YAR SADAKA 1-END

YAR SADAKA Page 41 to 50 (The End)

Wani irin dadi nijlah taji yana ratsata a hankali ta maida kallanta garesa tana cewa’ kayi parking anan wata magana nakeso zamuyi idan ba damuwa’.

Ba musu mujaheed ya nemi guri yayi parking yana kallanta’ sai kuma yasa hannu biyu ya kamo nata hannu ya hada da nashi yana shafawa a hankali a hankali.

Shirune ya ratsa cikin motan kafin mujaheed yace’ 

Nijlah inajinki’ ki fadi duk wani abu da kikeso ni kuma nayi Miki alqawarin Baki dukkan farin ciki..

Lumshe ido nijlah tayi ta kuma budesu akan mujaheed tana cewa’

So nake kagayamin da wani irin Abu masu kudi suke taqama?

Shiru mujaheed yayi yana kallanta’ 

Nijlah ta dauke kanta tana cewa’,ka Tina ka riqa kayi alqawari.

Nannauyan ajiyar zuciya mujaheed ya safke,, kafin yace’

Nijlah babu abinda yafi ilimi dadi a rayuwa’ hatta kudi nijlah a bagan ilimi yake,,idan ka mallaki kudi baka da ilimi tofa wannan ilimin ya tashi a banza Dan haka ilimi shine tushen rayuwar talaka dame kudi..

Murmushi nijlah tayi tana kallan mujaheed yayinda idonta be Dena zubda hawaye ba tace’

Naji dadin haka Amma wanne irin ilimi kake magana?

Shiru mujaheed yayi yana kallanta’ nijlah, ahankali ya dauke idonsa daga kanta yana cigaba da magana’

Babu ilimin dayafi ilimi na addina sedai ayanzu idan baka hada da ilimin zamani ko ince na nasara ba to zaka zama kama Wanda be taba shiga ajiye ba’ 

Zaro ido nijlah tayi tana cewa’ kana dubin akwai wani karatu dayafi na alqur’ni.

Babu nijlah sedai a yanzu dole saika hada Dana boka ta hakane kadai zaka Samu cigaba da samun kudi masu yawa’ Wanda samun irin wadannan mutanan a wannan zamani yake wahala shiyasa kikeganin masu kudi dayawa basu tausan talaka balle su taimaka masa.

Meyasa suke kyaman talaka?

Nijlah ta qara jefa masa wannan tambaya..

Murmushi mujaheed yayi yace’

Sabida dayawa masu wulaqanta talaka Kona qasa dasu ko azzaliman shigabannne wallahi kinji na rantse basu da ilimin addini boka kawai suka sa a gaba shiyasa tin a farko kikaji nace saika hada duka biyu kafin ka zama abinda kike tinani..

Dariya nijlah tayi tana tafa hannu lokaci guda ta hade fuska ta kuma janye hannunta a nasa tana cewa’

Indai ko hakane ni nijlah kawu ‘yar gidan kaka da malam sai na hada ilimi guda biyu sabida na nuna wulaqantantun mutane cewa Nima mutum ce’ wallahi ko banyi kudi ba sainayi ilimin da Zan taimaki al’ umma dashi..

Tana gama fada ta safke qafanta kasa ta durgusa tana hawaye tace’

Dan Allah mujaheed ka cikamin burina ka taimaka kasani makaranta,,inaso nayi karatu me zurfi ta yadda Zan banbanta da ‘ya ‘yan masu kudi irin Yasmeen..

A fili mujaheed ya sauke ajiyar zuciya tare da Kiran sunan nijlah,, ahankali nijlah ta amsa muryanta na rawa tana tsoran kada yace ah ah.

Na’am’. Mujaheed ya cigaba,, nijlah banqi ta taki ba sedai a gaskiya ni banaso matata tayi karatu me zurfi Wanda zesa tayi wayewar dazan kasa sarrafata yadda nakeso…

Haba yayan ayman’ kada ka manta ka banbance min tsakanin ilimin Boko zallah da Wanda aka hadashi Dana addini’ mujaheed duk da akwai wata a qasa,,hakan baze hanani daukan alqawarin auren kaba sabida kasoni a lokacin Dana rasa masoya,,

Yini daya jal yasa nagane Kai masoyine na gaskiya’

Dole nayima halacci sabida baka nuna kyama da hantara gareni ba,, saita saki kuka tana cewa’ Kai da aunty husna bansan Wanda yafi Sona ba..

Janyota jikinsa yayi yana kallan pink lips dinta har besan lokacin daya Kai mata kiss a kuma ba yana cewa’

Inji waye’ karma ki soma hadawa sabida ni mujaheed nafi kowa sanki da kaunarki,, fatana daya shine ki rayu Dani…

Runtse ido nijlah tayi tana jin yadda sautin qaran kiss din daya mata na ratsa dukkan ilahirin jikita har tafara tinawa da ranar da mashkur yafara kissing dinta gami da koyamata salon sa Mai wuyar fassara,, dasauri ta dauke tinanin tana cewa’mungama magana ko..

