WATA RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

”Amin ya Allahu zainab na gode”
Cewar Mom

Mom kallon ta tayi tace
” Mamana mota ɗaya zaki riƙe , wancan wani zan bawa ita wanda Abdu yan kawo yan zu ”

” To tan faɗa tare da zuwa kusa da motar ta buɗe ta ɗauko wasu kayan ta harda ledar da take tunani tana ciki bayan ta gama ɗaukar komai ta liƙe motar tan miƙawa Mom kiii ɗin . Zee ce tace
” Mom na ɗauke ta sai ayi kyauta da tawa ”

Murmushi Mom tayi tace
” Ok yata ga kii ɗin nan ”
Murmushi tayi tare da rungume ta tana godiya

Hjya Aisha murmushi tayi tare da gyaɗa kai

Nan ita ma tan ɗauki abun da zata ɗauka tan maida a sabuwar mota tan miƙawa Mom kiii ɗin motar ta

Kallon Hajara tayi tace
” Sai na zo ko ?”
” Ok to ki bar motar sai kice tare da mama in zamu na biya na ɗauke ki in mun dawo sai ki tafi da motar ki ko?”

” Ehh fa hakan ma yayi ”

Kallon su Mom tayi tace
” Ina zakuje ?”
Hajara kallon ta tayi tace
” Wajan wata ƙawar mu da mahaifiyar ta tasa mu baby”

” Ehhh wanan wanda anka ce sai an mata aiki an ciro yaron na tuna . Amma fa in anje gar a wani jima ”

” Insha Allah Mom dan naso muje yan zu to ana zafi yau kuma tana azumi shiyasa nace da tasha ruwa munyi sallah sai muje da mun gaida ta shike nan mun dawo ”
Cewar Zee

” To ko daima k…..”

Bata ƙarasa ba Hajiya Aisha tace
” Ni zan yuce sai anjiman ku”

” Ok to godiya nake sosai Hajiyata ”

Hjya Aisha bata ce da ita komai ba sai murmushi da tayi tare da ɗaga mata hannu .

Suna tsaye sai da sun ka fita sun ka liƙe kofa sun ka yuce ciki …..

Kiɗa kawai yake tashi a motar gudu yake sosai wani katafaren gida motar tan tsaya bai wani jima ba anka wangame kofa yana shiga bai kai inda anka tanadar dan aje motoci ba yan fito wani matashi ne ba laifi fari ne gajere marar jiki amma da kaga nesa kasan dalla ta zauna dan ko daga kayan jikin sa zaka gane dalla ta zauna duba da kuma gidan da yan shigo yana zuwa wani wawan mari yayi wa wanda yan buɗe masa kofa zai kai masa wani sai can yaji ance
” Wlhi in kasa ke marin sa sai nasa sa ya rama rashin Kunyar banza ina tsaye naji zuwan ka yan tashi ya buɗe ma . In ma jimawa yayi baka tambayar dadi sai ka zo kana wani marin sa wlhi kafita daga ido na”

Gunguni yafara

Sake cewa tayi
” To gama zagina kaji”
Ɗago kai ya kalleta yace
” Yi hakuri ”

Nima ɗaga kai nayi naga wace ce mai magana . Wata dattijuwa ce daga gani kasan hutu ya ratsa ta . Yana aje motar ita ma saukowa tayi yana shiga fallon ita ma tana shigowa . Wani kallo tan masa tace
” To koma kayi sallama ”
Fita yayi yayi sallama kin amsawa tayi sai da yayi sau uku kana ta amsa shigowa yayi , sai yanzu ne naga fallo masha Allah faɗin yanda yake ma ƙauyanci ne da haɗuwa ya haɗu
Nuna masa waje tayi tace
” Ka zauna ” tan nuna masa da yatsa kujera mai kallon sa tan zauna
” Umar wai dan Allah yaushe zaka sauya hali kai kullun baza ka canja ba ? Baka tuna mutuwa ? ”

Wayar sa ce tan fara kuka ɗagawa yayi tare da ihu yana faɗin
” Kaii dan Hajiya kana gari ?”
Jim kaɗan kuma sai yace
” Ai garka damu ”
Yana gama faɗar haka yan tashi kallon sa tayi tace
” Aww ga karya na haushi ko ? Ina ma magana shine zaka ɗaga waya kuma kana gamawa zaka tashi katafi kabar karya tayi ta haushi har ta gaji ”

Tsayawa yayi yana yarɓa hannuwa yace
” Kai kai kai Momy Gaskiya wlhi kun cika magana kullun magana kullun cikin magana kuke . Shiyasa wlhi nafi son daddy tunda shi koba komai yana gane rayuwa …..”

