RAUDHA Page 11 to 20

Insha Allahu ta ɗau alƙawari daga yau zata soma nuna ma Suhaib kuskuren sa ko zai dawo hankalin sa yakula da ƙanwar sa ta hanyar da yadace, da sannu idan har suna zaune a gidan nan tabbas sai tayi nasaran sauyawan RAUDHA da iznin Allah kuma tare da yardan mahaifin ta da yayan ta, dole abu na farko ta fara nuna musu kuskuren su ta yanda zasu dawo hayyacin su akan wannan mummunan makauniyan soyayyan da suke mata
A karo na babu adadi tasake jan numfashi kafin tayunƙura daƙyar tatashi tanufi kichen ta ajiye Plate ɗin sannan kuma tafito tanufi ɗakin su.
????????????
Tunda RAUDHA tashiga ɗaki wayan ta taɗauka takira Ramcy suka sha hira kafin takira Daddy, but har a lokacin baya shiga, jefar da wayan tayi tana turo baki, ƙunƙunai tasoma yi ita kaɗai tana janyo HangBag ɗin ta taciro Tap ɗin ta tasoma revision ɗin karatun da suka yi yau
Bata sake fita ba sai da tasan cewa lokacin yayan ta ya dawo gida sannan tafita, Can tazauna sukai ta hira har dare kafin tadawo ɗaki
Alwala taɗauro tazo tazauna bakin gado tasoma ƙirgan sallan da ake bin ta na kusan kwana biyar, sai da tagama lissafi kafin tatashi tazurma Hijab tasoma gabatar da sallan
Wajen awa biyu tayi tana gabatar wa kafin tagama, duk da kuwa ƴar faki take yi but sai da yaɗauke ta tsawon wannan lokacin
Miƙe wa tayi tacire Hijab ɗin sannan tasaka kayan barci riga da wando farare masu taushi da zanen Flower kalan Coffee a jikin sa, gado tahaye taja pilow taɗaura kanta tana sakin hamma, dayike barcin ne a idanun ta babu jima wa yaɗauke ta.
Can cikin dare tasoma mutsu-mutsu duk ta haɗa zufa kashirɓan, duk da kuwa akwai a.c ga fan da yake aiki amma haka RAUDHA tajiƙe da zufa yana ta kwaranya daga fuskarta zuwa cikin rigan ta
Mummunan mafarki take yi na baƙaƙen halittu, gashi wani narkeken maciji da yaninka ta a tsawo da girma ya kanannaɗe mata jiki ya cure ta, wannan dalilin ne yasaka take fitar da huci tare da gumi tana son ƙwace wa amma ina ko motsi ta gaza, kuka sosai take yi tana neman taimako babu me jin ta, wani irin baƙin daji ne da babu komi sai ƙoramu da namun daji masu ban tsoro, kukan su kawai ya cika jejin yana wani amsa kuwa a kunnen ta
Macijin buɗe bakin sa yayi tare da saita kanta yanufo da bakin sa zai haɗiye mata kai
Wani irin ihu tasaki wanda lokaci ɗaya tafarka a matuƙar gigita tana ci gaba da ihun a gaske, jikin ta wani irin mazari yake yi gaba ɗaya idanuwan ta sun fito waje tamkar zasu faɗo, izuwa yanzu kamar an ɗibi bokitin ruwa ne an kwara mata sabida yanda tayi tsamo-tsamo cikin zufa
Zumbur tamiƙe saboda yanda idanun ta suka hango mata ƙaton macijin a jikin bango Ya biyo ta baki a buɗe yana wani irin fitar da sauti me ƙara wanda gaba ɗaya ɗakin sai da yagirgiza yasoma juyawa
Ƙofa tanufa a guje tana sakin wani ƙara me firgitar wa, tana riƙe handle ɗin ƙofan sai wani irin juwa yaɗibe ta tazame ƙasa tafaɗi a ƙasa sumammiya.
Kuma duk wannan halin da tashiga da kuma ƙaran da tasaki babu inda be amsa ba a gidan, amma kuma babu wanda yaji ta, har ta su Suhaib da suke cikin gidan basu san meke faruwa ba.
.
_plz ku riƙa yin comments da yawa wlh shi ke ƙara min ƙwarin gwiwa._
_yanzu wasan zai so ma, ku dai kuji gaba da bi na a sannu alƙalami na ✍️ zai warware muku duk abinda kuke son sani._
*Jikar Lawali ce* ❤️
[12/31/2020, 10:35 PM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????
????????????????????
????????????????????
*RAUDHA*
????????????????????
????????????????????
????????????????????????????????????????
*MALLAKAR*✍️
_Nafisat Isma’il Lawal Goma_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO????*
“`®Ɗaya tamkar da Dubu????✓“`
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*????
