NAMIJIN DUNIYA COMPLETE NOVELTHE WORLD MAN COMPLETE NOVEL

THE WORLD MAN (NAMIJIN DUNIYA) COMPLETE NOVEL

Bayan sun gama gaisawa ne su Jabeer suka fara shigo da haɗaɗun akwatuna seda suka shigo da akwati sha biyu nan aka shiga buɗa akwatunan dake shaƙe da kaya tsadaddun kayane ƴan ubansu a ciki kowanne da takalminsa da mayafinsa da jakarsa sosai murna gurinsu Khadijah da Hauwah ba’ah cewa komai tun suna ƙirga kaya har suka dena domin Zaid yayi ƙoƙari sosai nan Momynsu Hauwah tasa su Hauwah su fito da snacks ɗin da sukayi aka aje a gabansu da kuɗin tukuicin da Abban Hauwah ya bayar dubu goma aka basu har an aje akasa aka kaisu mota Hauwah tayiwa wannan budurwar rakiya zuwa gidansu suga Inteesar .

Kwance take tana karatu littafi taji shigowarsu Hauwah ba tare data tashi daka inda take ba ta amsa sallamar su Hauwah shiga sukayi suna shiga ƙanwar Zaid a zuciyarta tace”wow gaskiya dole bro ya gigice amma gaskiya ta haɗu ko ni mace nasan ta haɗu balleshi da yike namiji kalli gashinta dan Allah har gadon baya”.
tana cikin zancen zucin taji Hauwah tace”Besty ga ƙanwarki tace tana son taga wadda ta susutamata Yayanta”.
rife fuska Amna tayi tana dariya tace”Aunty ina yini”.
murmushi Inteesar tayi tace”lafiya ƙlau Amna ko”.
ɗagamata kai tayi bayan sun gaisa suka kawomata ruwa tasha suka ta miƙe nan suka mata rakiya a bakin get ɗin gidansu Hauwah Inteesar ta tsaya tare da ɗagamata hannu alamun bye-bye sannan ta juya.

Ɓangaren Uwar gwarama ko tunda taga irin dukiyar da Zaid ya kashe a lefen Inteesar hankalinta yaƙara tashi takasa zaune takasa tsaye ko gurin lefan bataje ba saboda tsananin baƙin cikin dake damunta ga Jameelah ta tasata a gaba se kuka takemata kan ita har yau bataga alamun Zaid baze auri Inteesar ba hankalinta inyayi dubu ya ɓaci ta rasa inda zata saka kanta taji daɗi.

Washe gari suna tashi suka tafi gurin aiki da wurwuri suna isa Comphanyn kowacce ta nufi gurin aikinta a hankali take tafiya kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki yayinda zuciyarta ke dukan uku-uku sakamakon tayi fashi bata sanarmasa ba a hankali ta tura ƙofar office ɗinsa yayinda zuciyarta tashiga bugawa da sauri -sauri kanta a ƙasa tashiga!!!!!!

Ga meson karanta book two ɗin MAN OF THE WORLD nafara post ɗinsa a paid group ɗina domin book two na kuɗine akan farashi mafi sauƙi naira #300 domin neman ƙarin bayani ki tuntuɓi wannan number koda kuɗinka seda rabonka 08108362334.

Votes and Comments
Plz share to others

_Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo._anen Gwa???? MAN OF THE WORLD
(NAMIJIN DUNIYA)

MALLAKIN
REAL EESHOW

HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCI…

BOOK 1

PAGES 3️⃣3️⃣➡️3️⃣4️⃣

     Samun office ɗinsa tayi bakowa a ciki se ƙarar a.c dake ta faman aiki da mayataccen ƙanshin turarensa daya kama office ɗin waige-waige tashiga yi gani tayi bataga alamar yazo ba sosai tayi mamakin rashin zuwansa  da wuri domin tasan yana rigata zuwa duba agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunta tayi taga har goma tayi zuciyarta ce tacemata"ke meye naki na damuwa dan wannan mara mutuncin bezo ba aikyama fi sakewa da binki da yikeyi da wa'innan mayun idanun nasa masu firgita mutum".

