SARAN BOYE COMPLETE

No. 70
…………Sai dai kuma ɗagowar da zaiyi cikin matsanancin fushi sai idonsa akan Momynsa daya yasar a ƙasa. A matuƙar razane yace, “What!!. Momy! Innalillahi wa’innalillahirraji’un”. Cikin karkarwa jiki ya shiga bin ɗakin da kallo, tabbas daga shi sai ita ne, hakan na nufin ba Mira ba. Ƙirjinsa ya sake bugawa da ƙarfi. Yay azamar jawo rigarsa dake gefe danya saka Madam Chioma da ALLAH yaba damar tashi tai saurin riƙe masa hannu. Dan ita haukanta gaba ɗaya bai nuna mata maganinta baya aikiba. Faɗa masa tayi ajiki tana faɗin, “Haba my boy ya kake abu kamar wani…….”
Ai kafinma ta ƙarasa ya sake hankaɗata da rawar jiki. “Momy kina lafiya kuwa? Ninefa Yoohan?! Kodai kinsha barasa ne?!”.
Duk da mamakin yanda yakeyi ya fara sata dawowa hayyacinta, ga zafin maguzar daya sake mata hakan bai hanata sake nufosa ba. Hankalin Yoohan ya sake kololuwar tashi, dan shi yafi tunanin Maman tasa bata a hayyacinta ne. Ta sake riƙe rigar daya ke ƙoƙarin sake kai hannu ya ɗauka tana wani narkewa hawaye na zirara mata. “My boy kaine mafarkina. Kai ne farin cikina. Tunda ka kai shekarun girma ka ɗauke hankalina ga kowanne namiji a duniya. Hatta da papanku baya birgeni gaba ɗaya duk da auren soyayya mukayi. Please masoyina kazo na baka zumar da wata a duniya bata taɓa baka itaba, na maka alƙawari……..”
Duk yanda Yoohan yaso jurewa yama mahaifiyar tasa uziri ya kasa, dan haka ya fisge hanunsa data riƙe wani matsanancin tsoro na sake kamashi. Da sauri ya nufi hanyar ƙofa danya kuɓuta. Sai dai kuma ya sameta gam alamar ta kulle. Sunayen ALLAH ya shiga kira babu ƙaƙƙautawa, yay azamar kaucewa ganin ta sake nufoshi ido rufe. Dan har ta cire rigar jikinta tana ƙoƙarin cire wandon ma.
Wata azababbiyar ƙara da hatta Miracle da Blessing dake ƙasa a laɓe sai da suka jiyosa ya daka mata.
“Momy!!!! Are you mad?!!” Ya faɗa yana hankaɗata da iya ƙarfinsa da matsanancin fushi dan gaba ɗaya hankalinsa ya kai ƙololuwa a tashi. Sai ko gata a ƙasa wanwar. Wata wahalalliyar ƙara ta saki saboda faɗawa datai akan hannun damarta.
Ya cigaba da magana cikin fushi na ficewar hayyaci. “Wane irin ruɗaɗɗen al’amarine haka momy? Momy na tabbatar wlhy baƙya cikin hankalinki. Ninefa ɗanki Yoohan. Mikike shirin aikatawa haka?!!…….”
“Cikar burina John. Idan har bakai tarayya dani ba zan iya halaka Yoohan. Dan ALLAH ka daina ɗaga murya kazo gareni. na maka alƙawarin a yau duk ƙishirwarka ta shekara da shekaru sai na gusar maka da ita, nima ka gusarmin da taw……”
Da sauri ya tura yatsunsa cikin kunneta alamar baya buƙatar jin kalamanta. Sai da ya fahimci tayi shiru sannan ya nufeta. Da wani irin zafin nama ya kai hannu ya fisge key ɗin ɗakin daya hanga a yatsan hannunta. Ƙara ta saki dan taji zafi. Shiko ko saurarenta baiyina ya nufi ƙofa ya buɗe ya fice. Rasa inda zai dosa yayi a sashen nasa. dan ko ina a kulle yake. Cikin azama ya nufi ƙofar falon ya buɗe dan tabar key ɗin a jiki. Yana buɗewa tana fitowa daga ɗakinsa da jan jiki tana kuka da roƙonsa karya tafi.
