WATA RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

” Ga su nan ki saka su ta asusun bankin ki in kina da buƙatar wani abu ko ɗan uwan ki ba sai kin neme Ni ba ko kin jira na baki ”

Amsawa tayi tana juyawa kana tace

” Mom akwai sauran kuɗi fa bamu ma kashe su ba ”

” Ehh nasa ni wanan ribar ku ce wanda naba da ana juya muku wayan can kuma albashina , bana son ku zo kuna kukan rashi ko ku nemi wani abu ku rasa kuma ina son dan allah garki sa in da bai dace ba kiriƙa saka su inda yan dace dan Allah gar kiga kina da ƙudi kiriƙa abun da bai dace ba kiji tsoran Allah ”

Hawaye sun ka zubo mata tashi tayi ta rungume ta tace ” ina son ki Momy na Allah yaƙara muku lafiya da tsawon rai ya biya buƙatun ku na alkhairi”

Amin ta amsa

Kallon ta tayi tace

” Nace ma asamo miki motar da tafi wanda kike hawa , ban saniba ko gobe ko jibi ya kawo kenan ko ya kawo ki amsa ”

To ta amsa

MASHA ALLAH

Yanzu muke fa muje zuwa. Gyara ko shawar wari ƙofa abuɗe take
[9/5, 11:28 PM] ❤️❤️ ???????????????????????? ????????: ⛱️⛱️⛱️ WATA RAYUWA⛱️⛱️⛱️

0️⃣3️⃣. Rubuta wa RASHIDA yar tahoua (tawa) mutan ???????? nijar

Hasbunallah wa ni’imal wakil

Tan ƙara yi mata godiya kallon ta tayi tace

” Momm zan yuce ina da exercice da zan je na yi gobe zamu kai su ”

Ɗago kai tayi tan kalleta kana tace
” Yan zu har kin koshi ? Naga biki ci wani abun kirki ba ”

Dan murmushi tayi tace
” Ɗazu ma da na zo na dafa indomi har Abdul yaci dan ban son ya kwana da yuwa”

Gyaɗa kai tayi tayi murmushi tace
” Haka yayi amma gar ki manta gobe Alhamis azumi ”

” Eh ban manta ba shiyasa naci sosai dan ko na makara ban yi sahur ba zan iya yucewa dashi”

”Masha Allah Allah yabada lada yasa ma rayuwar ku albarka ya shirya min ku ya Allah ko na mutu gar yara na su zama ƙaskan tatu walakantantu ” kusan a tare sun ka amsa da Amin

Kama hannun Mom tayi tace

” Shiyasa naƙe son Mahaifiyata dan tafi kowa ce uwa a dauniya”

Murmushi tayi tace

” Kai mamana ban da son kai”

Murmushi tayi tace

” Ba son kai bane ina alfahari da Mom ɗita sabida ko ranta ya ɓaci tasan me zata furtama yaran ta tana control ɗin kanta kulun tana cikin muna addu’ar shiriya da tsare mu a koda yaushe saɓanin wasu uwayen su ke musu mummunar addu’a alhali basu san addu’ar uwa tana da tasiri akan yaran ta ba….”

Murmushi tayi tace

” Ya isa haka kije kiyi aikin ki dare nayi ”

” To bari na tattare kayan da mun kaci ”

” No barshi kawai in nagama zan ɗauke komai ”

” Ok Mom sai da safe ”

” To Allah ya tashe mu kima Abdul addu’a ”

Juyuwa tayi ta kalleta tare da langwaɓe kai cikin muryar shagwaɓa tace
” Na masa fa”

Zatayi magana wayar ta tayi ƙara ɗauka tayi tare da amsa sallamar jim kaɗan kuma tace to shike nan Allah ya kai mu rai da lafiya . Tana gama wayar tan juya taga ko tana nan taga bata nan ci gaba da cin abincin ta tayi tana gamawa ta ɗauke komai taje ta liƙe kofofin da tagogi ta koma ta zauna wayar ta ta ɗauko wathssp ta shiga wani group ta shiga mai suna femme class ( Mata masu aji )
Shiga tayi ta dun duba wasu saƙon ni na amsawa ta amsa saƙon wata tabi ta privat saƙo ta fara tura mata kamar haka
” Tayaya zaki biye wa Hajiya balki dan Allah ita Hajiya Balki ɗin ma har wata abu ce da zaki tsaya kina ɓata lokacin ki akan ta haba dan Allah ”

Ita ma bata amsa tayi kamar haka
” Haba Hajiyata kin ji me take cewa fa ai kin shiga group kin gani ni fa ba ruwana da ita dan a cikin group ɗin ma ita ce Zakka acikin mu kawai da ta ɓata min rai ne shiyasa har nan taka ta ”

Dariya tayi sosai tace

” Walhi kin ban dariya to me nene na murya tana rawa kamar zakiyi kuka ”

” Walhi Hajiyata naji kishi ne sosai wai Hajiya Balki ɗazu kun haɗu haba wlhi naji kishi ”

