Uncategorized

RAUDHA Page 11 to 20

Abinda yafaru RAUDHA tasanar mata

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un… Amma basu yi miki komi ba ko Besty?”

“Babu abinda sukai min ki kwantar da hankalin ki”.

Ajiyan zuciya Ramcy tasaki da ƙarfi wanda sai da yasa RAUDHA darawa tace

“Wannan ajiyan zuciya haka my Ramcy?”

“Hmm ai dole ne my Besty wlh bazan taɓa jindaɗi ba idan wani abu yasame ki, dole zan shiga tashin hankali sosai”.

Murmushi RAUDHA tayi cike da jindaɗi batare da tafurta komi ba

“To yanzu yaushe zaki dawo ko sai Daddy ya dawo garin?”

Girgiza kanta RAUDHA tayi fuskarta na nuna damuwa tace “Besty bazan dawo nan kusa ba sabida waɗanda suke son yin garkuwa dani suna nan ba’a kama su ba, dole zan zauna anan har sanda za’a yi solving matsalan”.

Shiru Ramcy tayi batace komi ba

Sai da RAUDHAN tasake mata magana kafin tace

“Shikenan Besty mun yi nisa?”

“Nima banji daɗi ba wlh, amma komi zai wuce ai zamu sake haɗu wa ba da jimawa ba, zan saka Ya Suhaib yakawo ni”.

Ramcy tace “nima idan nasami lokaci insha Allahu zan riƙa zuwa har nan Besty, muna nan tare ako ina ne, nisan gari bazai hana Ni zuwa gare ki ba”.

Murmushin jindaɗi RAUDHA tayi kafin tace “Thanks friend Allah yabar mu tare”.

“Ameen ameen My Besty, kinga aunty Nafeesa ta haihu ɗan babu rai?”

Cikin damuwa RAUDHA tace “oh yaushe kenan?”

“Jiya ne, dama cikin be isa haihuwa ba”.

“Eyya.. ki miƙa min gaisuwa ta gare ta kinji?”

“Insha Allahu zata ji Besty”.

Daga nan hira suka ɗan taɓa kaɗan kafin takashe wayan ta’ajiye

Tana nan kwance shiru kamar ruwa ya ci ta, sai kuma daga baya tamiƙe taɗauko HangBag ɗin ta wanda tazuba ƙwayoyin ta

Tunda tazo gidan komi bata sha ba, shiyasa take jin ta daban

Kallon cikin jakar tayi, babu yawa duk ya kusa ƙare wa

Tsaki taja tana ajiye jakan, sai kuma taɗauka taciro tasoma afa ƙwayoyin, sannan kuma takoma takwanta tana lumshe idanun ta, ajiyan zuciya kawai take sauke wa har zuwa lokacin da ƙwayoyin suka soma mata aiki, gyara kwanciyarta tayi babu jimawa barci yayi awon gaba da ita, a lokacin ƙarfe 05:30pm.

Har bayan isha’i bata farka ba, don haka Farida tashigo ɗakin domin tatashe ta tunda ta shigo har sau biyu tana duba ta

A bakin gadon tatsaya tasaka hannu tana shafa baby face ɗin ta, ta jima tana ƙoƙarin tashin ta kafin tabuɗe idanun ta da suke a rine sosai, sake lumshe idanun tayi tana buɗe wa ahankali

Murmushi Farida tayi mata tace “ƙanwata wai barcin nan baya isan ki ne? Tunda kika zo babu abinda kike yi koda yaushe sai barci, ko kasa sai ya shafa miki lafiya ai”.

Kallon ta kawai RAUDHA take yi bata ce komi ba, sai dai a yanzu ɗin ta ɓata fuska

Still Farida murmushi tayi tasaka hannu tana janye jakar dake ajiye akan gadon tana faɗin “kiyi haƙuri kinji, naga Yakamata ki tashi kiyi sallah ne kici abinci tunda lokaci na ƙure wa”.

Kamar ance taleƙa cikin jakan sai taga ƙwayoyin ciki, duk da Farida ba wai tasan kayan maye bane amma taga an rubuta sunan shi ajiki, sai kawai tasaki baki tana kallon RAUDHA dake ƙoƙarin miƙewa zaune

Bata ce komi ba kuma taɗau jakan tamayar mata inda sauran suke sannan tafice

Ɗakin su takoma inda Suhaib ke zaune yana faman aiki a Lapton, zama tayi kusa dashi kan Two sitter tana kallon sa, cikin sanyin murya tace

“Dama RAUDHA tana shan kayan maye?”

Cakk yatsai da abinda yake yi yana ɗago wa yakafe ta da idanun sa masu matuƙar kyau.

[12/20/2020, 4:01 PM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????

????????????????????

????????????????????

  *RAUDHA*

????????????????????

????????????????????

