WATA RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

[9/5, 11:28 PM] ❤️❤️ ???????????????????????? ????????: ⛱️⛱️⛱️ ⛱️⛱️⛱️

Rubuta wa :. Rashida yar mutan ????????

Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai

Allah yasa mu fara lafiya mu gama lafiya . Kuma wanan Labarin ƙirƙirare ne ban yishi dan cin zarafin wata ba.

Allah yasa mu gane mu gyara Allah ya muna kyakkyawan ƙarshe Amin ya Allahu ka shirya muna zuri’ar mu Amin ya Allahu ya rahamanu. Dun wanda yan ga kure ko abun da bai dace ba ƙofa abuɗe take zaku iya min magana dan ɗan adam ajizine Allah yaƙara muna fahimtar juna Amin

89 44 56 56

0️⃣1️⃣

Cikin sauri take tafiya tana riƙe da jaka baƙa ahannu ɗaya kuma tana ɗauke da ledodi sai sauri take bakin ƙofa ta tsaya jim kaɗan sai ga yara sun fito wasu na gudu wasu na tafiya wani yaro ne yan zo a guje yana dariya itama dariar take ta rungume shi tare da fida masa jakar sa kallon sa yayi yace

” Aunty ina mota ? “
Kallon sa tayi kamar baza tayi magana ba ɗaukar sa tayi taci gaba da saurin ta . Dan ɓata fuska yayi yace

” Ni ki jin dani zan iya saurin ”

Yi tayi kamar bata ji me yace ba fara kokowar zai sauka yayi juyuwa tayi taga yara na masa dariya sauke shi tayi tan juyu wajan yaran tace
” Wa yake so na ɗauke sa? “

Kowa buɗe hannayansa yayi suna faɗin ni! Ni murmushi tayi tan kalle shi tace
” Kaga yan class ɗin naku ma suna son ɗauka “

Murmushi yayi yace

” Ni fa bana so tun da ni babba ne mai bawa yara kashi”
Yana faɗa yana kallon yaran da gudu kowa yan bi hanyar sa murmushi yayi yace

” Aunty kin gani ko ?”

Murmushi tayi bata ce dashi komai ba kama hannun sa tayi sun ka ci gaba da tafiya. Ɗagowa yayi ya kalleta yace
”Aunty ina motar?”
Kallon sa tayi tare da shafa kan sa tace

” Motar ce ta samu matsala shine nake sauri na zo na ɗauke ka gar na barka kayita jira na dan na kira mai gyara to shine kaga nake sauri in ya zo ya tarar dani”

Murmushi yayi yace
” To Aunty muyi gudu kar ya zo ” yana gama faɗar haka yayi gudu murmushi tayi tare da gyaɗa kai ita ma ɗan gudu gudun tan fara basu wani jima ba sun ka iso dai dai da shima mai gyara ya iso gaisawa sun ka fara nan tan miƙa masa kiii ɗin motar tambayar ta yayi matsalar me ce ce

” Wani kuka take nayi tunanin zata kaini makaranta na dawo in naje gida sai na kira ka to shine ina tafe sai kuma ta tsaya ”

Buɗe gaban motar yayi yace

” Hajiya sai kun ɗauki abun hawa dan tayar ma dab take da ta fita Allah dai ne yan kiyaye yan zu zan kaita gareji kenan ko zuwa dare ne ko kuma da safe na kai miki ita makaranta”

Gyaɗa kai tayi . Yaron kallon ta yayi yace

” Aunty ba momy sun kusa sauka ba muje sai ta biya damu gida”

Murmushi tayi tace

” Muje gida zai fi bamu saniba ko tana office ko da mutane a ciki ”

” Ai sai mu jirata tun da suma sun kusa sauka sai mujira su wanje in kuma suna da baƙi zasu yi taro sai kawai muzo gida”

Murmushi tayi tare da shafa kan sa tace

” Muje ”

Tafe suke suna hirar su saman karatun da sun kayi yau haka suke har sun ka iso ma’aikatar suna zuwa sun ka tarar da mai gadi direban su da sauran wasu mutun biyu ma aikata gaida su mai gadi yan fara da gudu yaron yan je kan ciyoyin direban ya zauna bayan sun gama gaisawa ne tace

” Dan Allah ko Momy tana nan ?”

Kusan a tare sun ka amsa mata da tana nan

Yuce wa tayi kai tsaye bakin office ɗin tazo tare da buga kofar jin shiru yasa ta shiga kai tsaye tana shiga da sauri ta ce

” Momm cikin ɗaga murya haba Momm ” tana gama faɗa ta fashe da kuka ƙoƙarin gyara kan ta tashi ga yi . Tare da cewa
” Yi hakuri ba a son raina bane ko nayi ƙoƙarin dan ne zuciya mun din……”

Bata ƙarasa ba ta fice ta bar mata office sai da ta saka kayan ta tan fara neman gyalen ta can ta gan sa sai da tasa mu natsuwa kana ta gyara teburin tan mayar da komai wanjan sa ta ɗan jima zaune tana tunani kana tan nemi jakar ta turaren ɗaki ta ɗauko ta feshe da turare kana ta liƙe office ɗin tan yuce ko sallama batayi da kowa ba ta fice tsaye tan hagota cikin sauri ta ƙara so tace muje ko ?”

