NAMIJIN DUNIYA COMPLETE NOVELTHE WORLD MAN COMPLETE NOVEL

THE WORLD MAN (NAMIJIN DUNIYA) COMPLETE NOVEL

Knocking suka yi tsananta faɗuwa gabanta ya yi sabo da tuno ze iya wulaƙantata a gaban Hauwa’uh zuciyarta ba abin da take se dukan tara-tara tashiga duniyar tinani daga ciki suka ji muryar Adam ya ce”come in”.
dafata da Hauwa’uh tayi ta ce”bestyna be a women mana be strong naga duk kin tsorata”.
“hmm ba komai kuma Wallahi.
Ok toh muje”.
I nan suka shige kanta a ƙasa ba tare data ɗago ba har suka ƙarasa in da suke zau ne shi da su Ahmad ganin Hauwa’uh yasa Ahmad faɗaɗa murmushinsa ya ce”Hauwa’uh ƙawartaki kika kawowa ziyara?”.
A’ah sir gurinka nazo”.
“Toh ina jinki ku ƙaraso man kamar wa’in da zamu kama”.
Dariya Hauwa’uh tayi ban da Inteesar da tayi kicin-kicin da ranta kanta a ƙasa har suka ƙarasa in da suke zau ne suka duƙa cikin girmawa Hauwa’uh ta ce”sir dama tambayarka zanyi in babu abin da za’a yi maka dan Allah zamu tafi gidan ƙunshi bikin ƙawarmu za’ah fara yau takiramu sun wuce gurin ƙunshi “.
murmushi Ahmad ya yi tare da ce wa”ba abin da zaki yi mun nima dama yan zu zamu tashi yau zamu fara program ɗin bikin Adam kice ku bazaku leƙo mana bikin namu ba kenan kije sekun dawo Allah ya sanya Alkhairi “.
Ameen ya Allah sir nagode Sir Adam Allah ya sanya Alkhairi”.
Ameen ya Allah Hauwa’uh nagode”.
A jikinta taji kamar wani yana kallonta ɗago idanunta tayi da niyyar satar kallonsa jin kamar baya gurin caraf suka yi four eyes da Namijin duniya da ke satar kallonta saurin mai da kanta ƙasa tayi sabo da wani kwarjini da taga ya yi mata taɓata Hauwa’uh tayi alamar su tafi miƙewa suka yi Hauwa’uh ta ce”mun gode se anjumanku”.
Yauwa”.
Suna cikin tafiya wayar Inteesar tafara ringing ɗagawa tayi tare da sakin ƙayataccen murmushin daya ƙara fito da tsananin kyawun da Allah ya bata cikin sanyin muryarta me kashe jikin duk wani ɗa namiji me lafiya ta ce”Salamu Alaikum”.
“Wa’alaki salam zuciyata na iso”.
Toh gamu nan muma”.
taƙarasa zancenta tare da kashe wayar damm ƙirjinsa ya bayar jin abin da ta ce a zuciyarsa ya ce”da wa take waya da har take zumuɗi haka?”.
Wata zuciyar ce ta ce”to kai meye naka nasanin dawa take waya ?”.
Haka nan yaji wani mugun ɓacin rai ya baibaye shi ɓangarensu Inteesar ko tana katse waya suka cigaba da tafiya bazato suka ji lion voice ɗinsa ta daki kunenta ya ce”kee! wa kika tambaya da zaki bita ko ce miki aka yi kin gama aikinki na yau ne?”.
Tsayawa suka yi cak jin abin da ya ce” ɗago oily eyes ɗinta tayi da suka fara tara ruwa ta kalli Hauwa’uh murya na rawa sabo da kukan dake tahomata ta ce” sorry sir kije Zaid na waje a fara yi miki in yaso in na tashi daga aiki sena biyoku”.
“a’ah kibari na jiraki mutafi tare”.
A’ah kitafi a fara yi miki a rage idan nazo ni kawai za’ah yiwa”.
“toh muje na rakaki”.
Toh.
Har sun fara tafiya cikin ɓacin rai ya ce”wa kika tambaya permission ɗin fita?”.
Tsayawa tayi cikin sanyin da jikinta yayi lokaci ɗaya ta ce “sorry sir kije besty sena taho idan kuma yamma ta cika yi ba lallai nazoba semu nazo ba sena kira ki sanar dani gidan kwalliya nazo na sameku”.
sosai taji tausayin ƙawarta na ratsa zuciyarta ta ce”toh”.
Ta tafi tabar Inteesar komawa tayi ta tsaya ɗan nesa da in da suke zau ne tana share hawayen dake ƙoƙarin zubo mata a zuciyarta tana dana sanin biye masa da tayi a rayuwarta har suka gama hirarsu tsawon lokaci tana tsaye suka miƙe zasu tafi Adam ya ce”se mun haɗu anjima mu yan zu zamu wuce”.
Basu hannu Namijin duniya ya yi tare da ce wa”toh sai mun haɗu a gurin dinner dan akwai wani abu da zan ƙarasa idan kun shirya mayi waya”.
Toh shi kenan”.
Nan suka tafi suka barshi daga shi se Inteesar shiru office ɗin ya ɗauka na tsawon wani lokaci ba abin da kake ji se ƙarar a.c da keta faman aiki kallon yadda ta takure alamun a.c tayi mata yawa yayi tare da taɓe baki ya miƙe ya koma kan kujerarsa ya kunna system ɗinsa ya shiga kallon wani series na ƴan korea me suna Play full kiss yama manta da wata Inteesar daketa faman tsaiwa kamar wadda ta haɗiyi taɓarya yanata faman doka smile da alama film ɗin yana kai masa a hankali ta ɗago lulu eyes ɗinta daketa zubar da ruwa ta kallesa gani tayi kallonsa ma yike yi hankalinsa kwance yama manta da ita ga ƙafafunta daketa faman zafi sabo da tsayuwa da taketa yi wani mugun tausayin kanta ne ya kamata a haka ta cigaba da tsayuwa ba tare data nuna tagajiba ko wani sauyi a fuskarta lokaci zuwa lokaci tana share ƴan kwallolinta .

