Uncategorized

RAUDHA Page 11 to 20

Jinjina kansa yayi kafin yace “That’s good RAUDHA, da fatan dai kin fahimci duk tambayoyin naki ko?”

Tagyaɗa masa kai

Murmushi kaɗai yayi mata yakalli ƴan ajin da suke mamakin ta jin sunan musulmai ke gare ta, yayi musu sallama yafita

Kasancewar Lecture ɗaya suke dashi a yanzu ɗin, sai zuwa goma zasu shiga wani don haka ɗalibai suke ta fita, waɗanda kuma zasu zauna suka gyara zama suka dasa hiran su a tsakanin su

RAUDHA ma tana zaune bata tashi ba tana bitan karatun, sosai RAUDHA take son karatu shiyasa idan har ba komi take yi ba to karatu shine abokin hiran ta, bata wasa da karatu ko kaɗan that’s why take da ƙwaƙwalwa

Har time ɗin lecture yayi Malamin yashigo yasoma gabatar musu da karatun sa, One hour yaɗauka kafin yafice

A lokacin ne RAUDHA tamiƙe tasaka Tap ɗin ta cikin jaka sannan ta rataya tayi hanyan fita, bata lura ba tayar da keey ɗin motan ta

Wata dake zaune su biyu da wani saurayi manne da juna a tsakankanin kujerun bayan, ita talura takalli Saurayin nan tace

“Kaga wancan Babe ɗin ta yarda keey ɗin ta”.

Kallon wajen da tatashi yayi yahangi mukullin yashe a ƙasa, kafin yace “to yanzu ya za’a yi zaki kai mata ne ko kuwa?”

“Bari in Kai mata dai, kasan Babe ɗin ta min kaga sai mu ma ƙulla ƙawance”.

Dariya yayi yace “baki da dama ke dai, daga shigowar ki har zaki soma jaye-jaye”.

Fari tayi da ido tana miƙe wa tsaye tace “ya son ranka? na san ko kai ta burge ka ba dai zaka faɗa bane kawai”.

Still dariyan yasake yi

“To je ki dawo dai sai mu tattauna maganar mu, kar kuma ki shanya Ni fa”.

“Baka da damuwa”. Tayi maganar tana ɗaukan keey ɗin lokacin da taƙarisa wajen

Tana fita hole ɗin tahangi RAUDHA batai wani nisa sosai ba, kasancewar tana tafiyan ne tana latsa wayan ta

Cikin sauri taƙarisa wajen ta tayi mata sallama

RAUDHA bata san da ita ake yi ba duk da kuwa taji sallaman kusa da ita

“Aslm alaikum RAUDHA”. Tasake sallaman tare da kiran sunan ta

Hakan yasa RAUDHAN taɗago kai tana kallon matashiya ƴar gayun dake tsaye a gaban ta, wanda a girme dai baza ta fi ta da shekaru biyu ba

Ganin kallon da RAUDHA ke mata batare da ta amsa mata sallaman ba, sai tayi mata murmushi tasake cewa

“Sannu ko?”

Gyaɗa mata kai tayi tana sake kafe ta da idanu

“Keey ɗin ki kika yar a class shine na ɗauko miki”.

Tayi maganar tana miƙa mata keey ɗin

Kallon keey ɗin tayi kafin tasaka hannu ta’amsa tana maida idanun ta kanta

“Thanks”. Tafaɗa cikin dashashshiyar muryan ta

“Babu damuwa.. Ni sunana Rash ko zamu iya zama friend sabida gaskiya kin burge Ni? Zan so mu kasance ƙawaye”. Rash ɗin tayi maganar tana faɗaɗa murmushin ta

Ɗan jimm RAUDHA tayi tana kallon ta batare da tace komi ba

“Yanzu ina zaki je sai muje in raka ki kafin mu shiga Lecture”.

Waro idanuwa RAUDHA tayi cike da mamakin ta, sai kuma tayi gaba batare da ta furta uffan ba

Duk da Rash taji haushin shirun da tayi mata, amma ita a ganin ta ci gaba ne a ganta tare da RAUDHA, duk da bata san ƴar gidan wanene ba but kallo ɗaya kayi mata zaka san a gidan manyan mutane tafito, barin ma yanzu da mutane suke ta kallon su, tasan idan tayi tarayya da ita zata sake zama Big gril ne

RAUDHA da har ta kai jikin motan ta tana ƙoƙarin buɗe wa, sai tatsinkayi muryan Rash kusa da ita

“Plz sister ko dai ba kya son tarayya Dani ne shiyasa kika ƙi kula Ni?”

Juyowa RAUDHA tayi takalle ta, sai kuma ta ɓata fuska tace “bana son friend.. ba shi.. yakawo ni.. ba”.

Yanda tayi maganar a ɗai-ɗai yasaka Rash tasaki baki tana kallon ta, har tashige motan ta bata motsa a wajen ba, sai da taji an dafa ta sannan tajuya dasauri tana kallon wanda ke kusa da ita

Murmushi yayi mata yace “maganin ki kenan ai, taƙi kula ki ko?”

