WATA RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Yan ƙarasa maganar da kashewa dawa ta irin dariya
MASHA ALLAHU LAKHUWATI ILLAH BILLAH
INA GODIYA SOSAI DA MASU KARATU ALLAH YAƘARA LAFIYA . NA GODE SOSAI DA COMMENTS
[9/5, 11:28 PM] ❤️❤️ ???????????????????????? ????????: ⛱️⛱️⛱️ WATA RAYUWA ⛱️⛱️⛱️
1️⃣9️⃣. Rubuta wa Rashida yar tahoua ( tawa ) mutan nijar ????????????????
Ina godiya sosai da comments ɗin ku ta dalilin comments ɗin ku nake jin ƙwarin goyiwa na gode sosai
Kallon sa tayi tace
” Yanzu….”
” Dan Allah ya isa haka yara dai yara na ne ko dukiyar ma tawa ce , to sau nawa zan nanata miki ? Wlhi da ace bake kin ka haifesu ba da nace kina bakin ciki ne dub…..”
Bai ƙarasa ba yan ji ana hayaniya ana ɗaga murya kallon juna sun kayi alamar waye tun da farar safiyar nan kusan tare sun ka fito filin gida . Wani dattijo ne ke ƙoƙarin shigowa mai gadi kuma yana ƙoƙarin tare shi suna fitowa Umar ne yace
” Lafiya ?”
Mai gadin ne ya amsa da
” Wlhi wanan ne yake neman….”
Da sauri dattijon yace
” Aw har kana da bakin magana ka manta wanan yarinyar ?”
Yana magana cikin ɗaga murya yan ƙarasa maganar da nuna musu wata budurwa da take bayan sa
Ɗan ya mutsa fuska Umar yayi yace
” Ban ganeba gaskiya ”
Dattijon kusa dashi yan zo tare da cakumo wuyan rigar sa yace
” Kai sai Allah ya tsine ma albarka kai har ka manta wanan yarinyar ?”
Da sauri Dady yace
” Kaga malan gar ka yarda ka jimin da yaro dan wlhi in kaji masa ciwo hukuma ce zata rabani da kai ”
Momy ce tace
” Malan lafiya dai ? Wani abu yan faro ?”
Kallon ta yayi yace
” Kin ga wanan tsinan nen albarkar nan ne jiya da misalin karfe bakwai na yamma yan zo har gida shida wani sun kayi sallama dan cin mutun ci da rashin kunya sun ka bukaci da yata ”
Yanuna musu yarinyar
Yan ci gaba da cewa
” Tana fitowa sun ka shiga sun ka gaida ni azato na yaran kirki ne sun ka ɗauki kuɗi sun ka miƙa min na nuna Ah ah sun ka yi magiyar duniya naƙi karɓa sai da mahaifiyar ta tan amsa tare da musu godiya ”
Yana cikin maganar yan fido kuɗin yan nuna musu tare da watsoma Umar kuɗin yaci gaba da cewa
” Daga mun bar su a ɗaƙin yayan ta dake zauren gidan anshe shi manufar da yazo da ita ba mai kyau bace ”
Hawaye nu sun ka zubo masa yan saya yana share hawaye yaci gaba da cewa
” Shine fa sun ka sumar da ita sun ka biya buƙatar su da ita…..”
Bai ƙarasa ba Dady yan katse shi da cewa
” Kai ma haukacin ina ne da ganin yaro ganin farko ku barshi da yarinya a ɗaki ? Ko baka san…”
Bai ƙarasa ba dattijon ya katse shi da cewa ” Haba gar kayi tunanin haka kasan da zuwan sa na farko ne bazai yiwu ba na gane sa har na gano gidan su ba kuma a ƙa’idar mahaifiyar ta in namiji yazo zan ce wajan ta bazai yuce awa ɗaya ba kuma bata fitowa ita kaɗai sai tare da ƙawa ko yar uwar ta kaga…..”
Cikin ɗaga murya Dady yace
” Ku fice min da gani in ba son kuke na muku rashin cin mutun ba daga kai har ɗiyar taka ”
Kallon sa yayi yace
” Haka ma zaka ce ? To shike nan ai in kafi karfina baka fi karfin huku ma ”
Dady kallon mai gadi yayi yace
” In sun kara minti ɗaya a nan zaka ga me zai faru ”
Yana gama maganar yan yuce ciki Momy ce tan kalli dattijon da yake ta Allah ya isa yana ƙara tsine ma Umar kallon sa tayi tace
” Dan Allah kayi hakuri ”
Kallon mai gadi tayi tan ci gaba da cewa
” Ka karɓar min numbr wayar su dan Allah ”
Tana gama faɗa bata jira me zai ce ba tan yuce tana zuwa ta kalli Umar tace
” Dan Allah kafaɗi gaskiya kayiwa yarinyar nan fyaɗe ?”
