NAMIJIN DUNIYA COMPLETE NOVELTHE WORLD MAN COMPLETE NOVEL

THE WORLD MAN (NAMIJIN DUNIYA) COMPLETE NOVEL

Ɓangarensu Inteesar ko sun ɗanyi tafiya sannan Zaid yace”wacce unguwar zankaiku gimbiyata”.
“Suleja”.
“ok amma baki faɗamun sunanki ba”.
“sunana Inteesar”.
“nice name “.
shiru tayi sukaita hirarsu shida Hauwa’uh tayimasa kwatancen gurin me ɗinki seda suka biya yabiya musu kuɗin ɗinkinsu dukda basusoba suka yimasa godiya sannan suka ɗauki hanyar gidansu daidai kwar gidansu ya tsaya yana gama parking suka buɗe suka fito hakan yasashi shima fitowa yana wasa da ɗan key ɗin dake hannunsa yace”Hauwa’uh se gobe kuma”.
“eh Uncle Zaid”.
“a’aaah godiya nike ƙawarmu “.
nantayimusu sallama ta wucetashiga gida kallon Inteesar yayi dake niyyar tafiya yace”ranki shidaɗe kitsaya inada magana”.
“toh inajinka”.
“da farko sunana Zaid a unguwar Garki nike sunan mahaifina Cheif Judge Muhammad Abdurrahman nagankine na yaba da nutsuwarki tunda naganki nafara murna nasamu muradin zuciyata ina fatan zaki karɓi soyayyata”.
dammm gaban Inteesar yabayar lokaci ɗaya wasu hawaye da take ƙoƙarin ɓoyewa suka shiga silalomata domin tinda take ba’ah taɓa furtamata kalmar so ba se a ranar ganin haka Zaid bakaramun gigicewa yayiba yaɗauka bata sonsa cikin karayar zuciya yace”Inteesar karki cemun bakya sona ko ammiki miji”.
wani murmushin farinciki dabata shirya yinsaba ya suɓucemata tayi saurin juyamasa baya tace”ba’ah mun miji ba ka kwantar da hankalinka nima ina sonka”.
cikin jin kunya zata ruga kenan ya riƙe gefan hijab ɗinta tsayawa tayi murmushi Zaid yayi yace”godiya nike gimbiyata gobe wuraren ƙarfe nawa zaki fita gurin aikin”.
shiru tayi seda taɗau lokaci da alama tinani take sannan tace”around 9:30 haka”.
“okay gimbiyata kijirani nazo nakaiku sena wuce office”.
“tom mungode”.
“no wayarkifa”.
“bani da waya”.
“okay to bara na baki ƙaramar wayata kafin nasan yadda zanyi”.
“toh”.
nanya shiga mota ya ɗakko haɗe da bandir ɗin 1k ya miƙamata ƙin amsar kuɗin tayi seda ya zari guda biyar yabata sannan ta amsa sukayi sallama tashiga gida.

Ruƙayya da Uwar Gwarama dake raɓe tace”Innah kinga arziƙi ko gaskiya kisan yadda zakiyi inasonsa dan Allah kisan yadda zakiyi”.
“kwantar da hankalinki Ruƙayya indai wannan mejan kunnen ne sekin aureshi hauka nike inbari ɗiyar Amina tayi aure gidan hutu aiko zan rasa zanin ɗaurawa bazata auri wannan mutumin arziƙinba zakisha mamaki kidena wani ɗaga hankalinki aure dake dashi kamar da ƙasa muje ciki”.
“yauwa Innah ta haka nike sonki Allah yabarmanake”.
“Ameen”.
nansuka shige tin daka zaure Uwar Gwarama take cewa”Malam! Malam!! Malam!!!”.
fitowa Abbah yayi daka ban ɗaki a zabure hanunsa riƙe da buta yace”lafiya”.
“inafa lafiya yanzu naga wannan me baƙin jinin da wani a mota yana lallatseta basusan ina kallonsu ba naga yabata dunƙulin kuɗi ta amsa ba sharri nikemata ba zakaga hannunta da kuɗi”.
kallonta Abbah yayi zatayi magana yace”rifemun baki sakaran yarinya baki isa kin ɓatamun suna a gari ba ana ganin ƙimata ko waye yike tattaɓakin gobe kice indai dagaske yike sonki ya turo”.
fuskarta na zubar da hawaye ta ɗagamasa kai zata wuce kenan Abbah yace”munafuka kinbani kuɗin ko sena tattakaki”.
miƙamasa tayi ya amsa ta wuce ɗakinsu .

AFTER ONE DAY

9:20min
Zaune take kusa da Khadija wayar da Zaid yabata tayi ƙara gabda zata tsinke ta ɗaga tare da cewa”Salamu Alaikum”.
“wa’alaiki salam gimbiyata ina waje ina jiranku”.
“toh gamunan”.
nanya kashe miƙewa tayi tare da kallon Hauwa’uh daketa magana da Khadija tace”sarkin surutu yazo”.
“toh muje”.
nansuka yima Ummah sallama suka fita tadda shi sukayi tsaye gaisar dashi sukayi sannan suka hau motar suka nufi Comphany Namijin duniya dalilin traffic da suka samu basu suka isa ba se wuraren 10 yana saukesu sukayi sallama suka nufi cikin ma’aikatar a compound ɗin gurin suka rabu kowa ya nufi gurin aikinsa.

