YAR SADAKA 1-END

YAR SADAKA Page 41 to 50 (The End)

Mashkur’ mashkur yaji Daddy ba Kiran sunansa,,be iya amsawa ba ya yinqura da kyar ya iya Tashi’ fitsari yakeji’ Amma baze iya tashiba zaune sabida koya ya motsa jikinsa jiyake kama ze fadi’ sosai yayi baki ya rame kallo daya zaka masa kagane Yana cikin tashin hankali mara misaltuwa.

Kallo daddy ya bisa dashi Yana cewa’ auta menene ko Dai jikin ne?

Girgiza kai mashkur yayi ya bude baki a hankali yace’ daddy fitsari nakeji’

A hankali daddy ya kama hannunsa ya Shiga dashi cikin toilet nan ya sakeshi Yana cewa’kayi fitsari nizan jiraka a waje daka Gama saika kirani kaji?

Juyawan daddy kenan mashkur ya fara qoqarin cire wandonta’ beyi aune ba yaji kafansa ya dau karkarwa nan yayi saurin riqe kan famfo Yana Kiran daddy.

Dasauri daddy ya shigo Yana tambayansa’ menene auta kayi fitsarin ko Yaya.

Cikin kuka mashkur yace daddy bazan iyaba’ Sai ya dafe saitin zuciyarsa Yana cewa’daddy zuciyana zata buga Dan Allah daddy ka taimakeni nijlah ta dawo gareni,, wallahi zaku iya rasani ya qare maganar Yana rungume daddy..

Hannu daddy yasa Yana shafa bayansa alamun rarrashin’ ganin yayi shiru ya Dena kukan yasa daddy tambayansa’

Auta kayi fitsarin?

Bazan iyaba Babu abinda Zan iya matuqar nijlah Bata dawo gareni’ ba,,meyasa zatayimin haka menayi Mata daddy Dan Allah ka gayamin?

Yawu me daci daddy ya hadiye batare dayayi Magana ba yafara qoqarin taimaka masa nan yayi fitsarin daddy ya bashi ruwa ya wanke tare suka fito mashkur Na jikin daddy Yana fidda numfashi dakyar dakyar..

Dakinsa daddy ya wuce dashi nan ya kwantar dashi kan dagonsa Yana cewa’

Mashkur kayi hakuri’ kana kallo nayi iyakar qoqarina Akan batan yarinyarnan Amma duk da haka ba’a gantaba,, inaso ka dauka batan nijlah daga Allah ne” yayi Hakan sabida ya jarraba imaninka’ Na tabbata idan kayi hakuri wata Rana nijlah zata dawo gareka..

A firgice mashkur ya Tashi zaune Yana cewa’

Daddy wata Rana fa kace’ yaushe Kenan? Yau ko gobe? Jibi ko gata?

Daddy bazan iya jurewa ba bansan a hannun da take ba,,ina tsoran kada a cutar da marainiyar Allah,,nasan duk a inda take hankalinta yafi nawa Tashi daddy ka taimakeni tinda ni ka hanani fita nemanta..

Hannunsa daddy ya riqe Yana cewa’ Amma Dai kana kallo Na zagaye gidajen radio da television Na Bada sanarwan cikiyanta kai har gidan jaridu Sai da nakai cikiya Amma kake Abu kama Wanda kaga Na rumgeme hannuna Na zuba ido banyi komai ba?

Dan Allah daddy karka bari mafarkina ya zama gaskiya’ ko kana so na rasata?

Wallahi daddy Zan iya Zama mara amfani da mamora na kare rayuwana cikin qunci da tashin hankali,, daddy Zan iya Zama mutum mutumi idan har Na rasata.

Kafin daddy yayi Magana mummy dake shigowa dakin tace’ 

Wallahi karyane auta,,zaka samu farin ciki irin wanda nake fata,,Nina sani’ wannan duk abinda kake Na Dan lokacine da an daura aurenka da Yasmeen shikenan zata mantar da kai wancan jakar.

To waini Dan Allah uban wa yace ta fita’ ina ita Da kanta ta fita tabar gidan?

Ita Bata damu da Hakan ba Sai kai zaka tadamana hankali.

Duba kaga yadda ka rame ka Zama kwaran gwal Sai hanci.

To wallahi ka kiyayeni’ kai Banda Allah yasa an rufe fita ko ina sabida wannan cuta da Allah yakawo ai da tini ka dade da barin qasar nan dan ni bazan iya zuba ido kana wannan abun kunyar ba,,yarinyar dako nonon kirki Babu a qirjinta kake wannan haukan..

Toka sani nijlah ta tafi tafiya ta har abada’ kaini ina fata nijlah ta hadu da….

Ya isa haka”’ mummy taji daddy ya daka Mata tsawan daya hanata qarasa abinda takesan fadi..

