NAMIJIN DUNIYA COMPLETE NOVELTHE WORLD MAN COMPLETE NOVEL

THE WORLD MAN (NAMIJIN DUNIYA) COMPLETE NOVEL

5:00pm

Zaune Abdallah yike yana danna phone ɗinsa kallo ɗaya zakayimasa kasan tinani kawai yikeyi a guest house ɗinsa Ahmad ya buɗe ƙofar falo har ya ƙaraso inda yike Namijin duniya kasan cewa yayi zurfi a cikin tinani domin ko sallamar da Ahmad yayi be amsaba taɓashi Ahmad yayi da sauri ya ɗago ya kalli Ahmad dafashi Ahmad yayi tare da cewa”Abdallah meyasa koda yaushe kakeson ɓoyemana damuwarka ne tin muna yara baka da abokan da suka fimu inbaka faɗamana damuwarkaba wazaka faɗawa”.
sauke numfashi Namijin duniya yayi tare da cewa”bakomai Ahmad inda dashi dana faɗamaka”.
“ohk to meyasa kasa na kori mutum haka kurum ba dalili dafa wannan aikin sukecin abincifa shida iyalansa”.
sauke numfashi Namijin duniya yayi tare da labartawa Ahmad komai da Inteesar tayi masa murmushi Ahmad yayi tare da cewa “haba My Man aiba haka yakamata kayiba ai kan yarinyar yakamata ka huce “.
kallonsa namijin duniya yayi alamun yana san sanin mezaiyi mata murmushi Ahmad yayi tare dakai bakinsa saitin kunnensa yayimasa raɗa wata magana wadda nima kaina Real eeshow bansan meya faɗamasa ba lokaci ɗaya namijin duniya yasaki wani murmushin gefan baki tare da furta “amma Ahmad kana ganin ba raini a wannan shawarar taka kuwa ?”.
“wanne irin raini My Man ai wannance kawai hanyar da zaka rama kenan a ganina”.
shiru Namijin duniya yayi kafin daga bisani ya saki wani ƙayataccen murmushi saboda se yanzu yagane abinda Ahmad yike nufi cikin jindaɗin shawarar Ahmad ya furta “shiyasa nike
ƙara ƙaunarka saboda kai akwai kawo light”.
dariya su dukansu sukayi sai a sannan namijin duniya yaɗanji ranshi yayi sanyi nan suka koma hirar bikin Adam daga bisani Ahmad ya ɗaga waya yayi sai kuma ya aje naga yayi murmushi
Babu ɓata loƙaci sakataren Ahmad yashigo shida wani ɗan dattijon mutum abayansa.

Zama sukayi a ƙasan carpet cikin girnamawa sakataren Ahmad yace”ranka yadaɗe gashinan”.
“ohk we can go”.
nan yafice yabarsu da Abbah daketa ƴan kalle-kalle saboda tinda yike bai taɓa ganin tsararren guri ba kamar wannanba saboda falon yagaji da haɗuwa komai na more rayuwa akwaisa a falon gefe guda kuma tanƙama-tanƙaman photunan Namijin duniyane a kowanne bango na falon
dakyar ya ɗauke idanunsa daga kalle kalle yamaida ƙasa cikin rawar jiki ya gaishesu Ahmad ne kawai ya amsa namijin duniya kuwa kallo ɗaya yayi masa yakauda kai ya taɓe baki a zuciyarsa yace”dama wannan ne mahaifin dirty girl ɗinnan yarinyar nan mara tarbiyya dubeshi wani iri”.
yana cikin wannan zancen zucin yaji Ahmad yace “dama abinda yasa kaga
na sallameka agurin aiki babu laifin dakayi dama wata sabuwar dokace tafito mun dena ɗaukar tsofaffi da wa’inda basuda kwalin degree amma idan kana da wanda zaka kawo mai kwalin degree tom ka kawo sai yamaye gurbinka ko mace ko namiji amma bada Comphany ɗina za ai aikiba na Namijin duniya ne zasu ɗaukesa”.

