ta duba wayoyi.

“Ko zaki bani aron kawar nan taki mu zagaya gurin masu IPhone”

“Yeah ba matsala, zan jiraki a mota”

Ramlee ta fada tana murmushi, sai Baturiya ta daga mata kai.

“Okay”

Bayan Ramlee ta wuce ya bawa kanwarsa key din motar.

“Je ki jirani a moto”

“Okay sai anjima in-law”

Budurwar ta fada sai duk suka yi dariya, sannan ya nuna mata hanyar da zasu bi su bullo gurin da aka jera iPhone din.

“Fahat sunana duk dai baki tambaya ba”

Ta kalleshi ta yi murmushi, da kansa ya zaba mata iPhone mai kyau, sannan ya nufi wajen biyan kudi ya mika atm dinsa, kamar ance ta juyo, tana juyowa tai arba da Nura tsaye gurin biyan kudin, da alama wani ya rako, suna hada ido tai saurin dauke kai gabanta ya shiga faduwa da mugun karfi. Bayan ya biya ya rakata har gurin motar Ramlee ya sake ciro katinsa ya mika mata.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button