WATA RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

” To ke ba sai ki sauya saba ?”

” Kai Hjyata irin masu kuɗin nan kana cewa wani abu zasu ce ka tattara ka bar gida dan gannin suke suna da kuɗi suna iya auro wacce tan fika kin ga ba’a yi komai ba an zo a zauna zama na din din kuma ka zo asamu akasi ”

” Allah ya rufa muna asirri ya zaɓa muna mafi alkhairi ”

Amin sun ka amsa kowa yan shiga motar sa kai tsaye gidan Mom sun ka yuce suna zuwa ba’a wani ɗauki lokaci ba anka kira sallar asham suna gama sallah ne Hajara tan zubo abinci cikin ƙaton faranti kowa yasa hannun sa sun kusa gama ci ne sun kaji sallama kallon juna sun kayi alamar tambaya waye yan zu Mom ce ta tashi da kanta taje taga waye tana fitowa taga yan samari biyu gaban ta ne yayi mumunar faɗuwa ɗaurewa tayi ta zo kusa dasu ta ce
” Lafiya ?”
Ɗan sosa kai Umar yayi ɗan Hajiya ne yace
” Dama mun zo wajan su ne ”

Mom da ɗan mamakin ta tan juya baya tana kale kale tace
” Wajan suwa fa ? Bangane ba ? Wasu sun ka shigo nan da kuke neman su ?”

Hajiya Aisha ganin ta jima bata zo yasa tace bari naje na duba naga lafiya . Tana fituwa tan hangesu ƙarasowa tayi tana faɗin
” Hajiyata lafiya ? “
Kallon ta Mom tayi tace
” Lafiya lau wayan nan ne wai sun zo wajan su shine nake tambayar suwa ? kuma sun yi shiru ”

Murmushi Hajiya Aisha tayi tan mata raɗa a kunne tace
” Keda kike da yan mata har kin tsaya kina wata doguwar magana ? Haba Hajiyata ”
Tana gama faɗa tan juya tan kallesu tace
” Ok ga waje can ku zauna suna zuwa ”
Mom zata yi magana Hajiya Aisha tan jata sun ka yuce ciki suna shiga Hajiya aisha ce tace
” To kune kun kayi baƙi ”
Hajara ce cikin sauri tan ɗago kai ta kalle su tace
” Mama baƙi kuma ? Ni ko dai sister ?”
Ɓata fuska Hajiya aisha tayi tace
” Kun ga kar ku wani ɓata ma mutane lokaci in ma wace ce in kun fita zaku bawa kan ku amsa ba shi kenan ba kun tsaya gaba kuna saka mutane da tambayoyin banza ”

Hajara ce ta kalli Zee tace
” muje ko ?”
Tashi tayi sun ka fita suna fita Hajiya aisha ta kalli Mom tace
” Lafiya dai ko ?”
” Lafiya lau wlhi gaba na keta faɗuwa tun da na kalli yaran can ina son na tunu da wani abu na kasa ”
Kama hannuwan ta biyu tayi tace
” Kiyi addu’a yaran da biki saniba kin ga sharrin sheɗan ne kawai gar ki saka wani abu a ranki ”
” Ok shike nan na gode bari ma na ɗauko aikin da oga ya bani kin taya ni ko kaɗan ne “

Ok tace tare da ɗaukar wayar ta tana dan danawa ita kuma Mom ɗaukar kii ɗin motar ta tayi tan fita waje ta ɗauko jakar wajan aikin ta tana fita taji Zee tana faɗin
” Me ya kawo ku gidan mu kun zo ma nan ku ci muna mutun ci ? To wlhi sai kun fita tun da ba gidan uban ku bane ” jin muryar sai sama take ƙaruwa yasa tan nufi in da suke dai dai lokacin da Umar ya rungume Zee yana ƙoƙarin saka bakin sa cikin nata cikin ɗaga murya Mom tace
” Kai kai lafiya ?”
Umar wani dogon tsaki yaja bai ce komai ba

Mom sake cewa tayi
” Lafiya nace nake jiyu hayaniya ? ”
Ɗan Hajiya ne yace
” ammm Hajiya hirar masoya ce shiyasa….”

Bai ƙarasa ba Zee tace
” Mom wlhi ƙarya ne sune wanda ranar muke cewa sun tare mu harda bara zana to sune fa ban san yan da ankayi sun ka gano gidan ba ”

Mom kallon su tayi tace
” To ku bayin Allah sun nuna basa so to mine ne abun takura ? Kayi hakuri ita soyaya ba’a yin ta da garaje ”

Wani kallo ne yan ma Mom kana yace
” Uhummm ni kuma dun yan da naso abu haka abun zai soni ya so ko bai soba kiba yaran ki ma shawara dan gar laifin su yazo ya shafe ki dan Babana in ya ɗauki mataki har ke abun zai shafe ki ki kula ki kiyaye”