Zai sake magana koda yan juyo bata nan aransa cewa yayi ko ina yan yi ohooo ita tasani

MASHA ALLAHU LAKHUWATI ILLAH BILLAH
[9/5, 11:28 PM] ❤️❤️ ???????????????????????? ????????: ⛱️⛱️⛱️ WATA RAYUWA⛱️⛱️⛱️

1️⃣0️⃣. Rubuta wa Rashida yar tahoua ( tawa) mutan nijar

Wanda yake da wasu shawarwari ko gyare-gyare ko shawar wari ƙofa abuɗe take ina maraba da kowaye

Godiya da jinjina ta musamman dama su bibiyar wanan latafi Allah ya bar zumunci da ƙauna

” Oyoyo oyoyo ya kake ka zo lafiya ?”

” Eh Mom lafiya lau ”
Hajara ce tan shigo ita da zee da sallamar su gaida su sun kayi Hajara ƙarar ɓar tsintsiyar a hannun Mom tayi tana cewa
” Mom ku bari zan share kuje ku kwanta ku huta kun sauko daga aiki ”

” Ah ! Ah kibar shi Mamana ki je ki huta keda kike azumi kije asabar in tashi da yuri sai ki share har harabar gidan tunda ba yara banle wajan yayi saurin dauɗa ”

Hajiya Aisha ce tan fito ɗauke da faranti tana zuwa tace
” La La La Laaa ! Yan makaranta har an sauko ? ”
Hajara ce tan sun kuya tan gaida ta tare dama barka da zuwa .

Zee tana ganin wanda tan fito daga madafa tan wani ɓata rai . Hajiya Aisha farantin tan aje tareda rungume zee tace
” yi hakuri nima tafiyar kwatsam ne tan zo min ayi hakuri yar maman ta, Ina Hafsat ne ?”

Turo baki tayi tace
” Kun biyu min da tsaraba ta ?”

Dariya Hjya Aisha tayi tace
” Tsarabar ki tana nan har muje gida ”
Dariya tayi tare da rungume ta tace
” An zo lafiya ?”
Dariya sun kayi su duka Mom tace
” To kenan dan sarabar ne ake wani ɓata rai yan zu kuma an zo da ita har kin saki rai , Yara yara Allah dai ya shirya ku yasa ma rayuwar ku albarka ya tsare muna ku ”
Kusan atare sun kace Amin .
Zama Zee Abdul ma yana zaune saman ciyoyin Mom sun kafara cin abinci
Kan su gama Hajara har ta gama sharar matsawa sun kayi tan share in da suke zaune . Tana gamawa tan zuba ruwa da garin sabulu kan kace mee har ta kammala sai ɗan goge goge da tace da Abdul ya goge table ya goge TV da kuma abun aza TV ɗin Hjya Aisha kallon su kawai take kasa hakura tayi tace
” Masha allah kalli fa har da Abdul ɗin ma ya iya goge gogen ”

Mom kallon ta tayi tace
” To ya za’a yi tun yana da shekara huɗu nake saka shi ɗan goge goge kin ga in ba Mamana daga ni sai shi ina gama sharar ruwa kawai zan haɗa masa tass zakiga ya goge ko ina ”

” Kai Hajiyata kina tsanan tawa diyawa gaskiya yan zu har shi da yake namiji ?”

” To Hajiyata ita Hajara aure zata yi daga ni sai shi zamu zama a gida kawai yana kallona ina yi sai dai ya wanke hannu yaci yasha ya tashi yatafi gantalin bin Fadodi Ah ! Ah ! Wlhi kin ga girki ma nan gaba zan fara koya mishi kin ga wanke wanke kwanoni wlhi zaki ce wata babba ce tayi in yayi ”

” Yanzu wanan yaron shiyasa yakasa ci gaba kullun wani ƙara mi yake komawa”

Dariya Mom tayi sai da tayi mai isar ta tace
” Wane aiki yake kalli mu lokacin da mun katashi in maza ne dake har daka suke miki fa su tuƙa miki tuwo da miyar kuka ko kuɓewa in kin ce zaki ce namiji yayi ? Ko kin manta na tuna miki ?”

” Ah ! Ah ! Kuma da kike zan cen ƙauye nan birni muke kuma a birnin ma acikin masu halin ma yake ”

” Hjyata kina bani mamaki wlhi , wai shi hallin nan da kike kira ba Allah ne da zai anshe abun sa babu jarrabawar Ubangiji ne ? Garki zamo kullun mai dogara da wani ko wata ko kice ko bayan raina akwai yan uwa masu kuɗi ƴaƴan ki bazasu ƙaskanta ba . Ki ɗura yaran ki akan koda yaushe wahala zata zo ma’ana akwai jarabta dora su akan sannin nema ko kina da ɗorasu akan tausayi ma’ana yau ko wani abu ne yan taso zasu tausaya miki su taimaka miki , in biki ɗora su akai ba ya kike ganin su nan gaba . Garki ɗauki tabi’ar wasu ki arawa kanki gar ki kalli rayuwar wasu kice ita zakiyi koyi da ita , Ah ah kalli abun da zai fidaki , kalli abinda zai gyara ki yau ko gobe shine kawai mafita ina fatan kin gane?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Leave a Reply

Back to top button