WATA RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

✍????. Rashida yar tahoua (tawa ) mutan nijar ????????

MASHA ALLAHU LAKHUWATI ILLAH BILLAH
[9/5, 11:28 PM] ❤️❤️ ???????????????????????? ????????: ⛱️⛱️⛱️ WATA RAYUWA⛱️⛱️⛱️

            2️⃣4️⃣

Yana tafiya Hajiya aisha ta kalleta tace
” Zan yuce sai gobe in muyi waya ”

Tashi tayi tana faɗin
” Insha Allah Allah ya kaimu goben lafya amin”

Ɗaga murya tayi dan kiran Zee tana zuwa tace
” Mu tafi ko ?”
A tare sun ka fita sake sallama sun kayi suna fita Mom ta kulle fallo sun ka koma liƙe kofar tayi zama sun kayi Mom ce tan kunna TV Abdul waya ya amsa yana wasa Hajara kwanta wa tayi saman ciyoyin Mom shafa kan ta tayi tace
” Wanan yaron a ina kun ka hadu dashi ?”

” Mom shine wanda Zee take baku labari ranar da ya tare mu ”

” Ok to ariƙa kula dai da samarin da ake mu’amala ”

” Mom wlhi ni ko saurayi bani dashi bama ruwa na da maza ”

” Shine ranar nan ganku tare da wasu samari dai dai shagon nan na RABILA’S CAKE and more (Insha Allah) harda riƙe hannu wani ”

Ƙara liƙe fuskar ta tayi tace
” Mom ƙanen wani ɗan makarantar mu ne fa ”

” To ba soyayya kuke ba ko in ce ba saurayin ki ne ba ?”

Murmushi tayi tace
” Wlhi Mom bani da ma saurayi da’ace sister ce amma ni ba ruwana ”

” Dun kyau ɗinan na Mamana Masha allah bata da saurayi kai bari na nema mata maganin farin jini ”

Dariya tayi take
” Mom ba wai ba mai cewa yana sona bane bana samu kawai dai ba ruwa na dasu ne ”

” sabida me to ba kya kula su ?”

” Mom wlhi samarin ne kuna fara hira sai kaga yace zai ma vidio call kana ɗagawa zaka ga yana nuna ma tsiraicin sa . Wani kuma sai yace sai ka tura masa jikin ka yaga ya kake to shiyasa gaskiya ba wasa wani damu na ”

Ɗan murmushi Mom tayi tace
” To ai ba duka suka zama ɗaya ba ”

” Mom kawai sai dai addu’ar Allah ya haɗaka da nagari Amin ”

” Amin ya Allah ”
( To iyaye Hattarar ku da kyarar yaran ku maza ko mata adun lokacin da kike da lokaci ki zauna da yaran ka ko kibasu rana ɗaya dun sati ki zauna dasu ta haka zaki gane akwai matsala ko babu , garki yarda yarki na miki hirar wani ko wata ki nuna ko in kula idan kin tsaya kin saurare ta zaki gano matsala in da shawarwari ki bata in da jan hankali ne cikin sanyi murya ba fushi da faɗa ba gobe in wani abu ya taso da kanta zata gaya miki ba tare da kin tambe ta ba . Allah ya shirya muna yaran mu yasa ma rayuwar su albarka).

Yau ya kama asabar tun da safe Hajara ta tashi ta gyara ko ina kana tashiga kicin ta gyara abun kari tana kusa kammalawa ta tayar da Abdul ya je yayi wanka . Ɗakin Mom ta shiga ta tarar da tana kwance saman darduma juya wa tayi ta rufe ƙoffar gyara komai tayi ƙasa kana ta yuce ɗakin ta dai dai da Abdul ya gama shiri yasa kayan sa fita yayi wayar ta ce tan fara ƙara ɗagawa tayi ba tare da tace komai ta ajiye wayar fita waje tayi ta buɗe ƙoffar Zee ce tashigo
” Kai kai ko shirya wa bikiyi ba ?”

” ki yuce ni shirina ba ke bace da kike ɗaukar lokaci bani minti biyar kiji ”

✍???? Rashida yar tahoua (tawa ) mutan nijar ????????????????

MASHA ALLAH
[9/5, 11:28 PM] ❤️❤️ ???????????????????????? ????????: ⛱️⛱️⛱️ WATA RAYUWA⛱️⛱️⛱️

               2️⃣5️⃣

Ciki suka yuce a fallo Zee ta zauna ita da Abdul Hajara shiga tayi ciki dai dai lokacin Mom ta fito Zee ce ta duƙa ta gaida ita , amsawa tayi tare da tambayar ta Maman ta amsa wa tayi da tana nan lafiya lau basu wani jima ba sai ga Hajara ta fito daga ɗakin ta doguwar riga ce tasa ka da ɓakin hijabi sai kuma dogayen takalma farare . Kallon ta sun kayi su duka Zee ce tace
” Waw masha Allahu LAKHUWATI ILLAH BILLAH gaskiya kin yi kyau Hajiya Fauzi Uwa ga Amatullah ta iya ɗin ki fa gaskiya nima can zan kai nawa idan na tashi ”
Murmushi sun kayi sun kuyawa tayi ta gaida Mom amsawa tayi tare da cewa
” Ba’a manta da azkar ɗin safe ba dai ko ? Dan in ba’a sallah wani lokaci manta wa kake ma da zama saman darduma ”

” Nayi sai da nayi ne ma na shiga aikin gida ”

” Masha allah haka ake so Allah ya muku albarka ”
Kusan tare sun ka amsa da Amin

Kii ɗin motar ta tan miƙawa Zee tace
” To muje ko ?” Mom ce tace
” To baza ku tsaya ku karya ba ?”

