Labarai

Tirkashi Ƙani Ya dirkawa Matar Yayansa Amarya sabuwa Fil Ciki a Nasarawa.

Tirkashi Ƙani Ya dirkawa Matar Yayansa Amarya sabuwa Fil Ciki a Nasarawa.

Jaridar Tsalle daya ita ta wallafa wannan labari a shafinta na Facebook inda ta bayyana cewa Wani mai suna David, ya dirƙawa matar yayansa ciki a ƙaramar hukumar Doma Jihar Nasarawa. bayan yayan nasa ya tafi samun horo na wata tara domin zama Ɗan sanda.”

“Rahoton ya cigaba cewa, yayan nasa mai suna Japhet ya yi sabuwar amarya inda suka yi alƙawarin ba za su kusanci juna ba har sai ya dawo samun horo na zama cikakken Ɗan sanda.”

Bayan tafiyar Japhet ɗin zuwa samun horo na zama Ɗan sanda sai ƙaninsa David ya Yi amfani da wannan damar na wurin maye gurbin yayansa suna goge raini tsakaninsa da matar yayansa ɗin.

Bugu da ƙari bayan dawowar Japhet jihar Nasarawa zuwa gida a domin duba iyali kawai sai yayi kaciɓis da wannan mummunar lamari, matarsa ɗauke da ciki rugum har na wata tara, biyo bayan bincike aka tabbatar da ƙanin sa David ya dirƙawa matarsa ciki.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button