Cikin ɗaga murya yace
” Kinga Hajiya in ma yayi ba na miji bane to ai rayuwa ta gaji haka kenan bana son sa ido ”
” Amma Alhaji hakan bai da…”
Bata ƙarasa ba yace
” Kaga ɗana ga wasu kuɗin kayi abun da kake so daga duniya sai kuma… Kasa ni ai , kuma ba wanda yan isa ya kamaka hukuma ta muce ”
Murmushi yayi yan rungume Dady yana faɗin
” Godiya sosai Dady Allah ya karo arzikin da yafi wanda anda kwai yaƙara shekaru irin na dabino ”
Amin ya Allahu na gode sosai
Wayar sa ce tan fara ƙara ɗauka yayi tare da tashi zuwa wani wajan
” Hajiya Aisha manyan mata Hajiya Aisha ba kida sa’a ”
Katse sa tayi da faɗin
” Ya kake My Alhhjjjj ? Wanan kirarin duka Ni ɗaya ?”
” Ai kin fi ƙarfin haka Hajiya Aishhhh ”
” To godiya nake , yi haƙuri dan Allah na ƙatse maka uzurin ka dama dan nace ma ne ina da wani uzurin da zan yi baza mu samu damar haɗuwa ba ”
” Ok Hjya babu matsala Allah yasa dai lafiya ?”
” Lafiya lau muna da ziyara ne nida yarana da yar uwata shiyasa”
” Wayo to gobe dai zaki daure mu haɗu ko ?”
Eh kawai tan faɗa tan katse wayar
MASHA ALLAHU LAKHUWATI ILLAH BILLAH
[9/5, 11:28 PM] ❤️❤️ ???????????????????????? ????????: ⛱️⛱️⛱️ WATA RAYUWA⛱️⛱️⛱️
1️⃣8️⃣. Rubuta wa Rashida yar tahoua ( tawa ) mutan nijar ????????
Washe gari tun da safe tan leƙo ɗakin Mom tan tarar da ita tana sallah komawa tayi ɗakin su tan shiga ban ɗaki tayi alwala tayi tayi sallah ta jima tana addu’a kana tan buɗe Alkur’ani ta jima tana karatu kana tan liƙe tan tada Abdul tilawa sun ka fara tare dashi tun da fatiha har zuwa naba’i kana tace dashi yaje yayi wanka ya ɗauko littafin sa na boko ya duba kan lokaci yayi ka karya
Tashi tayi taje tan tarar da Mom na karatun Alkur’ani koma wa kicin tayi thé tan fara shirya wa kana tan nemi abun da zai yi gaggawar dafuwa tan gama tan jera su kasa. Dan a tunanin ta jerawa saman dinner table ɓata lokaci ne kuma sun saba da kowa yasa hannun sa aci tana gamawa tan yuce wayar ta tan ɗauka ɗan shafa ta tayi kana tan ɗora a kunne kira biyu tayi ba’a ɗaga ba ban ɗaki tan shiga jim kaɗan tan fito kallon Abdul tayi jakar sa yan ɗauka yan fice daga ɗakin tare da rufo ɗakin ……. (Hatarar ku iyaye ƙanne yaye ku rika cire kaya ko kusa ka kaya gaban yara kuyi tunanin yara ne basu san komai ba to ku kiyaye. Allah ya shirya muna yara yasa ma rayuwar su albarka )
Yana fita kai tsaye ɗakin Mom yan buga amsa masa tayi yana shiga yaga ita ma ta fito daga ban ɗaki bai jira tayi magana ba yan juya yan liƙe kofa murmushi tayi a ranta tace ” Alhamdulillah Allah ya ƙara shirya muna su ”
Basu wani ɗauki lokaci ba sai gasu sun fito Mom ce tan ɗan riga ta fitowa kusan shigar da sun kayi ɗaya doguwar riga ce fara da mayafi ruwan toka Abdul ne yan tashi da saurin sa yan rungume Mom yana mata an tashi lafya da turancin yake mata magana dariya tayi tace
” To yau har da sauya halshe ?”
Murmushi yayi bai ce komai ba . Hajara kallon ta tayi tace
” Mom an tashi lafiya ?”
” Lafiya lau Mamana ya kike kin tashi lafya ?”
Amsawa tayi cikin sakin fuska nan sun ka zauna dan su karya wayar Hajara ce tayi ƙara ɗauka tayi tare da faɗin ” kiyi ƙoƙari ki shirya na gama gar na zo nasa mu biki shirya ba ”
Dariya daga can ɓangaren an kayi sai kuma naji tace
” To ko gaisawa mayi ko ?”
” Keda nake kiran ki biki ɗaga ba ?”
” Ehh ina kicin ne , ki tafi kawai sai mun haɗu makarantar Mama zata aje ni ”
Bata ce komai ba tan katse wayar kallon ta Mom tayi tace
” In kun sauko ki biyo office ɗin na in muyi sallar juma’a sai mu zo gida ”
” Ok Mom Kenan kar na tafi da mota ta ?”
” Ehh ki bar ta kawai sai na ajeku in kun sauko sai kije ki ɗauko Abdul ku yuce ma’aikatar mu ”
To shike nan ……
Yana kwance Momy ce a tsaye gefen sa tana faɗi yan zu Umar tun barcin jiya baka tashi ba kana kwance balle kayi tunani sallah ”