Wuraren ƙarfe biyar ya shigo office ɗin fuskar nan ba annuri a ciki-ciki ya ce”salamu Alaikum”.
“Wa’alaika salam sannu da dawowa”.
Taɓe baki ya yi ba tare daya amsa mata ba ya wuce ya zau na akan kujera ya ce”kya iya tafiya”.
Cikin sanyin murya ba tare data nuna ta damuba ta ce”thank you sir”.
Tafaɗa muryarta na rawa da kyar take iya ɗaga ƙafarta sabo da tsamin da tayi mata ga wani jiri da yike ɗibarta luuu ta tafi zata faɗi tayi saurin dafa bango Namijin duniya dayasa hannu ze da niyyar tareta saurin matsawa gefe tayi tare da cije ɗan pinky lips ɗinta murya na rawa sabo da kukan daya fara taho mata ta ce”nagode sir”.
Tana gama faɗan haka tashiga tafiya cike da jarumta duk da irin yadda take jin ƙafafun na mata azaba haka ta daure ta tafi abunta tana kuka.

Ji ya yi duk beji daɗin yadda ta fita ba tana kuka domin jin kukanta yike har cikin zuciyarsa be san meya saba ji ya yi beyi mata adalci ba kome ya tino kuma ya ɗaga kafaɗa alamar matsalarta ce ya cigaba da aiki a system ɗinsa ɓangaren Inteesar ko tana fita taga wani gangarumin hadarine a garin ga wata irin iska da akeyi ba alamun abun hawa ko kaɗan ta daɗe tana jiran abun hawa kafin dabarar kiran Zaid ta faɗo mata saurin zaro wayar da Zaid ya bata tayi daga cikin jakarta tashiga dialing no Zaid a kashe taji wayar a kashe hakan yasa hankalinta mugun tashi tashiga rage tafiya ko Allah ze sa tasamu abun hawa har tayi tafiya me nisa amma bataga masu napep ba samun guri tayi ta raɓe ta tsugunna kamar wata marainiya ta fashe da wani marayan kuka.

