WATA RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

MASHA ALLAHU
[9/5, 11:28 PM] ❤️❤️ ???????????????????????? ????????: ⛱️⛱️⛱️ WATA RAYUWA⛱️⛱️⛱️

1️⃣5️⃣. Rubuta wa Rashida yar tahoua ( tawa ) mutan nijar ????????

Ina godiya sosai da addu’ar da kuke min ina godiya sosai da comments ɗin ku Allah ya bar abun da yan haɗa Amin ya Allahu

Suna fitowa dai dai lokacin da ƙawar tasu ita ma tana ƙoƙarin fita Zainab ce tan kira sunan ta tsayawa tayi sai da sun ka iso wajan ta sun ka yuce kusan motar su kallon ta Zee tayi tace
” Yanzu nan ne gidan ku ”

Tan ƙarasa maganar da nuna gidan da hannu tana fashewa da wata irin dariya tan ƙara da cewa
” Keda kin kace gidan ku soron bene ne anshe gidan kun ma… ”

Bata ƙarasa ba Hajara tan katseta da cewa
” Ya isa haka dan Allah ya isa haka ” tana faɗa tana ƙoƙarin sakata cikin motar ɗaga murya Zee tayi tace
” Arage ƙarya dan wlhi watarana mutun zai ga mamaki a dun…. ”

Katseta Hajara tayi tace
” Nifa na tafiya ta mutun yana jin kunyar ma haɗa ido da kai amma sai ƙoƙarin kiga idon nata kike”

” Haba yar uwa ai gwara ki bari na rama tunda nima tamin ranar har abinci tace bazata ciba tunda mun saka hannu ɗiyan tallaka basu iya komai ba sai ci da ƙwaɗayi ”

” Eh tunda ta faɗa yan zu tayi na dama sai a yafe mata a yuce gaba”

” Humm ai ko asirrin ta ya kusa tonuwa tunda naji wasu yan ajin mu sun ce zasu zo sunan ranar suna . Yawwa dan Allah mu biya musha ice crème”

Kallon ta Hajara tayi tace
” Kina da kuɗi ne ?”

” Eh ina da kuɗi ajaka ta ”

” Ok to amma fa gar mu jima ”

” Ah ah da mun shafa shike nan in ma mun tarar da jama’a zamu saya muje dashi gida ”

” Ok to ”
Hajara tan faɗa tare da karya kan motar tabi wani titin basu yi wata tafiya ba sun ka iso wajan . Wajan da an ka tanada dan motoci ci tan aje fituwa sun kayi waje sun ka samu sun ka zauna Zee ce kawai tace akama ta . Hajara kuma cewa tayi asa mata uku a leda . Kallon ta Zee tayi tace
” Baza kisha ba anan ?”
” Eh zan je dashi gida ga Mom ga Abdul zamu sha tare kin ga muna sha muna hira ”

Zee zata yi magana wasu su biyu sun ka zo sun ka zauna a sauran kujerun kallon juna sun kayi ita da Hajara Zee zata yi magana ɗayan yace
” Kin sha kyau yan mata abokina nada buƙatar nombrki ”. Yan ƙarashe maganar da nuna Hajara . Hajara kallon Zee tayi tayi mata alamar mu tafi kusan a tare sun ka tashi tsaye riƙo gyalen ta yayi yace
” Yan mata biki ji me nace ba ?”

Ganin alamun basu da niyar sakin gyalen ta Zee ce cikin zafin nama tan ƙwace sa daga hannun ta tan riƙe hannun Hajara sun ka fice suna zuwa kusa da mota da sauri yan je ya tsaya musu a bakin mota gannin abun zai zama raini Zee tan koma wancan ɓangaren tare da amsar kiii ɗin hannun Hajara tan buɗe tan shiga tan tayar da mota buɗe ma Hajara tayi gidan baya ta shiga shima shiga yayi ɗayan leƙowa yayi yace
” ɗan Hajiya fito ”
Yana fitowa yan shiga kallon su yayi yace
” Kuyi hakuri dan Allah ko zan iya….”

Bai ƙarasa ba Zee tace
” Ohhh kana da bakin magana na ɗauka magana sai an ma baka iya magana ”

Cikin ɗaga murya Ɗan Hajiya yace
” Kee yarinya ki kiyayi kanki kin san da wa kike magana”

Fitowa tayi daga motar tayi dariya kana tan kalle shi sama da ƙasa tan nuna sa da hannu tana cewa
” Ni ban san kowa ba sai kaina kuma kaima ina baka shawara kaje kane mi sana’a zai fima aikin baran da kake sakaren banza marar aikin yi ”

Tana gama faɗa tan tayar da mota tace
” Malam ka fita muna da abun yi kaji “

Kallon ta yayi yace
” Kina cema wani ya nemi abun yi ina ga sana’ar ku ɗaya dashi tun da ni ga wanda nake magana da ita kece mai amsawa ama dadin ta ”

Fara tafiya tayi tace
” Wlhi idan baka fita zan maka ihun ƙwarto wlhi ”

Wani murmushi yayi yace
” Ok naji ”

