NOVELSWASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GOIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

Kwana biyu dayin hakan saleemah ta warware saidai duk da haka bata wani sake wa mu zauna amma bata min kallon tsangwama kaman lokacin baya,saima kallon jin kunya da takeyi a ganinta na ceci yaranta harda ita ga barayin,gashi na hanata tayimin Godiya,sai hakan yakara sakata jin nauyina.
Komai yakoma normal nima na koma bakin aikina,yayinda sirrina kuma muka binne nida sameer,abinda yakfaru nayi zato zai nisanta kaina dashi saidai hakan bai faruba sai ma kara shigowa rayuwata da yakeyi lokacin cikin lokaci.
Nima tun ina kin amincewa da yanayin dayake jiyartata har ya zamo nakarbeshi hannu bibbiyu sannan na amince da tunkarar duj abinda zai biyi baya.
Yamzu kusan kullum da kyar nake bacci kowane dare saboda matsanancin ciwon kirji danake yi harda jini nake amarwa,nasan bai wuce saboda ketare dokar danake ba,nikuwa bazan iya hakan ba zan cigaba da karbar kulawar yah sameer a daga gareshi kafin lokacina yakare,bazan kara yarda na koma rayuwar kadaici danake a baya ba wannan lokacin.
Duk nasan idan yagane halin danake ciki zai shiga damuwa,shiyasa nake toshe duk wata hanya dana san zai gano wane hali na ke ciki.
Madubi na kalla inda naga bakin abu kaman jijiya yana bin wuyana,zaro ido nayi dan ban taba kulada shi ba sai yanzu,hoda na dauko mai kalar jikina na shafa a wajen,domin boyewa kar wani yagani,kawar da damuwar data shiga cikin zuciyata nayi kafin na fito zuwa office.
Har nayi hanyar zuwa asibiti wajen doctor maryam ta dubani sai kuma wani tunani yazomin,ida naje mai zance mata,sannan idan ta duba bata komai ba nan ma mai zance?,da haka na juya cikin sanyin jiki na wuce wajen aikina.
Dakyar na bari lokacin tashi yayi na koma gida,saboda haka kawai banason naga mutane suna matsowa inda nake,gani nake kaman sudin ba jinsi na bane,kuma wannan yanayin ya farune saboda shigowar sabon wani shedani zuwa jikina a daren jiya da daddare.
Ina shigowa gidan na samu saleemah a zaune,sannu da dawowa tacemin cikin magana kasa kasa,duk da najita amma ban kula ta ba,ina shiga daki nayi wurgi da jakar hannuna ina huci ni kadai,nasan wannna abu danake ji kuma nake aikatawa bani bace,amma babu yanda zanyi inaji ana iko da jikina.
Washagari ban je aikiba saboda munyi da yah sameer zai kaimu wajen doctor maryam mu yini,haka kawai na tsinci kaina da jin dadin maganarsa,dan ba kadan ba matar take birgeni sosai.
Tun safe mukayi shiri nida saleemah,dan ina kulada itah bata so aka ce da ni za’ajeba,duk da wani abu baya hadamu na kiyyaya haka ma babu Abu na so dayake hadani da ita.
Lace na saka milk mai adon chocolate,sai kuma nasaka gyale kalar adon lace din,dan a rayuwata banason saka hijabi duk da a ina da bukatar yin hakan,da gangan wasu kuraje suke fitomin wanda nasan ba na allah bane.
Sai da mukayi dan tafiya kafin muka isa,kasancewar gidanta yana da dan nisa da inda muke ,duk da tana da gida da aka bata a barrack din amma tafison zama a nata gidan.
Shiru gidan babu motsi kaman babu mutum a gidan ,shiga mukayi da sallama cikin gidan,wata yarinyace bazata wuce shekara sha biyar ba a falon tana rubutu,da alama assignment takeyi.
Dagowa tayi ta kallemu tanayi wa farouq murmushi,shima sunkuyar da kai yake da alama yasanta .
Gaishemu tayi a hankali said kuma tashiga cikin daki domin kiran doctor maryam din,itama saleemah bin yarinyar tayi zuwa cikin gidan.
Nikuwa ganin nikadai ce a tsaye yasa na koma kan kujera na zauna,shima yah sameer din zama yayi kaman da alama zuwansa na farko gidan kenan .
Idon nane yakai kan wani hato dayake rataye a falon,kallon yah sameer nayi da sauri wanda shima idon sa yake kan hoton,da alama yaga abinda nagani.
Tashi nayi zuwa gaban hoton kafin na maida kallona zuwa kan sameer wanda shima ya zare ido cikin mamaki.
Muna cikin hakane doctor maryam tashigo falon hannunta rike da na farouq,kallon mu take da mamaki ganin munyi cirko cirko bama cewa komai .
Nice hannuna yana rawa na nuna hoton ina kallonta amma kuma na gagara furta ko kalma daya daga bakina.
Murmushi tayi irinna manya kafin tace,
“Lah wannnan hoton mai kuma yah faru naga kina mamaki wasu masu aikina ne wanda nake jinsu kaman yan uwana wani abune yah faru”
“Ahah kawai dai nasan na jikin hotonne amma bansan ya akayi hotonsu yazo nan wajen ba”

Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150

Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.

????Sadi-Sakhna________✍????????

(¯’•.¸,¤°’✿.。.:քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ.:。.✿’°¤,¸.•‘¯)

????•°• WASA FARIN GIRKI •°•???? {cigaban gidan gandu}

????37~38????