Huro hancin ta tayi batace komi ba illa maida idanun ta kan motan RAUDHA da tay nisa tayi

“Ke da ganin yarinyan nan kin san ba kalan ki bace, kallo ɗaya wlh nayi mata nasan zatay girman kai ne, muje da Allah kin tsaya anan rana na gasa mu”.

Kallon sa tayi tana hararan sa kafin tace “mtsww dalla kar ka ishe Ni, ina zamu je ne?”

Baki yabuɗe

“Ke fa kika ce yunwa kike ji zamu je capteria amma kuma kike tambayana? Ko dan wannan yarinyan ta ɓata miki rai zaki fanshe a kaina, ke fa baki da mutunci wlh, baki sanin wanda zaki sauke tijaran ki a kanshi sai Ni”.

Murguɗa masa baki tayi tay gaba abinta

Shi kuma yabi bayan ta yana sauya zancen dan dai ta sauko

“Rashh muje mana mu kora wlh yau gaba ɗaya bana jindaɗin yanayin sabida ban jini a sama ba, gashi kuma wancan shegen be zo ba shiyasa yau ko son shiga Lecture bana yi na zo na tare a wajen ki”.

Bata tanka sa ba illa tafiyan ta da taci gaba da yi

Sai shima yayi shiru be sake cewa komi ba.

             ????????????

Fitan RAUDHA cikin school ɗin sai tasoma zagaye akan titi ta rasa inda zata je, so take yi tasami wajen da zata sayi kayan mayen ta tunda nata duk sun ƙare

Haka tay ta kewaye gari, sai a wani Club tatsaya tashiga tatambaya, bata samu abinda take so ba illa su Wine ???? kala-kala da suke dashi, fito wa tayi batare da ta siya ba don ita tafi son na afawa ba kasafai take ƙaunar Giya ba

Motan ta tahau tay gaba, a wani babban kanti ta tsaya tayi siyayya cikin baƙin leda takoma mota, kayan ciye-ciye ne fal a cikin ledan

Tana tuƙi tana cin Cake ???? har takoma school, bayan tayi parcking sai tazauna cikin motan taci gaba da ciye-ciyen ta, youghot taɗauka tana korawa da Cake ɗin

Bayan ta gama tazuge glass ɗin ta jefar da goran tamayar tarufe, share bakin ta tayi da tissue sannan takalli Wrest watch ɗin dake ɗaure a tsintsiyan hannun ta, ƙarfe 12:40pm. Don haka tabuɗe motan tafita tarufe tanufi Hole ɗin da zasu ɗau darasi

Tana shiga tazauna a inda tazauna ɗazu

Sai ga Rash itama ta ƙariso wajen tazauna kusa da ita tana mata murmushi

Kallon ta kawai RAUDHA take yi batare da tace komi ba ganin Malam ya shigo, sai taɗauko Tap ɗin ta taɗaura a cinya tasoma sauraron karatun sa

Rash kuma ko a jikin ta sai ma buɗe jakan ta da tayi taciro wani ƙaramin kwalba, ta ɗan duƙar da kai tana kurɓan abinda ke ciki

Hakan yasa RAUDHA taɗago kai tana kallon ta, kwalban tabi da kallo na tsawon lokaci kafin takau da kanta, bata sake kallon ta ba har sai da Malamin yafita sannan tajuyo tace

“Aina zan samu wannan?” Tayi maganar tana nuna kwalban hannun ta

Washe baki Rash tayi tace “kema kice ƴar hannu ce kenan?”

RAUDHA bata fahimci abinda take nufi ba sai tagyaɗa mata kai tasake cewa “ina so ne idan zan samu”.

“Ai kuwa kin zo inda zaki samu duk kalan da kike so, Ina zuwa bari in Kira Maan”.

Wayan ta taɗauka talatsa tanemo wani Numba da akayi serving da Sweety, sai ta danna kira, yana ɗagawa tace

“Maan shigo class ɗin mu yanzu ina jiran ka”.

Wayan takashe tamaida kallon ta kan RAUDHA tace “baki da damuwa domin Zen ke samo mana duk abinda muke buƙata, kema zaki samu”.

Murmushi RAUDHA tayi bata ce komi ba

Dai-dai nan Maan yashigo yazauna saman Deks yana faɗin “ya dai menene?”

Rash tace “ƙawata ce take buƙatan kayan maye ina Zen yake?”

Kallon RAUDHA yayi sannan yamaida idanun sa kan Rash yace “ke dai sai da kika shige mata kamar wata mayya, to yanzu Ni zaki tambaya bayan kinsan be shigo school ba yau?”

Hararan sa Rash tayi tace “wai to ina ruwan ka idan na shige mata, bana son fa saka ido”.

Sai taja tsaki tana kallon RAUDHA da tamayar da hankalin ta kan Tap tana shafawa batare da ta maida hankali kan abinda suke cewa ba

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button