Da wani irin mugun sassarfa ya fice yana karasa saka t-shirt ɗin daya fito da ita a hannu. Wani irin mahaukacin jiri yakeji, kansa tamkar zai tarwatse saboda firgici. Da steps bibbiyu ya sauka a benen. Hakan yasa Miracle dake ɓoye fitowa ta biyosa da sauri tana ƙwala masa kira. Yana gab da ficewa ƙofar falon gaba ɗaya ta riƙo masa hannu. A wani irin juyowa tamkar wani walƙiya yayi sai jin saukar tagwayen maruka tayi a duk kumatunta. Kafin ta dawo hayyacinta ya hankaɗata ya fice abinsa duhu na mamaye masa cikin idanu. Hakan yasa sam ya daina ganin hanyar da yake ajiye ƙafa da ɗaukewa……..
★★★
A hankali yake buɗe idanunsa ya saukesu akan Omar dake a kujera zaune. Nauyin da sukai masa ne ya sakashi sake maidasu ya lumshe a hankali.
“Sannu Son”.
Muryar Dr Shikurah ta shiga kunnensa. Sake buɗe idon yayi a hankali yana mai juya kansa kaɗan ya kalleta itama. Babu zato sai kawai sukaga hawaye na gangaro masa ta gefen ido. Da ga ita har Omar dake jera masa sannu shima a tsorace suke kallonsa. Dr Shikurah ta shiga jera masa tambayar ko wani waje na masa ciwo ne?.
Karan farko yay guntun murmushi mai ciwo da ƙunan zuciya. Dan ya tabbatar da ciwon da yakeji a zuciyarsa gara ace duk jikinsane ke masa wannan ciwon da raɗaɗi zaifi masa sauƙin ɗauka. Yunƙurawa yay a hankali zai tashi zauna. Sara masan da kansa yayine ya sakashi saurin dafewa yana faɗin, “Ya ALLAH!”.
Da sauri Umar ya riƙosa. Yana faɗin, “Dude be careful mana”. Yayinda Dr Shikurah kuma ta gyara masa filo Omar ya jinginasa a jiki itama tana jera masa sannu tamkar zata fasa kuka. Dan har ikin ranta takejin zafin halin da yake ciki. Gyara masa drip ɗin da ake ƙara masa tayi, kafin ta dubi Omar da shima dai yana cikin tsantsar damuwa. “Omar kodai allurar za’a sake masa ne? Barcin kamar bai ishesa ba”.
Kafin Omar yay magana Yoohan yay saurin girgiza kansa. “A’a Momy babu buƙatar haka. Bazan iya sake kwana a ƙasar nan ba, dan zuciyata zata iya bugawa…..”
Cikin katsesa Umar yace, “Taya zakai maganar barin ƙasa kana a cikin wannan halin? kana son yin wasa da lafiyarka ne komi Yoohan?”.
Kallon Umar ɗin yayi da idanunsa dake jajur yana wani murmushi mai ciwo, gazafafan hawaye na ziraro masa a saman kumatu. “Bazaka ganeba Omar, duk bayanin dazan maka bazaka fahimceni ba. Tafiyata ba itace wasa da lafiyata ba, zamana a ƙasarnan shine wasa da lafiya ta. A yanzu haka inajin tamkar na rufe ido naga bana numfashi saboda ruɗanin da ƙwaƙwalwata take a ciki. Umar ni Momy zata n……”
Sai kuma ya fashe da kuka mai cin rai batare daya iya ƙarasawa ba. Jikinsa sai wani irin rawa na ɓacin rai yakeyi dan Yoohan akwai zuciya dama. Hankalin Dr Shikurah da Omar ya sake ƙololuwar tashi. Umar ya riƙo hannunsa yana lallashinsa. Amma sam hankalin Yoohan baya a jikinsa gaba ɗaya. Babu abinda ƙwalwarsa ke tariyo masa sai abinda ya faru shi da Momynsa tamkar a film. Gaba ɗaya ƙwalwar kansa da tunaninsa neman jirkicewa suke.