tana gama faɗin haka a zuciyarta ta taɓe ɗan ƙaramin pinky lips ɗinta ta wuce toilet tashiga aikinta tana gama wankin toilet tashiga goge chairs and tables ɗin dake cikin office tana gamawa ta share ko ina fes ta gyara ko ina yazama neat ta nufi gurin zaman sakatariya ta zauna ta shiga duduba takardun dake kan tables ɗin kamar an tsikareta ta miƙe tare da kallon tamfatsetsen agogon dake manne a office ɗin ta nufi cikin office ɗinsa tana shiga ta nufi drower dataga room freshners ta ɗauki ɗaya daga cikinsu tashiga fesawa ko ina na gurin ta wani toshe hanci tana cikin mitarta Hauwah ta shigo bakinta ɗauke da sallama amsamata tayi ta cigaba da fesa room freshner ɗinta ƙarasawa inda take Hauwah tayi tare da cewa”Besty wai yanaga kinata faman toshe hanci sekace wadda taji wari bakiji yadda kika cika room freshnern nanba har hawa ka yikeyi “.
“ai warinne domin turaren wannan mutumin har hawa kai yikeyi sabo da rashin daɗin ƙamshinsa har tasarmun da zuciya yikeyi wallahi inji kamar zanyi amai “.
“hhh Besty banda dai sharri dandai kuna faɗa dashine shiyasa kika tsaneshi amma ai Sir Abdallah komai nasa na daban ne ni tunda nike bantaɓa jin irin ƙamshin turarensa jikin wani kinsanfa shiɗin duniya ne “.
taɓe baki Inteesar tayi haɗe da cewa “Besty Allah bazancen sharri bakuma tsanarsa nayi ba kawai halinsa na tsana na girman kai da ɗagawa da nuna shi wanine uwa uba rashin tarbiyya da rashin ganin girman nagaba dashi ko kunya bayaji mutanen da suka girmesa suyita duƙawa suna gaishesa sekiga seya ɗauki lokaci saboda isa da izza sannan ze amsa wa’innan halayen nan nasa na mugun ɓatamun rai wallahi shi ko kunya bayaji isa kamar wani basarake”.
“hhh ni banga wata izzaba kedai kawai dan bakwa shiri dashine shiyasa kike ganin kamar bashi da kirki amma Sir Abdallah yanada kirki sosai ga sanin yakamata”.
zaro sexy eyes ɗinta tayi haɗe da cewa”wannan mutumin ne yasan yakamata tabɗi a rashin samun wa’inda suka san yakamata ƙila a ɗaukeshi domin wannan mara tarbiyyar mutumin ko hanyar inda yakamata tayi bebi ba”.
“to maida wuƙar bani nakar zomon ba rataya aka bani Besty ba wannan yakawoni ba gani nayi har 12pm tayi so nike yau mutafi da wuri saboda mufara tsare-tsarenmu ina tinanij daka yau ba lallai bane muƙara zuwa office ba inaso a gyarawa Uncle Zaid ke sosai dan karya rainamun ke “.
“dama nima yanzu nagama tinanin hakan yau tunda na tashi gabana keta faɗuwa na rasa dalili kome yake faruwa oho jinike kamar wani abu ze faru dani”.
” insha Allahu Besty ba abinda ze faru dake se Alkhairi kinji Bestyna kedai kawai idan kinji haka ki riƙa Innalillahi wa’innah ilaihi raji’un ki yawaita addu’ah wajan biyu zamu tafi kisan dabarar da zakiyiwa Sir Abdallah”.
sauke numfashi Inteesar tayi cikin sanyin murya tace”nagode Bestyna Allah yabarmu tare keɗin mahaɗin rayuwata ce Besty kinmun komai na rayuwa kullum baki da burin daya wuce kisani farinciki Besty nagode da kulawarki gareni Allah nima kabani ikon temakon wannan baiwa taka “.
taƙarasa zancenta hawaye na niyyar zubowa daga lulu eyes ɗinta girzgizamata kai Hauwah tayi alamun kar tayi kuka tace”Besty banason godiyar nan da kikemun domin nasan inke kike da damar da nike da ita da ba abinda bazakimunba toni meyasa bazan mikiba bayan inada halin yi domin keɗin kin wuce ƙawa a gareni ƴar uwata ce dan Allah duk abinda zanmiki kidenamun godiya”.
saurin rungumeta Inteesar tayi haɗe da fashewa da kuka seda sukayi kuka me isarsu sannan suka saki junansu Hauwah tace”Besty bara na koma gurin aiki”.
kai kawai Inteesar ta iya ɗagamata saboda kukan datasha nan Hauwah ta tafi tabarta jiki bakwari ta koma mazauninta na sakatariya a zuciyarta tana mamakin rashin zuwan Namijin duniya.