“Hmm dolene hotunansu yazo nan wajen,kuma duk inda nake ma hotunansu zai zo wajen.
Sudin mutanene da bazan manta dasu ba a tsawon rayuwata,saidai bansan a ina zan sake ganin su ba,hakan yasa na dauki hotonsu da muhimmanci har nake tunawa dasu a rayuwata,amma naji kince wai kinsansu a ina kenan?”
Sunkuyar da kaina nayi a raina ina cewa,kar ko abinda nake Tunani yakasance gaskiya,kallon yah sameer nayi wanda shima idonsa ya nuna alamar hakan.
“Su din iyayenmune nida yah sameer,ummah hajara ta rasu inada shekara goma a duniya,baba umaru kuma yana gida”
Tashi tayi tsaye tana kallona,kafin kuma tace,
“Inalillahi was inna ilaihi raji’un, Hajara ta rasu?kincemin ke yar tace shin ta kara haihuwa ne bayan mun rabu,kuma baga sameer ina mijinkine”
Yah sameer ne yakatse maganar mu nida doctor maryam ta hanyar cewa,
“Shin kece hajiya maryam da baba umaru ya bamu labarin yayi aiki a gidanki a garin bauchi shekarun baya da suka wuce?”
Daga kai tayi da sauri kafin tace,
“Eh tabbas nice wanda muka zauna da su a gidana dake garin bauchi”
Dan tsabar kaduwa bansan lokacin da na zauna a wajenba,kenan doctor maryam mahaifiyatace ,kuma nida saleemah yan uwa ne kenan,mahaifiyarta yayar mahaifiya tace,wannan wane irin al’amarine haka.
Dago da kaina nayi ina kallon doctor maryam wanda itama take bina da kallo,sameer ne yasamu damar cewa wani abu bayan dukkanmu munyi shiru.
“Indai da gaske kece wacce baba umaru ya bamu labari to ya tabbata kece mahaifiyar sameemah wanda take zaune a gabanki a halin yanzu”
Sakkowa tayi daga kan kujerar da take ta matso zuwa kusa dani,har numfashinmu yana bugar na juna,hannunta tasaka ta rungumoni zuwa jikinta wanda yake rawa kar kar,
“Kece sameemah meyasa ban dago sunan ba bayan nasan sunane da ba’a cika jinsa a gun wasu ba,tabbbas kece kam babu tamtama,allah sarki kawata ta kaina hajara itadin mutumce mai wuyar samu,hakika ba karamin babbar ni’imace ba dana hadu da ita,nasan ko ban tambaya ba tayi miki rikon da koni iyakaci kenan”
Dagowa nayi daga jikinta duk da ban ki mu shekara a haka ba saboda wata sabuwar nutsuwar da take shigamin,saidai dolene na yi mata tambayoyi na dalilin bayar dani ga ummah hajara da tayi, bakina yana rawa kaman bazai budeba na ce,
“Amma in da gaske kece mahaifiyata kuma kina sona kaman yanda na gani a cikin idanunki, mai yasa kika rabu dani kika raba rayuwata da taki a lokacin danake tsaka da bukatar kulawarki”
Lokaci daya daga gama jin tambayartawa yanayin ta ya sauya gabadaya,hawaye yana zubowa daga idanunta kuma tana jijjiga kai.
“Ban rabu dake dan son raina ba,sai dan tseratar da rayuwarki sameemah,kuma har yau bana nadamar yin hakan,amma kiyi hakuri bazan iya fadamiki dalilin ba,banida ikon yin hakan”
Kallon ta koma kan sameer wanda yake goge hawayen tausayinmu nkda ita,
“Tabbas kam kai dan kawata hajarane dan ga kamar tanan a fuskarka,duk da ban taba ganinka ba amma nashajin labarinka sosai a wajen ta,fatana allah ya jikinta da rahama,sannan allah yasa halinta ya bita,yanzu kutashi mutafi wajen yaya fatima tukunna”
Daga haka ta mike daga tsugunnen da take kafin ta kama hannun sameemah wanda har sannan kanta yake sunkuye.
Dukkan mu gidan hajiya fatima muka tafi,cikin motar babu wanda yake cewa komai,saidai lokaci zuwa lokaci muke hada ido da saleemah,wanda said ta kawar da kanta kaman mai kunyar wani abu.
A falon muka sameta tana kallon news hankalin ta gaba d’aya yana kai,dan ko sallamar ma bataji sosai ba.
Kallonmu take da mamaki ganin mu har da doctor maryam sannna kowa fuskarsa tana dauke da wani abu daban.
Hannuna ta kama zuwa gaban hajiya fatima kafin ta kama nata ita ma ta rike,
“Yaya fatima kinga sameemah na ganta,saidai mahaifiyar tata wanda na bata ita ta rasu ,bansamu damar ganinta a karo na biyu ba,saidai nayi ta mata addu’a a kullum,dan ta nunamin kauna haka ma ta nun aw a jikina tsakininta da allah,tunda har ta raineta sannan kuma ta hada ta d’anta aure,babu abinda zan iya saka mata dashi yaya fatima”
Kuka take sosai wanda nake jinsa har cikin raina,ban san meyasa ba amma kukan sosai yake taba cikin zuciyata,hannuna na kai zuwa bayanta na dafa duk da bakina yagaza cewa komai.
Its kanta hajiya fatima bata ce komai ba sai tsshi da tayi ta nufi dakin ta tana cewa,
“Bari na Kira alhaji tukunna,dan maganar ba tawa bace ni kadai,yazo ga y’ar amininsa a raye bata mutuba kaman yamda muke zato”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button