Uncategorized

RAUDHA Page 11 to 20

“Ƙawata ki bari gobe wanda zaki samu a wajen sa zai zo, idan ya zo sai in haɗa ki dashi kuyi maganar wanda kike so yakawo miki”.

Ɗago kai RAUDHA tayi takalle ta, sai ta ɗan yi murmushi kafin taɗau jakar ta tabuɗe taciro kuɗi, miƙa ma Rash tayi sannan tayi mata bayanin wanda take so idan ya zo sai ta amsar mata ta’ajiye mata

Rash kuwa sai washe baki take yi ganin kuɗin da RAUDHA ta bayar me yawan gaske

Ita kuma RAUDHAN sai tatashi tafice tabar su nan

“Kutt.. wlh yarinyan nan ba ƙaramar yarinya bace, kai daga gani zan ji daɗin ƙawance da ita”.

Dariya Maan yasaki yace “ke dai kin bani wlh”.

“Eh ɗin naji, kasan yanzu abinda za’a yi? Bari in ɗibi rabo na domin kuɗin nan yayi yawa wlh, wannan kuma kariƙe nasan zaku fi haɗuwa dashi sai kaba shi”.

Amsar kuɗin Maan yayi yatura cikin aljihu yana miƙe wa

“Da Allah tashi muje in sauke ki, yau akwai inda zani wlh, gashi ma ina so in gangara wajen Asha be da lafiya”.

Miƙe wa tayi tana rataya jakanta kafin tace “shine baka faɗa min ba? Ai kawai mu wuce tare don babu inda zan fita yau, wahalan makarantan nan ma ta ishe Ni”.

Dariya yayi yana faɗin “ke dai wlh raguwa ce daga soma zuwa har kin fara ƙorafi, amma idan yawo ne babu inda ƙafanki be takawa”.

“To ya son ranka? Wancan fa neman kuɗi nake yi ka ga kuwa bazan gaji ba, Ni dai muje da Allah na ƙosa in jini a kan gado na”.

Hannu yasaka yatallabe mata ƙeya

“Mayya kawai, to zo ki hau bayana mana”.

Rash da har ta saka ƙafa a waje tajuyo tana buga masa harara tace “wlh Sweety na fi ka iskanci kasan halina yanzu zan ɗare ka, kuma wlh bazan sauka ba duk uban da zai gan mu sai dai yagan mu”.

Taɓe baki kawai yayi yabangaje ta yay gaba

Tabi bayan sa kuwa dasauri tana ɗurma masa duka a baya, ahaka har suka kai wajen Motan Maan ɗin suka shige, lokacin sun sauya hiran su har da tafa wa cike da nishaɗi.

[12/26/2020, 3:48 PM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????

????????????????????

????????????????????

  *RAUDHA*

????????????????????

????????????????????

????????????????????????????????????????

*MALLAKAR*✍️

              _Nafisat Isma’il Lawal Goma_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

*FEENAH WRITER’S ASSO????*

“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*????

         *F.W.A????/*

.

  *NOT EDITED* ___________________________????

        *SEASON EIGHTEEN*

_______???? lokacin da RAUDHA ta isa gida Packing tayi tafito rataye da jakar ta a kafaɗa sannan tarufe motan tay cikin gidan

Tana shiga cikin parlour’n Farida na fito wa daga kichen riƙe da Plate a hannun ta shaƙare da kayan marmari

“A’ahh ƴan makaranta har an dawo?”. Farida tafaɗa fuskarta yalwace da fara’a

RAUDHA murmushi tayi tana kallon ta sannan tagyaɗa mata kai, sai tace

“Ina Yayana be dawo ba?”

“Eh Yayan ki be dawo ba sai zuwa anjima”.

Bata sake magana ba tayi hanyar upstairs

Ita kuma Farida sai tanufi saman kujera tazauna tana ɗaukan Apple ɗaya tana kai wa baki.

      Koda tashiga ɗaki jakan tayar saman gado sannan tazauna gefen gadon tana saka hannu tazare combat ɗin ƙafafun ta, sai tacire agogon hannun ta ta’ajiye sannan tamiƙe tasoma cire kayan jikin ta, anan tazubar tatsallake su nan ƙasa tanufi Toilet bayan ta ɗaura towel a jikin ta, wanka tayi tafito tasanya farar shimi iya cinyan ta, sannan tabarbaza gashin kanta yasauka zuwa kafaɗa kafin taɗau wayan ta tafito Parlour

Har a lokacin Farida na zaune tana shan Fruits ɗin ta tana kallo

Kai tsaye dainning tanufa taja kujera tazauna, sai da tazuba farar shinkafa a cikin Plate sannan takalli Farida taɗauke kai tace

“Aunty Wai baki da masu aiki ne anan?”

Da fara’a Farida tace “eyya ina dasu mana, wani abun zasu yi miki?”

Yamutsa fuska tayi kafin tace “naga yanda nafita nabar ɗakina haka nazo na tarar, na kula ma gaba ɗaya ba’a gyara min ɗaki”.