“gaskiya Ummah kayannan kwata-kwa basu dace da wannan tsinanniyar yarinyar ba da Jameelah suka dace”.
“haba Saratu ya kike irin wannan ne ke ai da Jameeha da Aishatu duk ɗaya ne meye abun baƙinciki kowa rabonsa ze samu kidena irin wannan ke babbace memakon kizama me kwantar da fitina seki zama me tayar da ita”.
a harzuƙe Uwar Gwarama tayi kan Badi’ah tana huci tace”nace duk biyune karki ƙara haɗamun hafizar ƴata da wannan ƴar barikin yarinyar data gama zubar da mutuncinta a titi ai gaskiya Saratu ta faɗa ai kozan rasa zanin ɗaurawa bazan taɓa bari ɗiyar Amina tayi aure inda zata hutaba kozan rasa koda zanyi yawo tsirara senaga bayanta daka ita har shegun ƴaƴannan nata masu yawon bariki anyako nina haifi wannan salamammar kuwa ni Hajara da a asibiti na haifeki da se ince canzamun ke akayi salamammar banza wadda batasan ciwon kanta ba kika ƙara sakamana abiki wallahi akan maganarmu wallahi sena saɓamiki shegiya ƴar uwartaki kikewa baƙinciki sarkin baƙin ciki kawai me baƙin halin tsiya kawai “.
jin furucin mahaifiyarta ne yasata kama bakinta tayi shiru taji Uwar Gwarama tace”kwantar da hankalinki ƴar albarka meson ganin farincikina wannan lefe da kike gani ba makawa na Jameelah ne kedai kawai ki zuba ido kisha kallo duk wannan ɗan banzancin da sukeyi zasu koma suyi laƙwas dani suke zance ni kaina nasan bani da kyau”.
cikin zumuɗi Saratu tace”Allah Ummah kice mufara shirin shiga aljannar duniya kenan”.
“sosaima kuwa tawan ki kira su Hafsah ki sanarmusu suma su shirya”.
“nagode Mamana takaina Allah yabarmana ke”.
“Ameen dai tawan”.
Uwar Gwarama tafaɗa ta wurgawa Badi’ah harara shiru tayi suna nan zaune sukaji sallamar Inteesar saurin miƙewa Badi’ah tayi ta fita tsaki Uwar Gwarama tayi haɗe da cewa “sakarai kawai wadda batason ciwon kanta ba kinga ai taji sallamar uwarta har jikinta ke ɓari dan taje gurinta karta tsinemata narasa me Aminah tayiwa Badi’ah ta liƙemusu haka ba”.
“ai Ummah aikin asirine wannan kiga dan Allah yadda har jikinta ke rawa kamar mazari dakajin muryar waccan karuwar”.
“aiko nafi ƙarfinta wallahi “.
nan Saratu taita zuga Uwar Gwarama.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Leave a Reply

Back to top button