Cikin farin ciki yaɗago ya kallesa yana washe baki Abbah yayi tare da cewa”to ranka yadaɗe Allah yasaka da alkhairi nagode Allah yaƙara arziƙi amma banida wani namiji dayayi wannan karatun sai dai mace zan iya kawota?”
Murmushi Ahmad yayi tare da cewa “ai babu komai Baba kakawota inhar tana da degree”.
shiru Abbah yayi daga bisani yace”ammafa wani hanzari ba guduba ita da ƙawarta suke komai Alhaji Zannah ne yayiwa yarinyar tawa komai be kamata na samarwa tawaba itakuma tashi nayi musu hakaba koba komai be taɓa ware tawaba abawa tashin kawai se a kyale Inteesar ɗin”.
damm ƙirjin Namijin duniya yabayar daketa shan ƙanshi jiyayi kamar yasamusu baki amma saboda tsabar girman kai da izza bazaka gane yaji wani abuba yacigaba da operating ɗin phone ɗinsa jiyayi Ahmad yace”a’ah Babah ka kawosu kawai gabaki ɗayansu a kawosu sesuyi interview in Allah yakaimu gobe”.
Wani farincikine ya lulluɓe Abbah nan yadungi zabga godiya yatafi yana tafe yana murna ganin aikinsa yadawo bai suɓucemasa ba.

Murmushi namijin duniya yayi wanda shikaɗai yasan ma’anarsa yabawa Ahmad hannu suka kashe Ahmad yace”to tazo hannu saura plan ɗinmu na biyu ita harta isa taja da ɗaya daga cikin ɗan cliff ɗinmu Tripple A saura shawarar Adam shima aji tabakinsa daganan semuyi tsare-tsaren biki”.
“toh tashi muje”.
nansuka tafi yayinda ran Namijin duniya yayi fess ji yike kamar yajawo gobe tayi.

Washe gari tin safe Namijin duniya ya shirya ko breakfast be tsaya yayiba yafito yana ɗaura agogon rolex a hannunsa yaga Abbih ɗinsa zaune a dining gefensa Mummy zaune ƙarasawa yayi gurin Abbih ɗinsa yayin ɗinsa sannan yace”Abbihna ka tashi lafiya”.
“lafiya ƙlau Babana harka sakko da wuri haka”.
“eh sauri nike zanyi wani abu”.
“okay yanaga yau kana cikin farincikiko ko suruka aka yimun”.
wani smiling Namijin duniya yayi wanda ko Abbih ɗinsa rabon dayaga yayisa harya manta yaji yace”Abbih the weather is so nice today”.
murmushi Abbih yayi nanya gaida Mummy data tsaya kallonsu sannan yayimusu sallama yafita ba tare dayaci komaiba.

Yana isa ya wuce Office ɗinsa direct koda yashiga yaja kujera yazauna tare da lumshe ido yayi shiru yashiga dunuyar tinani jiyayi anbuɗe ƙofa
sakatariya ce tashigo sai faman karai-raye karai-raye take da jiki dukda ƙamas take ga shegun riga da wando data saka sun matseta rabin breast ɗinta da suka zube kamar silifas a waje tasha heavy makeup sai taunar cingam take kamar karuwa baki ta saki ganinsa zaune akan kujera har yazo gani tayi shikaɗai se murmushin gefan baki yake lokaci ɗaya taƙara cigaba da karairayarta dan ita a tinaninta ita yikeyiwa taƙarasa gabanshu cikin yauƙi da iyayi irin na ƴan bariki tace”yallabai
barka da hut meza’ah kawo maka bayan coffee”.
taƙaraasa zancenta tana ƙuresa da kallo
Gyara zamansa yayi ba tare daya kalleta ba a daƙile yace”yau bana buƙatar komai”.
yafaɗa sai kallonta yaƙarasa zancensa tare da ƙara sakin wani murmushin
Ganin yanamata murmushi ne saitaga kamar da ita yake tako ƙara gyara gaban rigarta tana tsaida shafaffun nonuwanta wa’inda suka kwanta kamar lawashin albasa tana tunkarosa gani yayi tana matsowa gabdashi dan-danan yatattaro ɓacin rai yaɗorawa fuskarsa yahaɗe rai murtuke kamar bashine yagama murmushi yanzuba tana ganin haka tayi saurin wayencewa taƙarasa cikin freidge taɗauko cups tatafi dasu zata wanke tana fita taja dogon numfashi “yau danayi gisgirin taɓa oga dana shiga uku ashe murmushin danaga yanayi badani yakeba to dawa yike danni dai bazan taɓa bari Oga ya airi wataba koda zan rasa zanin ɗaurawa wallahi dole inƙara zuwa gurin boka na bayan tsauni yayimun maganinshi yau naso na gwadamasa irin tawa soyayyar”.
take faɗa aranta nanta wuce tazauna tana maida numfashi ta ɗauki wayarta tashiga dialing number ƙawarta bugu ɗaya ta ɗauka tare da cewa!!!!!

