YAR SADAKA 1-END

YAR SADAKA Page 41 to 50 (The End)

Dariya Abba yasa yana hamdala ga Allah dayasa nijlah ta gudu yasan koba komai mashkur dole ze hakura idan ya nemeta ya rasa tinda da Dai nijlah bakan gadone da itaba balle ayi tinanin zata iya dawo da kanta garesu’ to idan ma zata dawo meyasa zata gudu..

Zama yayi bakin gadon Yana cewa’ Kaji shashanci keda Zaki shigo kina rawa da kuyi saiki shigo cikin tashin hankali..

Dasauri Yasmeen ta Dago tana kallan Abba kafin tace’ Abba rawa fa kace,,koka manta mashkur Yana gadon asibiti?

Abba a gabana ya riqa Tari hadda jini Yana Kiran sunan wata bani ba,,abba nijlah yake kira,,wayyo Na Shiga uku ba..

Jin kukan yayi yawa yasa mama Tashi ta shigo dakin tana rarrashin Yasmeen Dan ita ki tambayan abinda ya faru Bata iyayi ba.

Sai da baccin wahala ya dauke Yasmeen mama da Abba suka fita yayin da mubeena ta zuba kawar Tata ido tana mamaki..

_________

Ke Maryam Dan ubanki jeki Kira Bala drive yazo ya kaini asibitin nan kinga auta shiru Basu dawo ba..

Wayyo ni hauwa naga ta kaina Na hadu da dangin tsiya zata kashemin yaro mummy ta fada cikin kuka tana goge majina.

Zumburo baki Maryam tayi tana cewa’hajiya nima banga Bala ba.

Dan ubanki kije dakin Musa Mai gadi nasan yanacan’ 

Ya Allah Kaba yarona lafiya ita Kuma wancan tsinan nan ka hadata da ‘yan mafiya su shanye jininta daganan su soye tsokan jikinta su cinye..

Zaro ido Maryam tayi tana cewa’kai hajiya musulmace fa kike Mata wannan addu’an.

Eh nayi kema zoki fita a gidanann kai gaba daya Na sallami ma aikata gidan kowa ya tafi gidan ubansa ‘ tinda kunajina Babu me taimakona gashi ni qafa Babu nakasa takawa..

Dan gudu Maryam ta fita a falon ta Sami Bala drive dake kofan falon Yana dariya’ 

Haduwa sukayi Suna ta shega dariya daga bisani Maryam tace kai bala ya isa haka,,nifa bansan abinda yasani wannan dariyan ba Dan gaskiya ina cikin jimamin rashin nijlah.

Addu’a sukayi Akan Allah ya bayyanata suka koma lambu Suna hutawa sabida gudun jarabar mummy.

Sosai nijlah taci abinci tana ci Mujaheed na Mata hira,, ahaka har suka Gama suka Tashi.

Kallan husna Mujaheed yayi Yana cewa’ aunty inaso zamu fita Na sama Mata kayan Sawa kinga yanzu ko kayan da zata chanza Babu.

Satar kallan daddy Ayman husna tayi tadan harari Mujaheed tana cewa’

Kai Dai kacika rawan kai ai Dai ka bari gobe tayi Sai Musan abinyi ko.

Sosa kai Mujaheed yayi Yana riqe da hannun nijlah yace’

Aunty Kenan kefa kincika sa’a ido.

Kallan daddyn Ayman yayi Yana cewa’ Yaya muje ko?

Kafin yayi Magana husna tace’ ah ah fa kanina,,Baka ga Bata da lafiya ka duba jikinta duk a sanyaye yake.

T

Murmushi Mujaheed yayi yana cewa shikenan a Na Bari sai goben.

Nan suka zauna ya Kalli nijlah Yana cewa’ 

Baby Zaki sha ice cream?

Duk da nijlah Bata San ko menene ice cream ba Hakan be hanata daga masa kai ba alamar zata sha’

Ok Tashi ki dauko mayafinki Sai muje Kisha ko..

Magana husna zatayi daddy Ayman ya katseta,

Dear Zafa mu Bata dake,haba mana ya kikeso nayi da Raina,,nasamu farin ciki kinasan hanani..

Girgiza kai husna tayi tana cewa’nifa ba wani Abu zance ba.

To me zakice? Daddyn Ayman ya tambaya fuska hade.

Cewa zanyi Allah ya kiyaye nima a kawomin nawa.

Dariya sukayi Mujaheed Yana cewa’ yauwa auntynmu ko kefa..

Nan ya kama hannun nijlah suka fita Yana cewa’ kinga bar mayafin kawai tinda Mota zamu Shiga basai kin sha wahala ba.

Shida da kansa ya bude mata motan yasata ciki ya zagaya Shima ya Shiga suka fara tafiya..

Langwabewa nijlah tayi tana……….

Comments & share.

