NAMIJIN DUNIYA COMPLETE NOVELTHE WORLD MAN COMPLETE NOVEL

THE WORLD MAN (NAMIJIN DUNIYA) COMPLETE NOVEL

Tana fita yamaida sexy eyes ɗinsa kan Inteesar data duƙurshe tana zubarda hawaye yace”keeeh inkukan zakiyi ki fita waje inkingama kya shigo nayimiki abinda zan miki domin nan ba gidan mutuwa bane”.
a hankali batare data haɗa ido dashi ba ta miƙe da niyyar barin office ɗin tajishi cikin muryar isa da taƙama yace”keeh banitakardunki ingani inya dacema a ɗaukeki aikin”.
a zuciyarta tace”banda kar inkoma gida Abbah ya rifeni da faɗa wallahi da bazan kula wannan tsinanneba amma yanzu yana iya tunda a office ɗinsa nike dole inkai zuciyata nesa”.
sauke ajiyar zuciya tayi gefe guda kuma wata muguwar tsanar Namijin duniya taji jitake kamar ta shaƙeshi ta huta a hankali tashiga takawa harta isa gabanshi bata bari ta ɗago idanunta ba saboda gani take tunda take ba’ah taɓa muzantata irin yadda Namijin duniya ya muzantataba batare data bari sun haɗa ido ba ta kauda kanta gefe tare da miƙamasa envelop ɗin documents ɗinta a yatsune ya ansa tana kallonsa ta gefen idonta yashiga bubbuɗawa.

Seda yaɗau lokaci yana kallon result ɗinta a zuciyarsa yace”wow ammafa yarinyar nan tayi ƙoƙari pharmacy”.
a fili kuma taɓe baki yayi a yatsune ya kalleta tare da cewa”anyako wannan nakine ba takardun ƙawarki kika aro ba dannasan kede yarda baki da tarbiyya bazeyiwu ki wani karanci pharmacy ba koba komai na masu kwakwalwa ne bana irinki bane masu kwakwalwar kifiba”.
banza tayi dashi harya gama zancensa sannan ya miƙamata tare da cewa”kije waje seki duba inda sunanki yafito”.
a fusace ta ɗauki takardunta tare yun fari da fararen oily eye ɗinta ta murguɗamasa small pinky lips ɗinta tare da cewa”Allah ya isana mugu azzalumi kasamun wani ƙazamun bakinka dayasha yawon bariki a tsarkakken bakine aiba ƙarya nayimaka ba ko yanzu ka gwadamun rashin tarbiyyartaka”.
taƙarasa zancenta tare da kwasa da gudu ta fice wata uwar tsuka Namijin duniya yasaki tare da cewa”zakisan nine banda tarbiyya stupid kawai aidai zaki dawo ba tafiyarki kenanba”.
ya miƙe tare da kallon agogon hannunsa yaɗauki phone ɗinsa ya nufi gurin pridge ɗinsa yaɗauki ruwa yadawo yazauna ya ɓalli drugs ɗinsa yasha sannan ya miƙe ya nufi waje.

INTEESAR POV
Tana fita da gudu taga sakatariya ta tsareta da ƙananun idanunta tana kallonta tsaki tayi haɗe da cewa”cusu ba karjini a haka zaki ƙare a titi ke inbanda tinkiyace ma wani yaganki ai seya ɗauka dangin ogomoshoce se wani tsinanne ƙirji kike banƙaromasa saboda rashin aji ƙirjin nakima kamar farantin fawa wama zegani harya burgeshi dan haka ina gargaɗarki niba sa’arki bace kije can ku ƙarata kedashi amma inkikace zaki sakani zan baki mamaki banza mara aji”.
tana gama faɗar maganarta zata wuce kenan taji sakatariya ta tintsire da dariya tare da nunata sama da ƙasa tace”tayama za’ace classy irin Namijin duniya yasoki dubifa kayan jikinki duk a koɗe sekace mabaraciya”.
“ke yadama da harkike zargin wani abu amma ni na wuce ajin wannan ɗan iskan mutumin dama sede irinku ƴan bariki karuwai da basusan mutuncin kansu ba”.
tana gabama faɗamata haka ta wuce fuuu tabar sakatariya tsaye nan baki buɗe Namijin duniya dake kallon duk abunda yike faruwane yasaki wani murmushin dabe shirya yinsaba yace”gaskiya wannan yarinyar tana buƙatar general service wai ƙirji kamar farantin fawa amma bata da mutunci”.
ya miƙe ya fice abunsa.