*F.W.A????/*
_wannan shafin naku ne masoyana na Wattapad, ina jindaɗin yanda kuke suburbuɗo min comments, ku ci gaba da gashi Ni kuma zan ci gaba da sambaɗo muku me daɗi, ku sha sha’anin ku da wannan ɗin????_
.
*NOT EDITED* ___________________________????
*SEASON NINETEEN*
_______???? Bata farka ba sai da hasken rana yabugi fuskar ta sannan ne tafara buɗe idanuwan ta tana lumshe su, juya mata wajen yake yi duk da kuwa bata san takamaiman inda take kwance ba, ta ɗau tsawon mintuna goma kafin tatashi zaune tana riƙe kanta da yayi mata nauyi sosai yake mata ciwo
Mamaki sosai tayi ganin ta bakin ƙofa a kwance sabida ko kaɗan bata tuna abinda yafaru jiya ba, komi ya shafe mata kamar babu shi a ƙwaƙwalwan ta
Daƙyar taɗaga kanta tasauke a agogon dake manne a ƙusurwan bangon ɗakin, idanuwanta ta fid do waje ganin ƙarfe 11:10am. yanzu, Kuma ƙarfe goma yau take da lectures tunda kafin takwanta sai da taduba tantable
Tun sassafe da Suhaib zai fita yazo yabuga ƙofan nata don yatashe ta, har yagaji da bugawa yatafi sabida a tunanin sa bata da Lecture ɗin safe ne
Shiru-shiru Farida zata ji ta sauko amma kuma babu RAUDHA babu alamun ta, itama sai tahayo tay bugun duniya but RAUDHA ko kaɗan ba ta jin su, wani irin barci take yi wanda tayi nisa da duniyar mu, dole Farida tasauka tatafi tunda taƙi buɗe ƙofan.
Wani gauran numfashi RAUDHA tasaki kafin tajanye hannun ta a kanta tamiƙe a hankali jikin ta kamar anyi mata duka, ko kaɗan bata jin ƙarfi a jikin ta amma haka nan talallaɓa tashiga Toilet tayi wanka tafito, cikin sauri take yin komin ta duk da kasalan dake jikin ta
Shiryawa tayi cikin dogon wando fari ƙal me guntun skert a saman sa kalan orange, sai tasanya rigan shi me gajeren hannu da igiyoyi a gaban anyi ado dashi, itama rigan orange ne amma kuma akwai ɗige-ɗigen fari a ƙasan rigan da kuma saman rigan, me hula ne don haka ta ɗauka tasaka akanta yayinda ta cure gashin ta a ƙeya, wannan dalilin ne yasaka tuntun gashin be shiga cikin hulan ba yafito waje, Sandal shoes tasaka fari tare da Socks, haka ma Wrest watch ɗin ta da HangBag ɗin ta duk fari ne, sannan sai takanga faskeken eyeglasess na Robber a baby face ɗin ta fari tarr ana ganin idanun ta tamkar ba Glasses tasaka ba
Ƙofa tanufa tabuɗe tafice, ahankali take taka Steps ɗin tana riƙe da ƙarfen benen, tana sauka tayi hanyan ƙofa da ninyan fice wa
Farida dake zaune tana hangen ta takira ta
“RAUDHA ina zaki baki karya ba?”
Ɗan juyo wa tayi takalle ta, sai yanzu ita takula ma da ita tunda tana ɗaya side ɗin ne na cikin parlour’n, wanda babu yanda za’a yi tahangi me sauko wa daga sama sai idan mutum na cikin parlour’n
“Bana jin yunwa”. Tafaɗa ahankali tana yin gaba batare da ta jira amsar ta ba
Kafaɗa Farida taɗage kafin tasoma kwaɗa ma House girl ɗin ta kira
Nan da nan tagurfana a gaban ta
“Yauwa Ester hau sama ki gyara ma RAUDHA ɗakin ta tunda ta fito”.
“Ok Ma’am”. Cewar Ester tare da rusunar da kanta alamun girmamawa sannan tawuce saman.
????????????
A cikin mintuna ƙalilan RAUDHA ta’isa school ɗin sabida gudun da ta sharara, tana yin parcking tafito tarufe motan tanufi department ɗin su
Koda ta’isa ta tarar akwai Malam acikin class ɗin, shiga tayi ta ƙofan baya tazauna taciro Tap ɗin ta tasoma sauraron karatun nasa
12:00pm. Na cika yafice wani yashigo
Duk karatun yau RAUDHA bata wani fahimta sosai, sabida sosai take jin babu daɗi a jikin ta, ƙarfin jikin ta yaƙi dawowa Sai kuma tana jin kamar ana buga mata guduma akai lokaci-lokaci, sannan sai tariƙa jin kamar da mutum kusa da ita ana yawan motsi, idan ta juya sai taga babu kowa tunda dama acan bayan tazauna, that’s why bata maida hankalin ta sosai kan karatun ba