Wani irin bahagon numfashi ya fara ja da ƙyar alamar motsawar Asthma ɗinsa. Hankalin Omar yakai matuƙa a tashi, dan yasan Yoohan nashan wahala akan Asthma ɗinsa. Takan daɗe bata tashi masa ba. Amma duk lokacin data motsa yana shan wahala sosai. Gashi shi koma yawo da inhaler bayi yakeba saboda yana jimawa bai yiba.
Ganin abin babbane yasa Dr Shikurah tambayar Umar a ruɗe.
Shina Umar ɗin a rikice yace, “Mom yanada Asthma, sai dai tana jimawa bata motsa masaba. Da alama yanzu kuwa itace”.
“Hasbinallahu wani’imar wakil”. Dr Shikurah ta faɗa tana fita da hanzari.
Babu jimawa sai gata ta dawo suka shiga bashi taimakon gaggawa ita da Omar. Basu ƙara samun nutsuwa ba sai da Yoohan ya koma barci mai nauyi.
Cikin sauke tagwayen ajiyar zuciya Dr Shikurah tace, “Omar anya kuwa ba wani abune mai girma ya firgita ɗan uwanka ba?”. Duk da Umar yasan ainahin abinda ya faru. saboda Blessing ta sanar masa ta waya sai ya ɓoyema Dr Shikurahn. “A’a Mom, faɗowar Momynsa daga benen ne kawai ya firgitashi”.
“ALLAH sarki, ai jikin nata itama da dauƙi, duk da bata farfaɗo ba har yanzun, amma Alhmdllh bataji wani mummunan ciwobama kamar yanda mukai hasashe”.
“ALLAH ya basu lafiya”. Umar ya faɗa a taƙaice. Daga haka Dr Shikurah ta fita daga ɗakin.
Fitar Dr Shikurah ɗakin tayi dai-dai da shigowar Papa da Uncle Joshua cikin asibitin. Dan isowarsa kenan ƙasar ya iske gidansa a harmutse. bayan ya tambayi dalili aka sanar masa Yoohan ne ya yanke jiki ya faɗi batare da ansan dalili ba. Wajen biyosa kuma madam Chioma ta faɗo daga bene. (Dan su iya abinda suka gani kenan. Miracle da Blessing ne kawai sukasan ainahin abinda ya faru. Su kuma babu wanda yace komai. ita dai Blessing tsoron rasa aikinta takeyi. Itako Miracle bamusan dalilinta na ɓoyewarba).
Sun sanar masa Richard yazo gidan a daidai faruwar al’amarin, shine ya tafi da su asibiti su duka. Wannan shine dalilin zuwan papa a sibitin da hanzari.
Kasancewar Yoohan sannan likita duk ma’aikatan sun sanshi. papa na ambatar sunansa da kuma tabbatar musu shi din mahaifinsane ko sai gashi an rakosa har office ɗin Dr Shikurah. Itace ta fara kaisu ɗakin da Madam Chioma ke kwance a sume har yanzun, sunata dai tsammanin farfaɗowarta. Duk an mata dressing ciwukan da taji, tare da gyara mata tsagewar ƙashi data samu a hannunta.
Papa harda su hawaye yayi na tausayin matar tasa. Dan yasan yanda take tsananin son ɗan nasu. Suko su Dr Shikurah sai faman masa sorry sukeyi. Daga haka suka fito zuwa ɗakin da Yoohan ke kwance shima. Anan ma hankalin papa ya tashi da ganin halin da yaronsa yake a ciki, dan tashin Asthma ɗinsa sunsan bata musu daɗi.