Too Masha allah.

Mine ne tatarar da Momm ta nayi ?

Muje zuwa insha allah
[9/5, 11:28 PM] ❤️❤️ ???????????????????????? ????????: ⛱️⛱️⛱️ WATA RAYUWA⛱️⛱️⛱️

0️⃣2️⃣ Rubuta wa Rashida yar tahoua ( tawa) mutan ????????

Bata ce komai ba ta tafi kusa da motar da gudu yaron yan ta so ya rungume ta yana dariya ita ma dariyar tayi tace
” ku shiga motar muje ”
Baya sun ka zauna ta shiga ita ma ta zauna Hajiya balki ta zo tace
” uhummm nace yaushe zamu haɗu ko na zo yau da dare? Dan har ga Allah ina bukatar wani abu ”

Murmushi Momm tayi tare da ɗaukar jakar ta ta buɗe ta ɗauko kuɗi ta miƙa mata tace
” Gar ki zo min gida dan Allah gasu na baki in wani abu ya taso da kaina zan zo nasa meki”

Murmushi Hajiya balki tayi ta amshi kuɗin tana jin daɗi a ranta kuma haushi da takaici ga samu ga rashi amma watarana zan kai ga inda bana zato aranta take magana . Suna hawa titi ta kelesu tace

” ya an kayi kuke a kafa ina mota?”

Yaron ne ya tashi tsaye kusa da kun nuwanta yace

” Mota ta lalace shine nace ma Aunty mu zo mu tafi tare tun da kun kusa sauka ”

Murmushi tayi tare da shafa kan sa kana tace
” Kenan da baka ce ta zo ba bazata zo ba ?”

Gyaɗa kai yayi alamar eh

Hirar su kawai suke ita kuma sai waya take dan nawa sun yi tafiya mai ɗan nisa tan kaleshi tace

” Mu tafi mu ci abinci ?”

Da sauri yace

” Eh ! Harda ice crème ”

Murmushi tayi sai tambi wata kwana wani kataɓaren restaurant sun kaje tsayawa tayi fitowa sun kayi zama sun kayi Momm gayin abun da take tayi shima yaron gayin abun da yake so yayi kamusu an kayi sauran kuma su kace asa lada dan ba sai sunyi girkin dare ba . Suna zuwa gida Momy ɗakin ta ta yuce tana zuwa wanka tayi tayi alwala tana gama sallah barci ya ɗauke ta bata haɗu da yaran ba sai bayan takwas na dare a falo tan tarar dasu suna kallon SUNNA TV kusa da ita ta zauna tare da rage sautin TV kallon ta tayi tace

” Ina Abdul ? ” Ko kallon ta bata yiba ta bata amsa da cewa yayi barci kusa da ita ta matsa tare da riƙe hannayan ta tace

” kune farin ciki na a duniyar nan kuna zan kalla naji dady bani da kowa bani da komai sai ku in Kin ce fushi zakiyi dani wane hali kike tunanin zan shiga ? Waye gare ni da zai share min hawaye in ba kuba ke ce babba Abdul yaro ne yanzu ne yake kece babba kece nake da kamar ƙawata yar uwata too in kin ce fushi zakiyi dani sai na zamo bani da yar uwa bani da ƙawa ”

Rungume ta tayi tace
” Momy ina son ku sosai kawai abun da kuke aikatawa ne baya min dady yana min ciwo sosai dan Allah Momy ku daina “

Ƙara rungume yar ta tayi hawaye na zuba ita ma kukan take sun jima haka .
Kwanta wa tayi saman ciyoyin ta sun ka fara hira , hira suke sosai suna dariya nan tan tambayeta

” Me yasa mu motar ki ?”

” Nima ban saniba Abdu yace dai Allah ne ya gyara da tayar ta fita ”

Shafa kanta tayi tace

” Allah yaƙara tsarewa ya ƙara karewa Amin ya Allahu yasa ma rayuwar ku albarka”

Kusan a tare sun kace Amin

Kallon ta tayi tace ki zubo muna abin cin nan .

Tashi tayi ta ɗauko ledodin nan sun ka zube suna ci suna hira suna dariya . ” Kisa ma Abdul ice crème inshi a firji . Ga kee ɗin mota na can ki ɗauko min jakata akwai wasu ladodi a mota ki biyu dasu ”

To ” ta amsa tare da tashi ta amshi kii ɗin tana fita bata wani jimaba ta shigo da sallama miƙa mata tayi , Amsa tayi tare da buɗe jakar ta tayi tare da ɗauko wasu maƙudan kuɗin tan mika mata tace

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Leave a Reply

Back to top button