” Kwantar da hankalinka kin san wace ce ni ai kawai na kasa gane kaina ne ina office na kirata kuma ta zo bamu ma kai da yin abun da nake so ba Mamana ta zo office ɗin kin ga ko ba abun da ya faru dan Allah ki kwantar da hankalinka ke mee zaki wani ji kishi Hajiya Balki ita da bata da aiki sai maula kin bata zata sake tambayar ki kowa ce présidente tace tana nema ita zata ce zata iya to ”

” To shi kenan na gode Hajiyata nayi kewar ki sosai ”

Murmushi tayi tace

” Nima haka tawan sai dai kin zo ”

Sallama sun kayi kashe datar tayi ta tashi ɗakin su Abdul ta nufa bata kai da shiga ba wayar ta tafara ƙara dawowa tayi ta ɗauka

” Uhummm Amin alaikin Salam ”

Daga can ɓangaren cewa akayi
” Sorry ban yi sallama ba , ya kike ?”

”Lafiya lau”

” Yawwa na kira ne nace na zo na taya ki barci yau tun da Hajiya aisha bata nan ?”

Murmushi tayi kamar baza tayi magana ba tace

” Ah ! Ah ! Na gode Hajiya Balki ”

” Haba Hajiya…..”’

Bata ƙarasa ba ta katseta da cewa

” Zan yuce wani aiki nake ”

Bata ji mi zata ce ba ta katse wayar da ajeta

Ɗakin yaran ta nufa tattarar da su har sun kashe wuta sun kwanta kun na wutar tayi tace

” Mamana har kin kwanta?”

Ɗaga mata kai tayi alamar eh

Kusa da gadon Abdul ta zauna addu’a ta masa ta shafa masa tashi tayi ta zo kusa da budurwar ita ma addu’ar ta mata ta shafa mata ta kalleta tace

” Har kin gama aikin da an ka baki ne ?”

” Eh na ida har na duba karatuna ”

” Masha allah allah ya taimaka , yawwa ɗazu oga ya kirani gobe da safe muna da ziyarar minista kenan tun shida dan fita ga kii ɗin mota na kije da ita ni zan ce tare da oga dan nayi tunani zan aje ku na yuce to sai ɗazu ne ya kirani yake gaya min”

Miƙa mata kiii ɗin taya kallon kiii ɗin tayi tace

”Mom wlhi ina jin tsoro in je da motar ku makaranta yan fashi nake tsoro kuma dama ni ko wani abu ne in bai birge su ba zasu ce zasu kashe ni”

Cikin sauri ta kalleta tace meee?

” Wasu samari ne su biyu sun dame ni kullun sai sun min barazana ”

Kamata tayi tace

” Haba Mamana miyasa baki gaya min ba dan ɗaukar mataki tun da yuri dan amasu kashedi ”

Kama hannu Mom tayi tace

” Ah !Ah ! Mom dan allah kuyi haƙuri abun da yasa ban faɗa ba sabida nasan Mom ɗin na zata tsaya min sai inda ƙarfin ta ya kare to su kuma suna ganin sune keda ƙasa ubansa yana iya yin komai a kan farin cikin ɗan sa ”

” Ok uban sa yana iya yin komai akan ɗan sa ? Ke kuma ba’a iya yin komai a kanki sabida ke ba ya bace ba haifar ki ankayi ba? To ko shi ɗan shugaban ƙasa ne zai san kina da gata , ke har kin manta waye uban ki ko dan kina ganin ya rasu ba wanda zai tai maka muna ?….”. Zata ci gaba kuma tayi shiru da sauri ta tashi tace

” Ki turo min suna yen su da uban su ta wathssp yan zunan ”

Bata jira me zata ce ba ta yuce tare da kashe musu wuta

MASHA ALLAH

Tofa muje zuwa yan anka ce
[9/5, 11:28 PM] ❤️❤️ ???????????????????????? ????????: ⛱️⛱️⛱️ WATA RAYUWA⛱️⛱️⛱️

0️⃣4️⃣. Rubuta wa Rashida yar tahoua (tawa) mutan nijar????????

La’ilah illah anta subahanaka inni kun tun minan zalimin

Kwance take tanana tunani da sauri kuma ta tashi ɗakin Mom taje buga kofar tayi izinin shigowa ta mata koda tashiga ta tarar da ita zata fara sallah zama tayi a bakin gado tana wasa da yatsun ta hijab ɗin ta Mom ta saka kusa da ita ta zo tace
” Mamana lafiya dai ?”
Hawaye ne sun ka fara bin kuma tun ta . Kamata tayi tan jayuta a jikin ta shafata take sun jima a haka sai kuma ta ƙara tambayar ta tace
” Baki da lafiya ne “?
Gyaɗa kai tayi alamar ah!ah
” To me ne ne ke damun ki ?”

Kama hannuwan ta tayi tace
” Mom dan Allah gar ku sa a kori yaran nan dan Allah “

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Leave a Reply

Back to top button