A farfajiyar Comphany ɗin taga Hauwa’uh tsaye tana jiranta ƙarasawa tayi inda take tare da dafata tace”sorry sweetheart nabarki ke kaɗai tunɗazu”.
sauke wata ajiyar zuciya Hauwa’uh tayi tare da cewa”bakomai ina nan ina tinanin Allah yasa ba wani abun yayimikiba dan bakiji yadda ƙirjina yariƙa dukan tara-tara ba tunda kika shiga”.
tinanowa tayi da ya haɗa bakinsa da nata saurin tofar da miyawun bakinta tayi tare da saurin aro jarumta dankar Hauwa’uh tagane tace”kwantar da hankalinki ƙawata ba abinda yayimun kidena ɗaga hankalinki kinji”.
“masha Allah se yanzu naji hankalina ya kwanta muje to gurin da ake bawa koya takardar can muji position ɗinmu dakanan semu biya gidan ɗinkinmu dan karmu rasa ɗinki next week ne bikin Muneera Musa”.
“toh muje”.
nansuka nufi gurin da ake rabawa suna zuwa ana kiran sunan Hauwa’uh ansa tayi b tare data buɗaba tana jiran akira Inteesar a ƙarshe aka kira Inteesar suna ganin mutane nata farinciki zasu bar gurin sukaji wata mata tana cewa ƴar uwarta”daɗina da Comphany ɗinnan indai mutum yayi karatu to zesamu muƙami babba idan kuma iya matakin secondry gareka shine za’ah ɗauke a irinsu cleaners haka da massengers Comphany ɗinnan akwai adalci”.
matsawa can gefe da mutane sukayi kowanne cikinsu yashiga buɗe takardarshi gabanta ya buga damm sakamakon cin karo da sunanta a matsayin cleaner ɗin office ɗin Namijin duniya wasu zafafan hawayene suka shiga sinitiri a idanunta cikin murna Hauwa’uh ta ɗago da niyyar magana taga halin da ƙawarta take ciki tayi saurin fisge takardar hannun Inteesar ta duba sosai taji bataji daɗiba cikin tausayin ƙawartata tace”kinga irin abinda nike faɗamiki ko a lokacinnan kika zage kikayimasa rashin kunya san ranki dama na faɗamiki baze barkiba wallahi duk gurinnan ba wanda yazo da karatun dayakai naki amma seyasa aka sakaki a matsayin cleaner a office ɗinsa”.
“Sweetheart bana taɓajin ina danasani a abunda nayiwa wannan sakaran sema ƙaramun karsashi da yikeyi muje kinji”.
tafaɗa tare da share hawayen dake zubomata “toh muje”.
“congratulation Sweetheart kice kinzama sakatariyar Adam”.
“nagode”.
hararta Inteesar tayi nansuka jera suka tafi a bakin Comphany ɗin suka tsaya samun napep basu wani jima da tsayuwaba wata jibgegiyar mota tayi parking a gabansu wani matashin gentle guy ne yafito daga motar tare da zagayawa indasu Inteesar suke fuskarsa ɗauke da murmushi ba ƙaramun kyakyawa bane bakinsa ɗauke da sallama ya isa garesu haɗa baki sukayi gurin cewa”Wa’alaika salam”.
“ƴammata ina zuwa haka be kamata haɗaɗɗun ƴammata kamarku suna tsaye rana na dukansuba bayan daka ganinku ba kalar shiga ranar bane”.
murmushi sukayi gabaki ɗayansu Hauwa’uh tace”waya faɗamaka haka Malam”.
“hmmm aiba se wani ya faɗamunba bayan ga zuciyata a kusa dake dole insani”.
yaƙarasa zancensa yana kallon Inteesar dariya Hauwa’uh tayi tace”inko hakane kayi dace da zuciya mr kyau”.
“aidama nasan zuciyata me kyauce kuzo muje inkaiku namanta ban faɗama zuciyata sunanaba sunana Zaid”.
“a’ah mungode me napep muke jira”.
Inteesar da ke tinanin muzantata da Namijin duniya yike ce ta sauke wata ajiyar zuciya wadda tasa su Zaid saurin kallonta yace”dan Allah ku shiga nakaiku kinga dakanan nasan gidansu zuciyata”.
Inteesar na shirin cewa a’ah taga Namijin duniya da anbuɗemasa mota ze shiga yana kallonsu tace”toh mushiga Hauwa’uh”.
nanya buɗewa Hauwa’uh baya ita kuma ya buɗemata front seat tana ɗaga ido caraf idonsu ya sarƙe dana Namijin duniya ta taɓe baki tashige ya rife ya zaga ya shiga yajasu sauke ajiyar zuciya Namijin duniya yayi a zuciyarsa yace” to wannan kuma meye haɗinta dashi da har suka shiga motarsa kenan duk abinda nayimata bataji haushi ba kenan aiko dole da sake dukda bankai ƙarshen plan ɗinba”.
ɗaukar wayarsa yayi ya tura text bayan 30mins wayarsa tayi ringing ɗagawa yayi tare da yin shiru daga ɗaya ɓangaren Ahmad yace”nagani amma kasan wani abu yarinyar nan taji haushi sosai ganinka ne yasa ta nunamaka bataji haushiba plan ɗinmu yafara tafiya sucessful wallahi”.
“ok to semu cigaba”.
nansukayi sallama ya kashe tare da cewa driver”mu tafi”.
nansuka ɗauki hanya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Leave a Reply

Back to top button