Tana isa ƙofar da sakatariya take zaune taji mararta tashiga tsunkunamata cikin dakiya da dauriya ta buɗe ƙofar haɗa ido sukayi da sakatariya daketa shan ƙamshi tana ganin Inteesar ta haɗe rai tsaki Inteesar tayi tare da wucewa fuuu danna ƙofar tayi ta buɗe shiga tayi kanta a ƙasa tace”Salamu Alaikum”.
ba tare daya amsa sallamartaba ya ɗago sexy eyes ɗinsa da sukayi kamar na mejin bacci ya zubamata cikin gadara da isa yace”yakamata kisan gurin aiki ba gurin nanaye bane da zaki riƙa hawa motar wani ƙato yana kawokiba sannan dama irin wannan lokaci yakamata cleaner yazo yayi aikinsa?”.
sosai ciwon mararta ke ƙara ƙaruwa cikin sanyin jikin da ita kanta batasan tana dashi ba tace”kayi haƙuri traffic muka samu ne”.
a gadarance yace”traffic ba uzuri bane da kin fito da wuri traffic ɗin ze tsaidake ne dan haka wannan ba uzuri bane dama ke ba albashi ɗaya zan riƙa biyanki da cleaners ba su dubu hamsin ne ke kuma dubu ashirin na zari kuɗin makarar da kikayi zan baki dubu sha shida gobema kinga bazaki ƙara bari ki makara”.
yana ƙarasa faɗar haka ya miƙe ya fita tashi tayi dakyar saboda ciwon yafara cin ƙarfinta tashiga share gurin dukda taga alamar anyi shara ta goge tana cikin goge wata haɗaɗɗiyar farar kujera fara tass da ita ta miƙe kenan taji tana jin jiri saurin zama tayi kan kujerar tana maida numfashi bazato taji anbuɗe ƙofa saurin miƙewa tayi ganin Namijin duniya waigawar nan da zatayi taga duk tayi staining ɗin inda ta zauna da jini!!!!!!!

Daka wannan update ɗin zaku jini shiru saboda zamu fara exam bani zan koma rubutuba se 18/1/2022 dan Allah ku tayani share dan masu karatu su sani ngd.

Votes and Comments
Plz share to others fisabilillah

_*Daga Alƙalamun ƴ???? *MAN OF THE WORLD*
(NAMIJIN DUNIYA)

MALLAKIN
REAL EESHOW

HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCI…

BOOK 1

PAGES 0️⃣9️⃣➡️1️⃣0️⃣

    Cikin matsanancin tashin hankali tayi saurin komawa ta zauna lokaci ɗaya zufa yashiga ketomata a zuciyarta tace"nashiga ukuna ni Aishatu na ɓatawa wannan jarababben mutumin kujera yazanyi wayyo Allah na Allah ka temakeni karya gani Allah kaɗaine yasan irin hukuncin dazemun wayyo Allah na haka nanma ya alah cika da wannan masifaffen mutumin bare na ɓatamasa farar kujerarsa Allah kaɗai yasan irin muzantani dazeyi Allah ka temakeni nashiga uku".

tana cikin zancen zucinnan ɗaga idonnan da zatayi caraf suka haɗa ido da Namijin duniya yana jifanta da wani
irin wulaƙantaccen kallo me cike da zallar ƙyama da ƙasƙanci Step biyu zuwa uku ya taka zuwa inda take kafin ya tsaya tare da harɗe hannuwansa aƙirji yayinda sexy eyes ɗinsa suka kaɗa sukayi jawur dasu saboda tsananin ɓacin rai se huci yike kamar wani mayunwacin zaki ya tsaya a gabanta .

Cikin lion voice ɗinsa wadda taƙara tsorata Inteesar yace”How dare You ?Waya baki izinin zama akujerata ke wacece da har kika samu damar zama akan kujerar da nike zama da wannan ƙazamun jikin naki wanda ba lallai banema yataɓa ganin ruwabama ko kina tunanin wannan wajen zama ƙasƙantattun mutanene irinkine duk ki wuce sauran chairs ɗin office ɗinnan ki rasa wadda zaki zauna se privet chair ɗina “.
yaƙarasa maganarsa cikin ɗan ɗaga murya Kasa furta komai tayi se ƙasa da tayi da kanta wani irin matsananciyar kunyarsa na shiganta dukda begani ba amma jitake kamar ƙasa ta tsage ta shige dan kunya shin taya zata iya tashi wannan mutumin ya ganta ahaka” Ya rabbi kada ka bari wannan bawa naka ya muzantani “.
tafaɗa a ƙasan ranta shiko Namijin duniya ganin tayi banza dashi yasashi ƙara hassala gani yike wani salon iskancin taƙara tsiromasa dashi hakan yasa yasaki wani guntun tsuka cikin ɓacin rai ya bugamata wata razananniyar tsawa wadda har seda ƴan cikinta suka kaɗa lokaci ɗaya jikinta yahau rawa batasan lokacin data miƙeba .

A hankali sexy eyes ɗinsa suka sauka akan kujeran data ɓatamasa Wara shu’uman idanunsa yayi yana kallon wajen wani irin baƙin cikinta ne yazo ya tokaremata maƙoshi dakyar ya iya haɗiye wani ƙullutun baƙin ciki daya tsayamasa lokaci ɗaya yaji yaƙarajin wata muguwar tsanarta na ƙara ƙaruwa a cikin zuciyarsa lokaci ɗaya kanshi yafara juyawa ga wata irin tsananin kyamarta dake damunsa ya buɗe baki da niyyar yimata magana kenan idanunsa ya sauka akanta .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Leave a Reply

Back to top button