NAMIJIN DUNIYA COMPLETE NOVELTHE WORLD MAN COMPLETE NOVEL

THE WORLD MAN (NAMIJIN DUNIYA) COMPLETE NOVEL

Bansamu nayi editing ba koda kunga typing errior aiki nike

Rashin comments ɗinku da votes shike sani ƙinyin typing saboda banajin daɗin irin abinda kukemun koba komai na tsaya dogon lokaci ina typing danna farantamuku amma ku comments and votes ya gagareku na ƙone a hannuna kullum se an wanke hannun amma haka na daure inayi amma ku comments dabe wuce layi biyarba shi kuke kyashin yi.

Votes and Comments
Plz share to others

_*Daga Alƙalamun ƴ???? *MAN OF THE WORLD*
(NAMIJIN DUNIYA)

MALLAKIN
REAL EESHOW

HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCI…

BOOK 1

PAGES 1️⃣3️⃣➡️1️⃣4️⃣

    "Hmmm banyi mamakin jin irin abubuwan da suke fitowa daka bakinba domin kincemun ke kishiyar maman Inteesar ce jin kalamanki akan Inteesar yaƙara tabbatarmun dakece babbar mara tarbiyya da har kika iya fitowa waje gurin surikinki batare da mijinki yasani ba inma kina tinanin wannan wasiƙar banzan da kika gama karantamun  tayi tasiri a zuciyata to ba haka bane domin ni ba abinda kalamanki suka ƙaramun  face jin wata sabuwar soyayyar abar ƙaunata Inteesar ta inda a zuciyata nikejin idan na rasa Inteesar zan shiga babbar matsala saboda haka gobe insha Allahu idan mahaifana sun tashi zuwa da kuɗin aure zasu taho domin banaso bikinnan ya wuce sati biyu  kodon ke ɗiyarki kuma da kike magana  koda na rasa matar aure a duniya bazan taɓa auren wannan kucakar yarinyar ba".

sosai hankalin Uwar gwarama yayi ƙololuwar tashi tace”anyako ɗannan kana cikin tinaninka kuwa ina ƙoƙarin temakonka daga sharrin wa’innan miyagun mutanen kana ƙara shigewa anya ba shanyeka sukayiba kuwa”.
murmushin daya ƙara fito da tsantsar kyawunsa yayi tare da cewa”Ummah kenan indai wannan temakon ne banaso nagode se anjuma”.
yaƙarasa zancensa tare da yin gaba yabar Uwar gwarama baki sake muryar Hauwa’uh taji a bayanta tace”ke yanzu bakiji kunyaba kin zubar da girmanki a banza ba biyan buƙataba amma gaskiya naji daɗin irin maganganun daya faɗamiki nasoma yaci mutuncinki wlh”.
“keeeh zanci mutuncinki munafuka ashe laɓe kikemun kenan to kinyiwa Saratu tsinanniyar yarinya wadda bata gaji arziƙiba “.
dariya Hauwa’uh tayi ta wuce da harara Uwar gwarama tabita tare da yin tsaki tace”tsinanne yaro kawai ko kanason Jamilah ko bakasanta baka da matar data fita zanyi maganinka dani kake zance”.
nan taita masifarta daga ƙarshe ta nufi gida.

Zaune suke shida doctor Shuraim suna ƴar hira akayi knocking wata matashiyar Nurse naga ta shiga hannunta riƙe da files cikin girmamawa taƙarasa cikin office ɗin bakinta ɗauke da sallama amsamata sukayi cikin nutsuwa ta nufi gurin doctor Shuraim tamiƙamasa files ɗin hannunta sannan ta juya ta tafi hannu yasa ya zaro takarda tare da warwareta ya duba gani yayi abinda suka saba gani ne kullum ba canji sema abinda yaƙara ƙaruwa sosai yaji abokinnasa yaƙara bashi tausayi ya miƙamasa tare da cewa” a zahirin gaskiya abokina bazan ɓoyemaka ba magungunan da kakesha yanzu summa dena yimaka aiki gabaki ɗaya ina ganin zancennan dai da bakaso shine mafita gaskiya domin abinnaka yayi worst sosai domin tunda nike a rayuwa ban taɓa ganin mutum me matsala kamar takaba kayi tinani abokina”.
sauke gauron numfashi Namijin duniya yayi tare da miƙewa kamar wanda aka yimasa dole da yayi magana yace”a situation ɗin da nike nace zanbi shawararka akwai cutarwa gaskiya bana tinanin haka zeyiwu”.
“eh hakane abokina nasan da cutarwa amma inba hakaba ba wata mafitar dan situation ɗin da kake inbakabi shawarar nanba to akwai babbar matsala”.
miƙewa Namijin duniya yayi jiki ba kwari tare da ficewa yana fita ya nufi inda guard ɗinsa suke jiransa kafin yaƙarasa har sun buɗemasa mota yashiga zama yayi akan kujera tare da lumshe sexy eyes ɗinsa da sukayi mugun canza kala yashiga tinani akan maganganun doctor Shuraim har suka isa gida bemasan sun isaba sejin drivernsa yayi yace”Sir mun iso”.
ba tare daya buɗe idanunsa ba yace”ok”.
fita yayi ya buɗemasa a hankali ya buɗe rinannun sexy eyes ɗinsa da suka yimasa nauyi yayinda yikejin wani irin yanayi a jikinsa me wuyar fassaruwa bazato yaji wasu hawaye masu zafi na fita daga idanunsa a zuciyarsa yace”ya Allah kabani ikon cinye wannan jarabawar”.
saurin share hawayensa yayi ya zura ƙafarsa waje a hankali yafita tare da saka baƙin glass a idanunsa saboda bayason granny ko Abbih ɗinsa wani ya fuskanci yana cikin tsananin damuwa yashiga tafiya .

