WATA RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Sun jima haka Hjya Aisha kallon ta tayi tace
” Hajiyata ko dai wani abun an ka haɗiya?”

” Wlhi Hajiyata nima abun har mamaki yake bani kin san gani nake abun na sauki sai kiga kuma wani lokaci kamar mahaukaciya abun ni har tsoro yake bani ”

” Kiyi ta addu’a Hajiyata Allah ya yaye ma kowa damuwar sa ya shirye mu yasa ma yaran mu albarka ”

Amin ya Allahu

Kallon ta Hjya Aisha tayi tace
” Sallah zan yi ”
Bata jira me zata ce ba tan yuce ban ɗaki ta ɗan jima kan tafito ɗaura ƙirji tan fito da shi dogon hijab ita tan ɗauka tan fara sallah tana gamawa tayi addu’a tajima tana addu’a kana tan shafa kayan ta taje ta ɗauka tan cire hijab da sauri Mom ta zo juyowar da take tan ganta da sauri tan ɗan ja dabaya tace
” Har kin bani tsoro ”
Kai tsaye hannun ta takai kan kirjin ta Hjya Aisha kallon ta kawai take a ranta tace
” ikon sai Allah Allah Ubangiji ya rufa mana assiri ya kare mu ya tsare mu ya shirya muna yaran mu ”

Hjya Aisha biye mata tayi baka jin komai sai nishi….

Waya ce keta kuka tana neman agaji ɗago kai yayi alamar barci yake ɗagawa yayi ya aza kunnen sa bata reda yace komai sai da yan ɗan jima yace
” Ok ɗan Hajiya zan kira ka in nafito ”
Bai jira me zai ce ba yayi yurgi da wayar liƙe idon sa yayi

MASHA ALLAHU LAKHUWATI ILLAH BILLAH

INA GODIYA SOSAI
[9/5, 11:28 PM] ❤️❤️ ???????????????????????? ????????: ⛱️⛱️⛱️ WATA RAYUWA⛱️⛱️⛱️

1️⃣4️⃣. Rubuta wa Rashida yar tahoua ( tawa) mutan nijar ????????

Yajima a haka kana yan tashi da dan dafe dan dafe ya kai ban ɗaƙi ya jima a ban ɗaki kana yan fito wasu kaya yan ɗauko masu kama da sama wato blue takalma farare da hulla kalar kayan jikin sa yan feshe da turare kana yan ɗauki kiii ɗin motar sa tare da wasu abubuwan buƙata yan maida a aljihun kayan yasa ka liƙe ɗakin sa yayi yan sauko yana cikin saukowa ne dai dai da wata budurwa da bata yuce sha hudu ba ɗan bige sa tayi da sauri tan ɗago kai suna kama sosai da Hajara sai dai Hajara tafita kyau kallon ta yayi yace
” Ƙanwata ina zuwa har da bige ni haka ?”

” Momy ce tan aike ni shine tace nayi sauri. Yaya ina zuwa haka wanan wankan ? gaskiya yaya manyan kaya sun fi maka kyau ”

To kauce kiga ni ina da abun yi ba surutun kiba yan raɓa ta gefen ta yan yuce fallo yan tarar da Momy tana zaune tana shan kayan marmari a gefen ta kuma Kulu ce a zaune kallon su yayi tare da gaida su Kulu ce kawai tan amsa masa ko ajikin sa jus yan ɗauko yan zauna a table ya zuba yana sha wayar sa ce tayi ƙara ɗaukawa yayi tare da ” faɗin kawai kashirya ni nagama ”

Dai dai da ƙanwarsa na zuwa kallon ta yayi yace
” Dan Allah ko zan iya samun thé dan allah ?”

” Ok to bari na gama ma Momy aikin da tasa Kani ”

” Ok na gode”

Kayan ta tasaka tace
” Yau nasan zan yi kwana mai natsuwa ”

Hjya Aisha kallon ta tayi tace
” In nayi sauri gamawa dashi wata ƙil in zo in kuma ban zoba sai Litinin in mun haɗu ”

Wani kallo Mom tan watsa mata tace
” Kice abun da bana so shi zan fara ”

” Me bakya so ?”

” Bibiyar matan ƙungiya mana”

Murmushi Hjy aisha tayi tace
” Allah ya baki haƙuri Hjyata. Amma ki shiga kiyi wanka ko ?”