????????????????????????????????????????

*MALLAKAR*✍️

              _Nafisat Isma’il Lawal Goma_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*????

         *F.W.A????/*

.

  *NOT EDITED* ___________________________????

        *SEASON SIXTEEN*

_______????Iska yafesar ta cikin bakin sa kafin yace “Nasan tana sha ai”.

Baki sake Farida take kallon sa, cike da tsantsan mamakin sa tace “kana nufin kana sane tana wannan rayuwan but bakayi komi akai ba?”

Zuwa yanzu damuwa ne sosai yanuna a face ɗin nasa, cikin rashin jin daɗin halin da ƙanwar nasa take ciki yace “Ni kaina bana jindaɗin halin da Baby take ciki amma bansan ya zan yi ba, na rarrashe ta na faɗa mata illan hakan but taƙi ji”.

Ido Farida tazuba masa ta kasa cewa komi, mamaki al’ajabi duk ya cika mata zuciya, bata taɓa tunanin soyayyan da suke mata zai saka su bar ta tana irin wannan rayuwan ba, a matsayin ta na ɗiya mace ma ba na miji ba

“Lallai kam akwai aiki”. Tafaɗa a ranta kafin a fili tace

“Wannan wani irin so kake mata da har zaka kai ta ga halaka?”

Tsare ta da idanu yayi cikin rashin fahimta yace “me kike nufi Wifey?”

“Ina nufin taya zaka bar RAUDHA tana shaye-shaye but ka kasa hana ta? Kana tunanin halin da zata shiga nan gaba? Meyasa soyayyar ta zai rinjaye ka kakasa ɗaukan mataki akanta? Idan baka sani ba wannan ba soyayya bane Husband, idan har baza ka hana ta wannan ɗabi’an ba tabbas nan gaba zaka yi nadama”.

Suhaib yace “ya kike so in yi My Wife? Kar ki manta bazan iya ko ɗaga yatsa bane akan ta, Ni na rasa ta yanda zanyi in hana Baby Shan kayan maye, ko kaɗan bana son ɓacin ranta..”

“Wannan ba hujja bane Sweetheart, tabbas idan har zaka ga tana aikata saɓon Allah kabar ta to wlh baka son ta sannan baka ƙaunar ta, kuma wlh sai Allah ya tambaye ka idan har baka taimaki rayuwan ta ba tunda har da kwamashon ka cikin gurɓacewar tarbiyyar ta”. Taƙarike maganar ta tana ƙoƙarin miƙe wa

Ruƙo hannun ta yayi yana mayar da ita yace “ina zaki je kuma? Don Allah ki zauna ki bani shawara bansan ya zanyi ba, Ni kaina nasan ina da laifi, but ke kanki kinsan halin Baby, hakan zai iya kawo babban matsala a tsakanin mu, sannan bansan ma taya zan iya ɗaukan mataki akanta ba”.

Izuwa yanzu haushi sosai yake bata, duk da tasan girman soyayyan da suke mata shi da Daddy amma hakan ba yana nufin baza su iya mata faɗa ba don kawai kar ranta yaɓa ci..

“Kinyi shiru my Wife? Taya kike ganin zan ɓullo ma al’amarin?”

Ajiyan zuciya tasauke kafin tace “dole ka ajiye soyayyan ta agefe kafaɗa mata gaskiya, idan takama ma har hukunta ta kayi idan har hakan zai saka tadena..”

Dariya Suhaib yasaki hakan yasa Farida tatsayar da maganar ta tana bin sa da idanu

“Wai kina tunanin Baby zan hukunta? Ni ɗin?”

Sai kuma yasake kecewa da dariya

Ita kuwa wannan karon kallon sa take yi cike da tsantsan tausayin sa, tabbas soyayyar RAUDHA ya rigada yayi tasirin da baza su taɓa koda ɗaga yatsa akanta ba, koda kuwa hakan na nufin rabuwa da farin cikin su ne

Kanta tajinjina kafin tace “to Allah yakyauta tunda baza ka iya ba”.

Sai tajanye hannun ta kawai tamiƙe tafice a ɗakin

Shima be sake dakatar da ita ba yaci gaba da aikin sa, be jima ba yajanye Lapton ɗin yana miƙe wa tsaye, miƙa yayi yana yarfe hannayen sa, sai da yaɗan jujjuya jikin sa yanda zai saki kafin yanufi ƙofa yafice

Akan kujera yatarda ita zaune

“My wife taso muje muyi dinner yunwa nake ji, Ina Baby bata fito bane?”

Yaƙarike maganar yana kallon saman, kafin kuma yamayar da idanun sa kan Faridan da a yanzu take ƙoƙarin tashi, zuwa wajen ta yayi yataimaka mata tatashi

“Bata fito ba”. Taba shi amsa tana yin gaba abin ta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button