NAMIJIN DUNIYA COMPLETE NOVELTHE WORLD MAN COMPLETE NOVEL

THE WORLD MAN (NAMIJIN DUNIYA) COMPLETE NOVEL

Ɓangaren Zuby ko tana kashe waya ta tintsire da dariya mahaifiyarta dake kusa da itace ta kalleta alamun dariyar metake tsagaitawa da dariya Zuby tayi tare da cewa”yanzu karyar zata turon da kuɗi Mum semuje gurin bokannan da kikeso muje ita inbanda itama tinkiyace ta ina zan bari inaji ina gani ta auri Namijin duniya bayan nina fara nunamata shi a rayuwarta tasameni ina sakatariyata tasa aka koreni a tinaninta kyaleta zanyi to wallahi yanzune ko zatasan wutsiyar raƙumi tayi nisa da ƙasa zan nunamata na rigata zuwa duniya koya kikace Mum”.
washe baki Mum tayi tare da cewa”aiko yanzu zanzo inkira Hajiya Mansura ta shirya muje ayimiki aikinnan dama kuɗine sukai tsaiko to yanzu Allah ya kawo na banza bara naje na wanki bayan tukunya a ɗaura a leda seki kaimata a matsayin maganin sede taga anayi Namijin duniya mijinkine ke kaɗai Zubyna”.
“yauwa Mum”.
nan Mum takira Hajiya Mansura tasanarmata suka cigaba da harkokinsu.

Zaune take akan kujera tana wanke-wanke Khadijat na ɗaurayemata Abbah yashigo fangan-fangan ya wuce ɗakin Uwar Gwarama zaune yasameta tana ƙullin magungunan mata zama yayi kusa da ita tare da cewa”yaufa yakamata suje yarannan shine nace bara insanarmiki”.
“toh kayimata magana ammafa albashin gabaki ɗaya namune kasansu da baƙin hali kar wani lokacin ace sun faɗi”.
“toh”.
nanya fita kallo ɗaya yayimusu ya kauda kai tare da cewa”kee”.
cikin ɓarin jiki Inteesar ta miƙe dantasan da ita Abbah yike cikin ladabi taƙarasa inda yike ta duƙa tare da cewa”gani Abbah”.
“ki shirya yanzu kutafi keda Hauwa kuje ma’aikatar Namijin duniya zakuyi interview yike kome saura kuma ki nuna baƙin halin naki a canma”.
gaban Inteesar ne yayi mummanan faɗuwa jin sunan da Abbah yafaɗa dakyar ta saita nutsuwarta cikin sanyin jiki tace”toh Abbah angode Allah yasaka da alkhairi”.
jin muryar Uwar Gwarama tayi akanta tace”bar wani saurin godiya munafuka Malam baka faɗamata ni za’ah riƙa kawowa kuɗin bane”.
taƙarasa zancenta tare da jifan Abbah da wani banzan kallon daya hautsinamasa ƴan hanji cikin rawar murya yace “ayi haƙuri ai bankai ga sanar da ita bane”.
“ka gama munafuncinka”.
suna wannan zancen wata mata tashigo tashigo gidan da sauri Uwar Gwarama na ganinta tace”Hassatu badai Jummalar bace kikaga ta wuceba”.
“ita ce kuwa yanzunnan tashiga gidanta”.
“to bara naje yau koni ko ita wallahi”.
nanta wuce ta tafi tana isa gidan Jummala sukayi kaciɓus a zaure zata fita saurin riƙota Uwar Gwarama tayi cikin masifa tace”wallahi sekin bani kuɗina ina dalili ina ɗan mafari tunkan inhau ruwan cikinki ki bani kuɗina”.
“kiyi haƙuri idan nasamu zan aikomiki dasu inzo inyimiki godiya”.
“wuce muje cikin gidan kome kike dashi kibani na daidai kuɗina”.
nanta tasa ƙeyar Jummai suka shiga ta buɗemata ƙofa ganin akwati uku a ɗakin yasa Uwar Gwarama ta ɗauka tare da cewa”naɗauki wa’innan dukda nasan kuɗina basukai wannanba dama akwai ɗan tala dayace inhaɗamasa akwati zeyi aure idan na haɗamishi se inbaki sauran canjinki”.
zaro ido Jummai tayi tace”ki rufamun asiri Uwar Gwarama kayan Nura ne ya siyo ze fara haɗa lefe”.
“ko kayan waye naɗauka ɗin”.
nanta ɗauka ta tafi abinta.