” No zan je gida kin san Mamana zasu fita to bana son tayi ta zaman jirana ”

Tana gama saka kayan ta tan fara neman jakar ta kallon ta Hajiya aisha tayi tace
” Hajiyata jakar ki na falo”
Murmushi tayi tace
” Kin ga har na manta ”
Suna zuwa falo tan ɗauki jakar ta kallon ta Mom tayi tace
”ki koma kici gaba da aikin ki na katseki ”
Murmushi Hajiya aisha tayi itama tace
”No Bakomai kar ki damu ”
Kusa da ita ta zo tare da rungume ta tace
” Na gode sosai Hajiyata ”

” No dan Allah godiyar ta isa haka yau ne anka fara haɗuwa? “

Kallon Mom tayi tace
” Yanzu ma anka fara dan ba’aje ko ina ba ”

Tana gama magana tan gama bakin su sun gima a haka wani sallon zatayi Hajiya aisha tan tare ta da cewa
” Sauri kike fa kuma kar zainab ta shigo kin ga akwai matsala in tan tarar damu haka ”

Ficewa tayi tare da mata sallama tana shiga motar ta ta juya kenan sai ga zainab tana shiga gida tattarar da Mama kicin sallama tayi tace
” Mama baƙi kun kayi ne ?”
Bata ɗago ta kalleta ba tace
” Eh wata ƙawata ce ta zo ”
” Ok zan ce nayi wanka kan Hajara ta iso ”

” Ok ”

Tana barin gida wani ƙaramin restaurant ta biya ta saye abun ka ta saye ta yuce tana zuwa tan tarar da Hajara tana girki kallon ta tayi tace
” Mamana ke kike girki ?”
” Eh Mom bana son abin cin saye in ba dole ba”

” Ok naga mu kaɗai ne balle ace kullun kin zo kina girki ”

” No Mom in mu ƙadai ne zamu iya yin miya biyu har uku sai kuma tajima a firjin shin kafa ko wani abun kawai zamu dafa ba wani ɗaukar lokaci amma abin cin saye wani wlhi kana cin sa kamar kayi amai ba ɗanɗano a ciki zaka ga nama bai dafuba sai tauri miya kamar miyan kaji ga kuma…. ”

” Ya isa Mamana yan zu dai zamu ci nida Abdul in kin gama ki barshi mun ci da dare ”

Ok tan faɗa tan ci gaba da aikin ta kallon ta tayi tace
” Ki fida ki aje mana in kin sha ruwa zaki so cin abun ƙwaɗayi ”

To tan faɗa kifi da kwalbar yaourt Kawai ta ɗauka tace
” Ya isa ”
Zama ita da Abdul sun kayi sun kafara ci suna ci suna fira tana masa yan tambayoyi kan makarantar su yana bata amsa suna cikin haka ne malamin su yan zo tashi tayi tace
” Mamana ki barshi zan ƙarasa malam ya zo ”
To tace tare da ɗauraye hannayen ta Abdul ya kai masa kujera tare da aza tabarma sun ka fara karatun sai ana magariba sun ka gama yana tafiya suma sun ka tashi dabino da thé Mom tan miƙa mata tace
” Mamana ga wanan”
ƙarɓa tayi tare da godiya
Suna gama sallah tan kira zee tace da ita
” Ganinan zan zo ”

Wanka tan shiga bata wani ɗauki lokaci ba ta kamala riga da zane ne na atamfa tasa ka tare da ɗauko ɗan ƙaramin gyale wanda zai yi tafi da kayan ta saka bata yi wata kwanliya ba tan ɗauki takalma kalar jakar ta fitowa tayi . Mom kallon ta tayi tace
” Wanan wankan fa yayi Masha allah sai dai wanan tafiya ki gyara ta gaskiya bata dace da yan mata ba koni da an tsohuwa nayi wanan tafiyar ”
Tashi tayi tan nuna mata yan da zata yi ta kuma gyara mata ɗaurin ɗan kwali . Godiya tayi sosai kana ta fita cikin ɗan ɗaga murya Mom tace
” Addu’a fa gar amanta kuma kar ajima ”

” Insha Allah Mom sai mun dawo ”

Bata wani jima ba tan iso gidan su zainab fita tayi tace ta gaida Hajiya aisha itama fatan dawowa lafiya tayi musu

Kallon ta Zainab tayi tace
” Kai gaskiya kin haɗu ba ƙarya kin sha kyau ”

Murmushi kawai tayi tace
” Na gode ”

Basu yi wata doguwar tafiya ba sun ka iso gidan zainab kallon Hajara tayi tace
” Yar uwa dama nan ne gidan su ? Ko dai kin manta unguwar ko gidan ?”

Wani kallo tan yurga mata tace
” Kin ga ni tashi mu shiga ba ruwa na da tsegumin ku da kun ka saba ”

Dariya Zainab tayi tace
” Allah tsine maƙaryaci gaskiya ƙarya batayi ba in ta zo makaranta tana ƙarya kalli gidan su dan Allah ”

Tan ƙarashe maganar da dariya har da riƙe ciki
Hajara ce tan harare ta kana tan yi gaba bin bayanta tayi suna shiga sun ka ganta jakura tan musu har ciki gaida ta sun kayi mahaifiyar ta cewa tayi abadu Baby sun kace Ah ah abar shi kwancin sa kuɗin ta ɗauko tan miƙa mata tace
” Mom ce tace abaku kun ƙara hidimar suna ”

Dai dai lokacin da baban ta yana shigowa ai kuwa sun ka fara rigimar ai shi za’a miƙa wa kuɗin tun da shine mai sayen rago da kayan suna ita kuma tace ai ita aka bawa suna ganin rigimar nata girma ma sun ka tashi sun kayi tafiyar su

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Leave a Reply

Back to top button