Yana gama faɗa yan fita daga motar kallon sa yayi yace
” Ɗan Hajiya asa mun in da gidan su yake dan Allah sai na ɗana su suduka an bini da lalama ya tan ƙare banle kuma anbini da garaje hummmm ”

Murmushi ɗan Hajiya yayi yace
” An gama ai sai kayi an so ba’a so ba ”

Ta madubi Zee ta kalleta tace
” Yi hakuri na kora miki sauri ”
Ɗan dukan ta tayi tace
” Ba saurayi ba sai miji ”

” Ahhh nasani naga bike komai ba”

” Wlhi dama na gansa wata faɗuwar gaba tan zo min amma ni baya daga cikin layin waɗan da nake so ”

Murmushi Zee tayi tace
” Muji gaskiya dai yar uwa kodai ina masifa kina tsine min a ranki ”

” Uhummm ai da nayi magana marin sa ne zan yi kin ga kuma in nan maresa akwai matsala babba ”

” Haka ne wlhi Allah dai ya iya muna ”

Suna fita Hajiya Aisha tan kira Alhaji in da zata tardo shi yan gaya mata dama da shirin ta kai tsaye tan fita tan ɗauki motar ta kai tsaye in da yan faɗa tan tarar dashi tana zuwa ta tarar dashi a harabar Hotel ɗin bin sa abaya tayi dama kan ta iso ya ɗauƙi ɗaki suna zuwa ya juyo . Jada baya nayi nace wazan gani haka too wata sabuwa…

Zama tayi bakin gado kusa da ita yan zauna tare da riƙe hannun ta suna gaisawa daga nan yan fara shafa ta sai kuma sun kashiga wata duniyar sun jima haka suna gamawa Hajiya Aisha tace
” Ni zan yuce ”

Kallon ta yayi tare da janyo ta ajikin sa yace
” nifa ban gamsu ba ”
murmushi tayi tace
” Dare keyi fa kuma ina da yara bana son su zo bana….”
Bata ƙarasa ba yan game bakin su…..

Sun ɗan jima tafe kan su iso gida suna zuwa ciki sun ka yuce da sallama sun ka shiga fallo Mom sun ka tarar tana koya ma Abdul karatu suratul naba’i . Kallon su Mom tayi tace
” Har kun dawo ?” amsa wa sun kayi da ehh. Miƙo ma Abdul da Mom ice crème ɗin tayi tace ga naku
Abdul murmushi yake yace
” Aunty na gode sosai ”
” Harda crème kun ka tsaya saye?”
Cewar Mom

” Eh Mom wlhi mun tsaya musha sai wani yan zo yana ma mutane wai dear tabasa nombr ”

Cewar Zee

Mom kallon su duka tayi tace
” To ba sai tabasa ba me yake ?”

” wlhi Mom wani ɗan rainin wayo ne shi yana tamaƙar ɗan wani ne ”
Cewar Zee

” To da kanku kun gane kenan ba irin mijin aure bane kenan ?”
Cewar Mom

” Wlhi Mom ko alama bai da irin wanan ariƙa lallaɓa mace shi komai sai yace isa da izza za’a masa ”
Cewar Hajara
Murmushi Mom tayi tace
” To kurika sanin wane mutane kuke mu’amala dasu dan kar wani ya zo da kuɗi ko ƙarya da ɗaɗin baƙi . Dun namijin da zakice ma yaje yaga iyayen ki yan tsaya yana ce miki har ku fahimci juna to yi ƙoƙarin nisa da shi dan ba aure ya zo ”

” Insha Allah Mom ”

Zee tashi tayi tace ” ni zan tafi ”
Kallon ta Mom tayi tace
” Bari mu ci abinci ”

Hajara kicin tan shiga ta zubo abin cin cikin ƙaton faranti tana ajewa tan koma ta ɗauko ruwan sha da na wanke hannu su duka sunka sa hannun su suna ci har da Mom suna ci ne tan ɗauki waya tan tura ma Hajiya aisha taso cewa
” Kiyi sauri yaran fa sun iso ”

Ganin har sun kusa gamawa bata buɗe sakon ba tan kira ta sai da ta ɗauka tan katse
Jim kaɗan tan mai do mata
” Na gama yan zu ma zan je gida”

” Ok to baza ki biyo ba ko na minti biyu ba naji ɗumin jikin ki ?”

Dariya tan turo mata tace
” nagaji sosai amma zan biyo tun da kin ce ”

” Ok na gode Allah ya kawo ki lafiya ”

MASHA ALLAH[9/5, 11:28 PM] ❤️❤️ ???????????????????????? ????????: ⛱️⛱️⛱️ WATA RAYUWA ⛱️⛱️⛱️

1️⃣6️⃣. Rubuta wa Rashida yar tahoua ( tawa ) mutan nijar ????????

Ina godiya sosai da comments ɗin ku Allah ya bar zumunci amin ya Allahu

Suna gama cin abincin sun ka ɗora da shan fruits suna tsaka da sha ne Hajiya Aisha ta shigo da sallamar ta gaisawa sun kayi kana tan zauna tana
” Wayan nan kayan marmarin da ni za’asha gaskiya ”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Leave a Reply

Back to top button