“Gaskiya ni Mum banaso nagama ɓata time ɗina sannan naga guy ɗin wani ajawo akwai ƙura wallahi Mum dan kinsan bani dakyau za’ah yita taƙarene dani dake ehe”.
“nasani Mima amma ki tsaya kigansa idan bemikiba kiyimun duk abinda kikaga dama domin nima inada terget akan yaron”.
taɓe baki tayi tana kallon mahaifiyartata a wani sheƙe suna cikin magana wayar Mimah tayi ƙara ɗagawa tayi tare da cewa”ganinan zuwa Husy ku tanadarmun wine ɗina nima”.
tana gama faɗin haka ta kashe wayarta tare da kallon Mum tace”Mum ni zan wuce Club su Husy nacan suna jirana munada shagali”.
“wai Mimah har yanzu baki denashan giyaba da bin mazan da kikeyiba kenan a turaibako”.
shiru Mimah tayi da Mum sema miƙewa datayi tare da cewa”next time ma haɗu dashi”.
taƙarasa zancenta tare da ficewa saurin bin bayanta Mum tayi.

Kaciɓus sukayi da Namijin duniya dake ƙoƙarin shiga part ɗin sosai Mum taji daɗin ganinsa cikin kwarkwasa irinta ƴan bariki tace”Son harka dawo”.
saurin waigawa Mimah tayi dan ganin wanene Son ɗin kaciɓus tayi da haɗaɗɗiyar fuskar Namijin duniya wow tafurta a zuciyarta tace”gaskiyane dole Mum tace nayimata duk abinda naga dama indai bemunba amma guy ɗinnan yahaɗu ƙarshene”.
yafara tafiya da niyyar wucewa yaji muryar Mum tace”Son ga ƙanwarka Mimah da nike faɗamaka Allah yayi tagama karatunta ta dawo Mimah ga Abdallah”.
tacikin glass Namijin duniya ya kalleta sama da ƙasa yaga wasu ƴan iskan kaya dasu da babu duk ɗayane a jikinta ya taɓe baki Mimah da son Namijin duniya yagama cikamata zuciya ce tayi caraf tace”sannu Yayah”.
taɓe baki Namijin duniya yayi kamar bazeyi magana ba sekuma yace”sannu”.
“yauwa Yayah”.
wucewa yayi yabarsu nan tsaye suna kallonsa saurin jan hannunta Mum Mimah tayi suka shiga ɗakin Mummy cikin zumuɗi Mimah tace”kai Mum amma gaskiya wannan karon kinyi abin arziƙi yayi sosai inada surar da duk wani ɗa namiji me lafiya yaganni dole hankalinsa ya tashi amma a tarihin rayuwata ban taɓa haɗuwa da ɗa namijin daya shiga raina lokaci ɗayaba se akan wannan guy ɗin kinga wani irin kwarjini dayayimun harna manta a inda nike jinayi kamarnaje na rugumesa haka na riƙaji ga wata irin muguwar sha’awarsa data dirarmun dole na mallakesa ban taɓa son abu na rasashi ba dan haka Mum wannanma ki temakeni sameshi”.
“damma bakisan wani abubane Mimah Namijin duniya shine mutum na uku a cikin jerin masu kuɗi na duniya”.
“what Mum dan Allah”.
“wallahi kuwa ke dama ina zaki sani kinata sakarci”.
“ki kwantar da hankalinki bakida wani miji bayanshi aurenki dashi kamar anyine kedai kawai ki zubamun ido kiga yadda zanyi dashi badai niceba”.
“yauwa Mummy na haka nike sonki”.
“kedai abinda nikeso dake ki kwantar da hankalinki kifara shigar gargajiya kiga abinda ze faru kawo kunnenki kiji”.
nan tafaɗamata magana suka tafa Mum tace”gobe zanje gurin boka zakisha mamaki duk girman kai irin na wannan yaron yadda zezamarmiki tamkar raƙumi da akala”.
“hhh Mum amma bakida kyau”.
“sosaima kuwa”.
“nama fasa fita bara inje infesa wanka saboda insace zuciyarsa”.
“yauwa ɗiyata”.
tana wucewa Mummy tayi wani shu’umin murmushi wanda ita kaɗai tasan ma’anarsa tabi bayanta.

AFTER 3 DAYS

Zaune yike a office yana cike files gefe guda kuma zuciyarsa ta matsamasa da tinaninta yau kwana biyu rabonda yaganta a zuciyarsa yace”anyako lafiya take kuwa”.
wata zuciyarce tace”tokai meye na damun kanka dan wannan mahaukaciyar yarinyar batazoba “.
sakin wani tsaki yayi meƙara tare dasa hannu yajawo system ɗinsa yashiga duba shige da ficen ma’aikata tsaki yayi tare da miƙewa ya leƙa window hakan yayi daidai da fitowarsu Inteesar daka motar Zaid suna dariya lokaci ɗaya yaji wani abu ya tokaremasa maƙoshi ga wani irin mugun ɓacin ran dabesan na meneneba yakoma ya zauna ya cigaba da cike files ɗinsa gefe guda kuma zuciyarsa ba abinda take se tafarfasa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Leave a Reply

Back to top button