Cike da tashin hankali,, mashkur ya maida kallansa ga daddy Yana cewa’

Dan Allah daddy karka bari maganganun mummy su tabbata inaso ta dawo gareni wallahi idan maganarta ta Zama gaskiya Zan iya rayuwa cikin kunci da bakin ciki..

Sai ya maida kallansa gaa mummy Yana cewa’ mummy Dan Allah kidena mummy namiki biyayya a matsayinki Na mahaifiya! Yakamata ace kema kinso abinda nake so!

Ko kinaso maganganunki su Zama sanadin ajalina,,tashin hankali Na bakin ciki na,a qarshe na mutu ban haifamiki yaran da kikeso daga gareni ba?

Kasa jure sauraran maganganunsa mummy tayi ta juya da sauri ta fita a dakin tana mejin takaicin yadda autan nata yafada tarko da kogin soyayyar jinin mutanan datafi tsana a rayuwanta..

Tabbas idan Na tsaya Na cigaba da sauraran maganganinsa zeyi galaba akaina sabida bazan iya jure ganin tashin hankali autana ba,,dakinta ta shige ta fada kan bed tunanin ta inda zata bullowa al’amarin..

Tinda mummy ta fita mashkur ya rungume daddy Yana cewa’ daddy nima Zan tafi yawan Duniya tinda mummy Bata San abinda nakeso,,ko Allah ze hadani da nijlah a can,,Amma kafin nan daddy inaso a daura aurena da Yasmeen..

Shiru daddy yayi ya zuba masa ido harya Gama Magana.

Ganin daddy yayi shiru mashkur ya bude baki a hankali yace’

Dan girman Allah daddy kada kace ah ah ka barni nabi zabin zuciya ta..

Nannauyar ajiyar zuciya daddy ya safke kafin yace’ shikenan auta Na yadda za’a daura aurenka da Yasmeen sabida kaima ka samu me kula dakai tinda Naga itama kana santa.

Eh daddy inasanta da Yasmeen nafara soyayya inamata so irin wanda nakema nijlah sedai Hakan baze taba Mantar Dani Abar kaunata nijlah ba sedai ze ragemin radadi da zugin rashinta idan har ina tare da Yasmeen..

Amma inaso ka sani Babu inda zaka,,koda anyi aurenka sedai ka zauna anan damu sabida muma hankalinmu zefi kwanciya idan muna ganinka’ batin tafiya Duniya Kuma ka ajiyeshi a gefe Dan Babu inda zakaje..

Bude baki mashkur yayi da niyyan Magana daddy ya katseshi,,kaga banasan dogon bayani ka kwanta ka huta nizanje Naga mahaifin ita Yasmeen..

Kwanciya mashkur yayi ya rungume hannunsa Yana tinanin Yasmeen..

Be jima da kwanciyaba Nasir ya fadomasa’ waya ya dauka ya kirashi nan yake gayamasa tashin hankalin daya faru..

Sosai hankali Nasir ya Tashi Dan yafi kowa sanin halinda kaka da Malam ke ciki kai harma da mutanan kauyen garin kankan..

Ran Nasir a bace ya hau mashkur da fada ta inda yake Shiga Bata nan yake fita ba,,Yana cewa’ yanzu shikenan kajamin bala’i Dan wallahi bazasu taba Bari Nabar garin nan batare dasu ba..

Jikin mashkur a sanyaye yace’ nima ba haka naso ba,,Nasir dakaga halin Dana Shiga bazaka gayamin haka ba Amma bakomai haka Allah ya tsaramin..

Haka Dai Allah ya tsara mana cewar Nasir cikin fada.

Kayi hakuri Nasir insha Allahu za’a ganta’ to naji Amma ni haka Zan zauna nawa iyayen nasan ganina Babu dama?

Shiru mashkur yayi Yana tunani kafin yace yauwa Nasir kasan me zakayi?

Saika fada ni Kawai ka gayamin Dan wallahi kaina ya kulle.

To shikenan Kawai Kabi dare ka gudu idan yaso daga Baya Sai mu koma abasu hakuri Na tabbata lokacin nijlah ta dawo gareni..

What mashkur kana haukane,,sokake kayi sanadiyyar mutuwar kaka da Malam kaga nidai Kawai ka sake tunani.

Hmmm Nasir Kenan Hakan danayi shine kawai mafita ka gudo cikin dare Dan wallahi idan kaka taji batan nijlah zata iya hadiyen zuciya ta mutu kaga Kenan anyi ba ai ba..

Shiru Nasir yayi kafin yace to shikenan Bari yanzu Na fito tin kafin tsare ya tsala…

Sallama sukayi mashkur yayi murmushi Yana cewa’ Na gama da matsala guda…

Basu jima da Gama waya ba mummy ta shigo da plate shaqe da abinci’ kauda kai mashkur yayi Yana cewa’mummy ni a koshe nake..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button