Dage mata gira yayi yace’ Nima ke nake sauraro.

Shagwabe masa tayi tana cewa’ bayan haryanzu bakace ka amince zaka sani makarantaba’

Lakuce mata hanci yayi yace’ indai nine na amince ayi karatu sedai fa Nima zaa bani nawa haqqin da an fara karatu Dan gaskiya bazan iya hakuri kina karatu ba aurena akanki ba..

Dariya nijlah tayi tace’ to indai aurene yanzu ma ai dashi Zan fara karatun ko?’ dariyar jin dadi mujaheed yayi ya daka tsalle kama qaramin yaro yana cewa’ yeeeeee Nima nakusa angon cewa yafada tana tada motan..

Tafiya suke suna Hira ahaka har suka qarasa gidan,,a tare suka shiga cikin falon nijlah na rabe jikin mujaheed yana tattalinta da alkintata..

Murmushi husna tayi tana kallan hannunsu sai kuma ta tabe Baki tana cewa’

Kanina badai kafara nunamin banbanci ba,, yanzu sabida Allah sai kuje Shan ice cream ku dawo haka bako leda..

Murmushi mujaheed yayi yana sosa Kai ya zaunar da nijlah kusa da aunty husna shi kuma ya dawo kujeran dake kusa da daddyn Ayman ya zauna yana cewa’ 

Aunty ba laifina bane’ kinganta nan itane tace’ bata yadda abama kowa ba!

Zaro ido nijlah tayi aunty husna tayi saurin magana..

Murmushi husna tayi ta Dora hannunta kan nijlah tana cewa’ 

Kanwata Wai hakane?

Boye fuska nijlah tayi takasa magana ..

Mujaheed yace’ to kingani’ ba,,hakan kadai ya Isa ya tabbatar Miki,,sabida tace’ na masoyane..

Kai kanina kadafa ka hada fada daddyn Ayman ya fada yana cigaba da latsa computer dake gabansa.

Da gudu nijlah ta tashi ta shiga daki tana dariya yayinda takejin tafi kowa sa’a Dan yanzu farin cikin datake ciki baza taba misaltuwa ba,,kan Dan qaramin gadonta ta fada ta rungume duka hannunta a qirji….

Dariya suka sa ganin yadda take gudu hips dinta sai juyi suke…

Kallan husna mujaheed yayi yace’ Kai aunty yana ga kina kallemin mata yafada cikin hade fuska..

Eh lallaima yaran nan daddyn Ayman kaji abinda yake fada ko?

Kunfi kusa indai keda mujaheed ne,,nasan duk Wanda ya shiga shizeji kunya..

Kukan shagwaba husna ta saki tana cewa’ Amma dai kana kallo ya shiganwa budurwanshi,,shine ni zakaqi shigan min ko..

Shikenan shikenan ya Isa haka indai ice cream ne ki shirya muma yanzu zamu fita saiki Sha ko..

Murna husna tayi tana cewa’ to kagani dai,,dadin abin Nima inada miji..

Bazawar dariya mujaheed yayi yana cewa’ Kai aunty kin cika kishi to bari kiji..

Mu babu inda mukaje’ muna hanya nijlah ta rigime tace ita gaba daya ta fasa zuwa’

A tare husna da daddy Ayman suka ce sabida me?

Ajiyar zuciya mujaheed ya safke ya fara basu labarin yadda sukayi da nijlah’

Tin kafin ya gama husna tayi hamdala ga Allah sabida Dama ita burinta nijlah tayi karatu ta waye ta yadda ko sun maidata ga iyayenta.

Iyayen nata bazasuji haushi sosaima..

_______

Bangaren mashkur abin ba’a magana,,sedai duk da haka saida mashkur ya takura aka bashi sallama sabida yace maganinsa bana asibiti bane Dan haka a nemo masa nijlah a duk inda take ta hakane kadai hankali sa ze kwanta..

Kuyi hakuri da wannan,,yanzuma dakyar nasamu nayi,, nagode sosai da kaunarku gareni’ ina alfahari daku masoyana a duk inda kuke.

Comment & share

*MOMN SULTAN CE*✍✍✍

???????? *YAR SADAKA..????????*

*STORY & WRITING…*

              *BY*

*MOMN SULTAN.*

*DEDICATED TO…*

*MOMN AMATULLAH.*

*SPECIAL GIFT To…*

*???? HUSSY❣…*

7⃣8⃣&7⃣9⃣

Kwance yake kan doguwar kujera’ Banda juyi Babu abinda yake’ jiyake inama mutuwa zata daukeshi koya huta da abinda yakeji’ 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button