Farida tace “Ni nace mata kar tashiga ɗakin ki wataƙil baki son me aiki tayi miki gyara idan bakya nan, but zuwa anjima zata shigo sai ta gyara miki, ina sallaman ta ne idan ta gama aikin nata”.

Abinci tazuba cikin bakin ta tana tauna wa idanun ta akan Faridan kasancewar Facing ɗin ta takey, sai da tacinye na bakin ta kafin tace

“Ya za’a yi ki riƙa barin ta tana tafiya ba aiki take yi bane? Idan kuma ana buƙatar ta fa?”

“Eh ai nan kusa take bata da nisa duk da tayi tafiya ne but jiya ta dawo, tana zuwa sau biyu ne a rana, idan tazo da safe tagama aikin ta sai tatafi sai yamma, tunda dama Kuku ne me mana abinci, shine kaɗai yake zama a gidan nan idan yagama abincin sa sai yakoma BQ yazauna sai an buƙace shi, kuma Yayan ki ne ma be son zirga-zirgan ƴan aiki sannan nima ina yin abinda yasauwaƙa da kaina don nima bana so komi ai min”. Farida tayi maganar idanun ta duk akan RAUDHA dake ta zuba abinci a cikin ta

Kaɗa kanta RAUDHA tayi sannan ta’ajiye spoon ɗin hannun ta tana tsiyaya Lemu cikin glass Cup tace “to Ni dai ina buƙatar ƴar aiki kusa dani sabida bana yin abu da kaina, ban saba ba kuma bazan yi ba, and yanzu da kike barin ta tana tafiya gida gashi na cire kayana babu wanda zai matsar min dasu sai Ni kenan?”

Murmushi Farida tayi tace “kai ƙanwata yanzu har kayan naki baza ki iya kai su inda yadace ba dole me aiki zata kawar miki? Ke fa macece yakamata kisan abinda yakamace ki tunda yanzu kin girma a koda yaushe za’a iya kai ki gidan miji, to wa zai miki acan ɗin?”

Waro manyan idanuwan ta da suke farare fat tayi kafin talumshe su tasake buɗe wa tana ci gaba da kora Juice ɗin ta

“Kina tunanin Ni ƴar gata har akwai auren da zan yi nan gaba in koma ina yin aiki da kaina? Ko kin manta wanene ubana?”

Sai kuma tayi murmushi tana ajiye cup ɗin hannun ta taɗau spoon tasoma tsakalan abincin kafin kuma taci gaba da faɗin

“Idan har ina da Daddy da Yayana a doron ƙasa to ba zan taɓa yin bauta ba, ki dena ma wannan shashancin”.

Numfashi Farida taja tana jin babu daɗi ta yanda RAUDHA take gaya mata magana a haka tamkar bata san da wa take yi ba, sai dai tasan bata da ishashshen tarbiyya bare ta san ba dai-dai tayi ba, don haka tamatse ɓacin ranta tare da saka murmushi a face ɗin ta tace

“RAUDHA duk abinda ɗiya mace zata yi a gidan Mijinta to ba bauta bane kamar yanda kike tunani, Bauta ne a wajen Allah sannan neman lahiran ta ne, kuma ta wannan bautan zata samu lada har a gobe ƙiyama ta samu wuce wa ni’imar Allah, wato Aljanna kamar yanda Allah yayi mana bushara, RAUDHA babu yanda za’a yi ace kamar ki har yanzu baki san abinda yadace dake b..”

“Enough Aunty”. RAUDHA tafaɗa da ɗan ƙarfin muryan ta

Miƙe wa tayi tana kallon ta tace “baki da hurumin da zaki shiga rayuwata da har zaki koya min dai-dai da wanda ba dai-dai ba, please and please bana son ganin ɗakina da datti, idan zaki nemo min me aiki tariƙa gyara min ɗaki a duk sanda nake buƙata ki kawo, idan kuma baza ki nemo ba..”

Sai tayi hanyar Steps batare da ta ƙarisa ba, tahaye da gudu ta wuce ɗakin ta

Ajiyan zuciya me ƙarfi Farida tasaki jikin ta duk a sanyaye, tabbas RAUDHA tana buƙatar sabuwar tarbiyya idan ba haka ba tana cikin halaka, tana son yarinyan har cikin ranta shiyasa take son taba da gudunmuwar ta wajen sauyawan ta, amma taya? Bata da ikon da zata iya sauya RAUDHA sabida bata kai matsayin ba, amma kuma idan har Daddy da Suhaib sun so ta sauya to tabbas zata sauya, gatan su a gare ta shine ya gurɓatar da ita sannan kuma su ne a yanzu zasu iya tanƙwara ta wajen sake bata tarbiyya tun kafin tafi ƙarfin su, duk da a yanzu ɗin tafi ƙarfin nasu amma su ne kaɗai zasu iya hukunta ta, idan har bada amincewar su ba to babu wanda ya’isa ya gaya ma RAUDHA gaskiya

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button