Bazato taji ana mata horn ɗago sexy eyes ɗinta tayi da suka rine sabo da kukan da take yi ta saukesu akan wata haɗaɗɗiyar farar G-box tasha tintac se ɗaukar ido motar take yi mai da kanta tayi ta cigaba da kukanta dan tasan da Zaid ne ze kirata ta cigaba tana cikin kuka taji muryar wani mutum akanta ya ce”ki taso mutafi inji sir”.
Ɗago jajayen idanunta tayi ta saukesu akan mutumin wan da daka ganin shi kaga security ta ce”waye ogan naka?”.
Zai yi magana kenan ya ji wayarsa na ƙara ɗagawa ya yi tare da ce wa”okay sir”.
Ya kashe wayar tare da kallonta ya ce”ya ce in ba zaki taho mutafiba inkyaleki”.
Waigawa tayi taga unguwar kwal ga duhu ya ɗan fara yi bako mutum ɗaya hakan ya sata miƙewa jiki ba kwari tabi bayan mutumin ƙofar baya ya buɗe mata tashiga ya mai da murfin ya rufe sannan ya zaga ya shiga mazaunin driver ya jasu.

Tana shiga daddaɗan ƙamshin turarensa ya daki hancinta satar kallonsa tayi ta wutsiyar idonta gani tayi yana karatun daily trust ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya saurin juyar da kanta wajan window tayi tare da ɗan tsuke ƙaramin bakinta a zuciyarta ta ce”shi dai ko a ina zamansa kenan sabo da isa”.
Tana cikin wannan zancen a zuciyarta taji lion voice ɗinsa ta daki dodon kunnenta ya ce”me yasa baki kira wannan faƙirin saurayin naki ya ɗauke ki ba? Ko yau be aro motar bane?”.
Sosai maganganunsa suka ɓata mata rai amma seta make tayi kamar ma bata san da ita yi keba jin tayi banza da shi yasa ran shi ɓaci ya yi kwafa ringing wayarta tashiga yi ɗauka tayi tare da ce wa”tun ɗazu nayi ta kiranki baki ɗauka ba”.
Sorry besty ina wanka ne kin taho muna gurin me make-up ki wuto kawai na faɗawa Umma na tafi miki da kayan da zamusa”.
Anya zanyi make-up ɗin nan ma ni kuwa kin san bana son a cika mun fuska kin tafi da Khadijah ko”.
Ai ko dole kiyi kin san Asma’uh bazata ji daɗi ba ki daure kawai kiyi eh na taho da ita amma fara yi mata make-up ɗin Uncle Zaid ya yi mana siyayya sosai ki kira shi kiyi mishi godiya kowacce cikinmu yasiya mata gown da takalmi da pos se kuma dalleliyar waya ƙirar iphone 13pro daya bani in ajiye miki”.
Cikin farin ciki ta ce”dan Allah”.
Wallahi kinga ko dole kiyi kwalliyar nan ko dan kiyi masa hotuna”.
Sosai ma kuwa aiko bara in kira shi in yi masa godiya kuwa”.
Ya dai kamata sekin ƙaraso muna gurin Reality “.
“toh sena ƙaraso”.
“yauwa”.
Nanta kashe cike da zumuɗi tafara lalubar no Zaid taji muryarsa ya ce”ki faɗa masa unguwar da za’ah kaiki”.
Se lokacin ta tina a in da take hakan yasa fara’ar dake kan fuskarta saurin gushewa ta katse kiran da take yiwa Zaid ta ce”kusa da Garki akwai wata me make-up a tsallaken titi nan zan sauka”.
Toh ranki shidaɗe”.
ce war security nan ya juya akalar mota suka nufi Garki shiru ne ya biyo baya har suka isa suka yi parking a ƙawataccen gurin tanƙamemen shagon make-up ɗin Real Eeshow juyawa tayi ta kalli Namijin duniya cikin girmamawa ta ce”thank you sir”.
Ba tare daya ɗago daga karatun daily trust ɗinsa ba ya yi banza da ita buɗe mata mota security ɗin ya yi ta fita tare da shigewa gurin driver yaja motar suka bar gurin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Leave a Reply

Back to top button