Idan naga ruwan comments da votes zakuga cigaban kullum ta Allah har sau biyu a rana idan ban ganiba daka wannan na dena wannan book ɗin.

Votes and Comments
Plz share sisters and brothers to others fisabilillah

_*Daga Alƙalamun ƴa???? *THE WORLD MAN*
(NAMIJIN DUNIYA)

MALLAKIN
REAL EESHOW

HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCI…

BOOK 1

PAGES 0️⃣5️⃣➡️0️⃣6️⃣

        "Lafiya irin wannan kira haka da sassafiyar nan kota warune".

“hmm ai dole na kiraki hankalina ne Zuby yayi mugun tashi”.
“faɗamun mana Feenah”.
“yau ina zuwa na tadda Oga harya zo yanata murmushi da farko na zata dani yike Allah yasoni da harnaje in rungumesa nayi saurin wayancewa saboda kingako yadda ya haɗe rai lokaci ɗaya da tini nasamu matsala bakiji yadda naji ba saboda tsoro nike Allah yasa dai ba wata ya haɗu da itaba dan wallahi Zuby bazan taɓa jurar ganin Abdallah da wata ba ko zan rasa zanin ɗaurawa sena nisantashi da mata matsawar bani ze aura ba”.
“kece Feenah tin yaushe nike cemiki koda muna yin amfani da maganin Bokanan to dole kema ki riƙa nunamasa kefa kina sonsa akwai wasu kaya danaga Hajiya Riga ta ɗakko ƴan gumamane masu kyau anjuma kizo muje gidan ki zaɓa zakisha mamakin yadda ze riƙa kallonki kamar wani magnet haka ze riƙa binki da ido saboda zasusa sha’awarsa ta motsa kinga dakanan kekuma sekisan yadda zakiyi har yayi sex dake dakanan zamu kamashi a hannu ta hanyar cemasa kinada ciki kamar yadda yike popular once bazeso ace zamu tonamasa asiriba duniya tasani kinga semuyi amfani da wannan damar muce masa sede ya aureki inba hakaba mu tona masa asiri”.
“wow gaskiya ƙawata kinyi dogon tinani sosai yanzu zan cigaba da nunamasa inasonsa dukda nasan ya gane hmmm inyazo hannu ze gane kurensa dan yadda yabamu wahala semun fanshe”.
“ai dole yagane kurensa Allah yasa karki samu duniya ki manta dani danke ɗan tsakoce samu kaƙi dangi kina samun abun duniya zaki yimun ƴan ta waye”.
“haba Zuby aina dena yimiki haka ai anzama ɗaya tare dake zamuci duniyarmu a tsinke ko banza a riƙa nunomu a mujallu”.
“toh ƙawata bara na tashi tunda kin tasheni “.
“toh dan Allah da kinjemun gurin bokan danni banga alamun aikinnan yanayiba ƙinji ta bakinsa”.
“aiko kema kince wani abu bara na shirya senaje gurin wani Bokan danaga su Mum ɗina suna zuwa aikinsa kamar yankan wuƙa haka yike ammafa sekin kawo wani abu”.
“kema dai ƙawata kinsan da wannan Bokan kikasa mukaita kashe kuɗi gurin wannan da aikinsa bayayi bara inyimiki transfer kiyi sauri dan Allah”.
“toh aikeɗince ƙawata bakya sakin kuɗi sosai tayayako zankaiki gurin wannan da manyan mutane ke zuwa shiyasama ban sanar dakeba”.
“kinsan dai ko nawane zan iya kashewa matsawar Namijin duniya ze aureni a riƙa kirana ta Mrs Namijin duniya ai zan bada ko nawane yanzu bara nafara turamiki idan bazasu isaba ki kirani”.
“toh ina jiranki dan inyi maza indawo”.
“toh”.
nansukayi sallama ta gyara zamanta ta cigaba da haɗa files ɗin da zata shigarwa da Namijin duniya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Leave a Reply

Back to top button