Tin fitowarsu Inteesar taga yanayin Hauwa’uh kamar mara lafiya gashi tayi shiru cikin kulawa Inteesar tace”Hauwa’uh lafiyarki kuwa naga duk jikinki yayi sanyi kamar wadda wani abun ke damunta”.
“hmm Inteesar tinani nikeyi saboda Comphany ɗin da zamufa na Namijin duniya ne bakya tinanin idan yaganmufa inajin tsoron abinda zemikine”.
tsaki Inteesar tayi saboda ita harta manta da abinda yafaru tsakaninsu tace”hmm halinki yana bani mamaki Hauwa’uh mufa sukayiwa laifi ba mumuka musuba bana taɓa regreting ɗin abinda nayimasa kuma ko yanzu yakuma yimana wani abun wallahi sena rama be isa yayimana abinda Allah bemana ba irin kune marasa kishin kansu da se a takasu su kyale”.
suna wannan zancen suka ƙaraso titi suka tsaya jiran napep basu daɗe da tsayuwaba suka samu adaidaita suka hau suka tafi.

Suna sauka Inteesar taji gabanta yayi mummunan faɗuwa dakyar ta tattaro sauran nutsuwar data ragemata da jarumta ta dake suka shiga inda akeyiwa mutane interview suka zauna.

Namijin duniya dake zaune a Office ɗinsa yana ganinsu Inteesar ne yasaki wani ƙasaitaccen murmushi me cike da ma’anoni kala-kala yace”yarinya kin shigo hannu zakisan wanene Namijin duniya zaki tantwncemun waye me ƙazamun hannu cikin ni dake waye mara tarbiyya cikin ni dake”.
ya miƙe yafita bin bayansa sakatariya tayi tana tinanin ina Ogan nata zeje gani tayi sunyi hanyar inda akeyiwa mutane interview mamakine yakamata tasan ogannata baya zuwa irin wa’innan guraren bata ƙara tsinkewa da al’amarinba seda taga Ahmad da Adam suma tsaye bayansu da sakatariyansu suma tana wannan mamakin har suka ƙarasa inda su Adam suke cikin girmamawa aka shiga gaida Namijin duniya cikin takun isa suka jera Tripple Apple suka jera kallo ɗaya Namijin duniya yayiwa su Inteesar ya ɗauke kai kamar be gansuba sunzo dafda su Inteesar ganin mutane hadda tsofaffi nata duƙawa har ƙasa suna gaidasu kamar zasuyi sujjada sukuma sun wani ɗauke kai ko amsawa basayi hakan baƙaramun ɓata ran Inteesar yayiba taja tsaki karaf a kunnen Namijin duniya dake side ɗinta suna haɗa ido ta taɓe baki cikin ƙasa da murya tace”mara tarbiyya kawai da rashin sanin darajar ɗan adam”.
baƙaramun ɓaci ran Namijin duniya yaƙara yi da Inteesar ba be nuna yaji komaiba har suka shiga theater da za’ah fara interview ɗin suka zauna lokaci ɗaya idanunsa dake cikin baƙin glass suka canza kala fuskarnan taƙara haɗewa kamar hadarin kaka aka fara kiran mutane suna shigowa.

Se yamma liƙis sannan akayi kiran sunan Hauwa’uh aka kira na Inteesar a tare suka shiga theater suna shiga sun zauna kenan su Namijin duniya suka miƙe cikin gadara Ahmad yace”muntashi gobe kuzo da wuri ayimuku Muh’d ɗauki sunansu gobe dasu zamu fara”.
“toh ranka shidaɗe”.
nansuka wuce suka barsu nan sosai ran Inteesar ya ɓaci domin wa’inda sukazo bayan-bayansuma ammusu amma su saboda rainin hankali sukacemusu sun tashi Hauwa’uh ce ta faɗawa Muh’d sunansu sannan suka tafi rai ɓace.

Zaune suke a falo suna hirarsu Ahmad yace”My Man kadena damun kanka kan wannan Babe ɗin domin tarigada ta shigo hannu yanzu zata gane kurenta”.
buɗe idonsa yayi yasaki murmushin gefan baki a zuciyarsa yace”zan koyamiki hankalin da har abada bazaki sake yiwa wani makamancin abinda kikayimunba “.
dariya Adam yayi tare da cewa”akan wannan Babe ɗin nafara ganin Namijin duniya yafara tinani dolene muyi maganinta ta yadda sunansa taji seta suma”.
“wallahi kuwa ai yanzu zata fara gane kurenta”.
nansukaita hirarsu Namijin duniya ya miƙe ya nufi pridge yaɗauki bottle water yashiga bedroom yana zuwa yazauna gefan haɗaɗen italian bed ɗinsa yasa hannu yajawo loka dake kusa sa gadon yaɗauki ledar drugs ɗinsa yazauna sannan ya ɓaɓɓala yasha ya mayar loka ya kwanta tare da lumshe ido yashiga tinanin wani mugun tausayin kansa ne yakamasa lokaci ɗaya wasu hawaye masu zafi suka silalomasa yasa hanky ɗinsa ya share yanajin wani irin nauyi a zuciyarsa idan ya tino da irin ƙaddarar dake tare dashi tashi yayi yashiga toilet ɗinsa ya ɗauro alwala yashiga yin nafila yana kaiwa Allah kukansa kan Allah ya yayemasa lalurar dake damunsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Leave a Reply

Back to top button