” Mom zamu makara in mun tsaya wani kari ”
Cewar Zee

” Ok to ku daure ku hada shayi mai kawri kusha yafi ku fita ba komai a ciki ”

Kusan a tare sun ka zauna ita da Zee sun ka haɗa shayi sauri sauri suke su gama Hajara ce tace
” Mom baza ku karya ba ?”

” kusha ban mayi wanka ba idan na gama zamu karya da ɗan babyna ”
Tan ƙarasa maganar da shafa kan Abdul murmushi yayi yace
” Mom waya nayi..”

Bai ƙarasa ba Hajara tace
” Mom ku daina yawan bashi waya yana game dan ya na ɓata gani lokaci zuwa lokaci ariƙa bashi ”

Murmushi Mom tayi tace
” nasani ganin bai da abokin hira shiyasa na ke bashi ”

” To Mom dan kawai bai da abokin hira sai ku bashi yaɓata ganin idon sa ? Mom ”

Gyaɗa kai Mom tayi tace
” ku ɗan jirani ina zuwa ”
Bata jira me zasu ce ba tayi gaba bata jima ba tan dawo dai dai da suma sun gama Zee ta ɗauki kofuna ta kai kicin . Tana fitowa Mom ce ta miƙa mata Zee ƙuɗi tace
” Ga wanan kema kin ƙara ki saye kayen kwaliya ”

Amsa tayi tana godiya tana miƙa mata tace
” Abdul ka bisu in sun fita ka liƙe kofa ”

Kallon Hajara tayi tace
” Kina ganin abun alkhairi baki taya ni murna ?”

” To mee Mom ce fa bata da kuɗi ne da yafi wanan , kuma ma wai yau ne kin ka fara samun kyautar Mom ?”

Murmushi tayi tace
” Kin san Allah ina da buƙatar kuɗi kin ga ranar ne Mama tabani wlhi yan zu ko kashe ni zakiyi ban faɗa miki suna ina ko kuma ga in da nasa su shiyasa ma ban cika ɗaukar mota na ba sabida bani da kuɗi kuma in nace bani da ƙudi kin ga ba daɗi ”

” kin ga in kin ida waƙar ki ki yuce mu tafi kinji ”

” Ohh waƙa ce nake Ok na gode ajiye min su to har mu dawo ”

Amsawa tayi sai da tayi tafiyar biyu da uku ta juyu tace
” kan na’aje kije ki fida motar kin tsaya jira na ? ”

Jakar ta ta ɗauka ta fita bata wani jima ba ta fito ko da taje tattarar da ta fida mota kai tsaye tashiga tare da ɗaga ma Abdul hannu tafe suke suna hira basu wani jima sosai ba sun ka isa makaranta suna zuwa sun ka aje motar in da aka tana da dan ajiye motoci suna zuwa suka ga ba ɗalibai sosai a aji wayan da an da kwai ma sai ƙorafi suke na an katse musu harakokin su sai wasu na cewa da yan zu suna barci kawai ya takura sai sun zo haka suke ta surutun su sai gashi kowa gyara zaman sa yayi ya natsu

Tun da safe da ya tashi kiran ɗan Hajiya yayi yace
” Kasa ido sosai kaga ko zasu fito ”

Yana gama faɗa ya katse wayar ban ɗaki ya shiga yayi wanka ƙana nan kaya yasa ka na sport fitowa yayi ya zuba masa da miyar kai yana ci ne wayar sa ta fara ƙara ɗagawa yayi bai kai da magana ba yaji ance
” gasu sun fito da’alamu makaranta zasu je kayi sauri ka fito mubi bayan su kaga ni ba abin hawa ne dani ba ”

Ƙatse wayar yayi yaci abun da yaci yatashi da sauri motar sa ya ɗauka gudu yake sosai wani waje ya zo ɗan Hajiya ya shigo motar sun ka tafi .

✍???? Rashida yar tahoua (tawa) mutan nijar ????????

MASHA ALLAHU LAKHUWATI ILLAH BILLAH
[9/5, 11:28 PM] ❤️❤️ ???????????????????????? ????????: ⛱️⛱️⛱️ WATA RAYUWA ⛱️⛱️⛱️

                 2️⃣6️⃣

Ina godiya sosai da comments ɗin ku da addu’oin ku Allah yabar zumunci amin

Tsayawa sun kayi sai da sun ka shiga makarantar kana suma sun ka dan na kan motar su waje sun ka samu sun ka aje motar su murmushi Umar yayi ya kalli ɗan Hajiya yace
” Kana gani makarantar yau ba jama’a sosai makarantar kagani ?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Leave a Reply

Back to top button