*Momn sultan ce*✍✍✍

???????? *YAR SADAKA..????????*

*STORY & WRITING…*

              *BY*

*MOMN SULTAN.*

*DEDICATED TO…*

*MOMN AMATULLAH.*

*SPECIAL GIFT To…*

*ALL MY FAN’S…*

7⃣6⃣&7⃣7⃣

Narkemasa nijlah tayi tana zuba masa shagwaba..

Banda murmushi babu abinda mujaheed yake,,jin kansa yake gama wani sarki’ a yayinda zuciyarsa ke cike da dumbin farin ciki mara misaltuwa’ kallanta yake yana murmushi hannunsu sarqe Dana juna.

Duk da ba wani abu yakemata ba Amma duk da haka sedai yanayinsa na chanza take yafara jin wani irin yanayi Wanda be tabajin irinsa ba,, dasauri ya janye hannunsa a nata hakan dayayi yasa nijlah saurin kallansa tana turo Baki sabida ganin yadda lokaci guda yanayin fuskansa ya chanza..

Murmushi mujaheed yayi yana cewa’ sweety lafiya dai ko?

Qara turo Baki nijlah tayi tana dire diren qafa yayinda madaidai tan nonuwanta suka fara karkadawa suna tsikarin mujaheed..

Mujaheed be iya magana sai ma saurin lunshe idonsa yayi yana qara godiya ga Allah..

A hankali ya budesu ya safke kan nijlah Wanda zuwa yanzu ta kwantar da kanta jikin kujera..

Hannu mujaheed yasa yayi mata alamun tazo,,makale kafada nijlah tayi tana cewa’ uhmn uhmn.

Dariya yayi ya Hura mata iskan bakinshi yace’ wow sweety inasan wannan shagwaban naki’ idan munyi aure Zaki riqayimin irin ta ko???

Dam dam qirjin nijlah ya bada har saida mujaheed ya iya jiyo ssautin bugun zuciyarta.

Sai yanzu ta Tina da mashkur sedai data Tina da dukan dayayi mata sai taji batasan qara tinashi’ wasu hawaye masu zafine suka zubo mata,,tayi saurin sa hannu ta goge tana qaqalo murmushi..

Tsare ta da ido mujaheed yayi yana cewa sweey lafiya dai ko,,meke damunki ko har yanzu jikin ne?

Girgiza masa Kai tayi tana cewa’ ah ah nifa bacci nakeji!

Bacci kuma a wannan lokaci?

Nijlah bata iya bashi amsa ba sai daga masa Kai tayi tana qara sakin jikinta yayinda duk take jinta babu dadi daurewa kawai take..

To shikenan bari muje nasai miki,,Kinga daganan sai mu wuce gida basai na kaiki dayan gurin ba ko…

Kamar zatayi kuka ta bude bakinta a hankali tana cewa’ Nina fasa Sha kaina ciwo yake ka maidani gida kaji..

Dan zaro ido mujaheed yayi ya maimaita maganan,,gida kuma sweety’ meyasa zakice haka bayan kina kallan yadda aunty tayi kafin ta bani ke.

Ko dai nine bakisan zuwa Dani sainayi parking anan na tari napep ya kaini,, Kinga saina siyomiki ki Sha.

Idonta fal da hawaye tace’ ni ah ah nakoshi,,Dan Allah ka mayar Dani gida bazan iya zuwa ba..

Sosai mujaheed ya cika da mamaki sedai yakasa gano dalilin dayasa nijlah tafasa zuwa Shan ice cream’ 

Bece komai ba ya juya akalar motan suka dauka hanyar dawowa gida..

Tafe suke tana goge hawaye yayinda mujaheed ya rasa ta inda zefara rarraahinta tinda dai Shiba iya soyayya yayi ba bare yasan ta inda ze fara.

Shiru yayi yana tinani yayinda yakejin zuciyarsa na qunu kamar zata tarwatse sabida tsananin bacin Rai da takaicin hawayen da nijlah ke zubarwa gashi yayi magana yayi magana taqi amsashi..

Hannu yasa ya janyota jikinshi yana shafa bayanta tare da yimata magana a hankali’

Nijlah ta! Meke damunki?

Lafiya muka fito Amma cikin mintuna qalilan duk kin dagula Mana lissafi?

Shiru tayi Bata bashi amsa ba ganin haka yasa mujaheed cigaba da magana’wani Abu namiki? Girgiza Kai nijlah ta qarayi haka yayita jera mata tambayoyi tana girgiza Kai,, a qarshe yace’ to ko gida kikesan komawa..

A firgice nijlah ta dago tana goge hawayen fuskanta’ da kyar ta iya bude Baki tace’ ah ah wallahi banasan komawa Zan zauna daku sedai inaso kuyimin Abu guda daze mantar Dani tsohuwar rayuwar danayi a baya..

Kallanta mujaheed yake cike da matsananciyar soyayyarta yace’

Nayi Miki alqawarin duk abinda kikeso shi zakiyi indai be saba koyarwa ta addinin musulumci ba…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button