MASHA ALLAHU LAKHUWATI ILLAH BILLAH
[9/5, 11:28 PM] ❤️❤️ ???????????????????????? ????????: ⛱️⛱️⛱️ WATA RAYUWA⛱️⛱️⛱️

2️⃣3️⃣. Ina godiya sosai da addu’oin ku

Wani kallo Mom tayi masa bata ce dashi komai ba tan koma ciki wayar ta tan ɗauka tare da ɗan shan shafata a kunne ta ɗora ta can kuma tace
” Wlk slm ya kk ? Yawwa nace kana gida ko huta ? ”
Shiru tayi can kuma tace
” Ok ina son ganin ka ne ka zo yan zu ka koma ”

Tana gama faɗar haka ta juya tan koma bakin motar ta tan ɗauko abun da zata ɗauka . Dai dai da lokacin da Zee taja hannun Hajara sun yuce ciki wani ne yan shigo da sallamar sa kallon sa tayi kana ta amsa ɗauko abun tayi daga motar kana ta rufe juyo wa tayi ta kalle sa tace
” Ina son nasan wayan can yara suwaye waye uban su “
Bin inda tan nuna masa yayi da kallon dai dai lokacin da su kuma suna nufo ƙofar fita dai dai gaban su yan tsaya wayar sa yan ɗauka yan haska su kana yan tambe sunayen su daga farko ƙin faɗa su kayi sai da yan nuna musu fuskar maza kana sun ka faɗa kauce musu yayi kana sun ka yuce kallon Mom yayi yace
” Nasan su sosai ”

” Ok mu shiga ciki ”

Suna shiga Hajiya aisha na ganin sa tayi murmushi tace
” To su yan laɓai ba’a ganin ku sai tare da masu laifi ”

Murmushi yayi yace
” To kenan Hjya na cikin masu laifi ko ?”

Dariya sun kayi su duka ban da Mom kana ta ce
” Rufa min asirri ni na’isa nace haka ba haka nake nufi ba ”

Mom nuna masa waje tayi alamar ya zauna

Kallon su Hajara tayi bata kai ga magana ba Hajara sun ka tashi sun ka bar wajan Abdul ne yan ɗan sun kuya yace
” Oncle ina kayan soja ?”
” sun je koyo gaisuwa ”

Murmushi Abdul yayi yan sun kuya yan gaida shi kana yan bi bayan su Hajara da gudu . Kallon sa Mom tayi tace
” Wane yaro ne wancan ?”
Nunfasawa yayi yace
” Nasan sa shekaran jiya ma wani dattijo ya kai ƙarar sa na yama yar sa fyaɗe amma ba abun da an kayi ”

” To waye uwan sa ?”
”Mahaifin sa cikakken ɗan kasuwa ne yana da dalla ansha kawo ƙarar yaron amma da yake mahaifinsa yana da abun hannu ba abun da yayi dan ba’afi wata biyu ba ma da yan bige wasu yara uku sun mutu har lahira ana kaisa gidan maza ko kwana uku bai yiba anka fido shi baban sa yan biya masa kuɗi yan bar kasar sai da ƙura tan lafa yan dawo yana dawowa ma yan shiga wani gidan kara da mota yan murje wata amarya da ciki daga ita har mijin ta to da yake matar tasan wasu asama sai da yafi wata a gidan maza kana an kayi Shari’a wajan Shari’a ma anka nuna ai bai da hankali shiyasa yana da taɓin hankali to ta haka dai anka fitar da shi . Ana fitar dashi yan uwan matar ko sun ka hana sa zama shine yan fita waje bai fi kwana goma ba da dawowa kuma an ka ƙarar sa na yayi wa wata yarinya fyaɗe ”

Hajiya Aisha ce tace
” Wane yaro ne kuke zan ce wai ?”

Kallon ta Mom tayi tace
” Wanda sun ka zo ɗazu ”
Juyawa tayi ta kallesa taci gaba da cewa
” yan zu har yanzu ƙasar nan haka take tallaka bai da gata Uhummm amma ni in ya zo nan in rashin Kunyar sa zai min zai san uba ma da uban sa ”

Gyara zama yayi yace
” Rashin kunya yayi miki ?”
Kusan a tare sun ka furta shi da Hajiya Aisha
” uhumm wai tarar da shi yana rungume da Zee ina masa magana ya tsaya yana cewa shi in yaso abo ko ta halin yaya ne sai ya samu dan ban san waye uban sa . Amma ina son kasa min yaran ka su ma yaran nan ido dan Allah ”

” Insha Allah Hjya anyi an gama ”

Suna fita ɗan Hajiya kallon sa yayi yace
” Baka ganin ka hakura da yaran dan da alama akwai matsala fa ”

Kallon sa Umar yayi yace
” Har ka manta waye ni waye ubana ai basu ne na farko ba kuma ma anyi kisa ba abun da yan faru banle kuma fyaɗe ? Tunda nagani ina so wlhi sai na lasa zumar su yan san da in sun Kama ni ma in na jima ne nayi kwana goma kuma mahaifina kaga akwai dala suma ana iya basu wani abu mai tsoka kawai su manta ”
” Humm wanan ban ga alama ba gaskiya dan daga ganin matar nan tayi zafi sosai ba wasa a fuskar ta ”
Tsaki Umar yaja yace ” jamuna mota muje kaji ”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Leave a Reply

Back to top button