YAR SADAKA Page 41 to 50 (The End)

Zama mummy tayi tana rararshinsa Amma duk da haka mashkur yaqi amsa a dole mummy ta hakura ta fita a dakin tana buga tsaki..
Tana fita bacci ya dauke mashkur..
_______
Karfe 9 na dare Yasmeen ta farka fuskannan Tata ta kumbura tayi jajur da ita,, dasauri mubeena ta fara tambayanta tana cewa’
Kawata menene ki haryanzu baki dawo daidai ba.
Uhmn mubeena Kenan tayaya kike tinanin Zan iya dawowa cikin hayyacina alhalin kina gani wata banza kuchaka ‘yar kauye Wanda Bata da galihu tayi nasaran Shiga cikin gonata har tayi shuka a ciki.
To shine me?karki manta haryanzu mashkur nasanki menene abin damuwa?
Akwai mana ke Bari ingayamiki wallahi ko’ mutuwa nayi bazan taba kaunar mashkur yayi wani auren ba balle yanzu danake a raye..
Riqe baki mubeena tayi tana cewa’ to GA abinci nan saikici..
Bazan iya Ciba,, ki daukesa kawai..
Kai yasmeen kinada matsala idan maganar aurenkune anfa Gama Magana domin kuwa daddyn mashkur yazo har gida sunyi Magana da Abba akan maganar daurin aurenki gobe.
Bayan Sallah Sai ayi duk wani shagali da kike so.
Zaro ido Yasmeen tayi tana cewa’ ke mubeena banasan Karya?
dagaske fa cewar mubeena tana cewa’
Wallahi kina bacci akayi komai aka gama,,nidai fatana kada kice baki amince ba..
Murmushi Yasmeen tayi ta ce’ Na amince mubeena nima fatana daya nakasance tare da mashkur’ idan bana tare dashi hankalina baze taba kwanciya ba..
Dama Abu guda nakeso ayi chasu a raqashe a lokacin aurena’ yanzu Kuma an amince daga Baya za’ayi kinga shikenan Sai a daura auren kona samu damar mallake zuciyar baby” ya cire wancan shegiyar daga cikinta..
Dariya mubeena tayi tana cewa to yanzu saikici abinci muje ko gyaran gashi ayimiki da kunshi.
Tashi Yasmeen tayi ta dauka mayafinta tare da sa takalmi tana cewa’ Tashi muje Nina koshi..
Tashi mubeena tayi suka fita,,karfe 9 :20 suka isa wani katafaren saloon,, anan aka gyarawa Yasmeen gashi tare da kunshi irin Na amare’ gyaran be tsaya anan ba saida aka Mata dilka da Halawa,,idan Mai karatu be mantaba,, Abaya mun fadi irin magunguna Na gyara’ da Yasmeen ke amfani dasu tin daga lokacin da akasa aurensu har zuwa yanzu.
Dan haka Bata da wani matsala Na gyaran jiki daga ciki har waje lolxx..
Basu suka dawo gida ba Sai karfe 11 Na dare,,Suna zuwa mama zata fara fada Abba ya hanata nan itama tayi shiru sabida tafara jimamin rabuwanta da tilon diyar Tata..
__________
Kwance take a daki ta hada kai da gwiwa tana tinanin rayuwa’ Babu shakka mutane Kala Kala ne wasu Na da kirki wasu akasin haka’ dafe qirji tayi tana cewa’
Yanzu me nayi’shin nima Na Shiga cikin mutanan kwarai ko kuwa?
Lumshe ido tayi tana tinanin rayuwar datayi da mashkur’ murmushi Mai ciwo tayi data Tina lokacin da Yasmeen ta hau kanta tana duka iwa jaka agaban mashkur batare daya dauki wani mataki ba,,Sai Kumar ta Tina dukan daya Mata a daidai lokacin data barmasu gidansu ta fito neman inda zata hau Mota ta koma gurin kaka..
Kuka ta saki tana cewa’ kado Baka Sona Dan haka nima Na hakura dakai kaje can ka zauna da Yasmeen tinda itace zabin Raina.
Sai ta tsagaita da kukan tana cewa’ Anya ko Na kyauta’ idan Na Manta alkairin da kayimin Sai Kuma ta bude ido tana cewa’ tabbas mashkur ba kaunata kake ba kana Dai San zamana a kusa dakai kodan ka riqa matsani ta inda kakeso’ tinawa tayi da irin kukan da take masa idan Yana shafa qananun nononta kafin zuji wahala su Girma Dan yanzu qirjin nijlah cike yake da kayan yaqi lolxx..
Tana nan zaune Mujaheed ya shigo Yana cewa’ ke wai Haryanzu me kike da bazaki fito kici abinci ba?
Dasauri nijlah ta rufe Ido tana sauke numfashi a hankali’
Jikin gadon ya qaraso Yana cewa’ badai bacci kikayi ba?
Leqata yayi yaga idonta a rufe alaman bacci a tare take,,nan ya zauna yasa hannu Yana buga katifan tare da Kiran sunanta.
Sweety, sweety na ki tashi haka kafin yinwa ya illatamin ke’ shiru nijlah tayi taqi motsawa ganin haka yasa Mujaheed sauka Akan gadon ya bude fridge.
Ruwa me sanyi ya dauko Ya fara shafa Mata a fuska Yana Kiran sunan.
Dasauri ta riqe hannunsa tana dariya..
Sallamar husna ya hanata Magana ta safke qafanta a qasa tana cewa’ aunty sannu da zuwa.
Ran husna a bace ta amsa tana cewa’ muje daki nah”inasan ganinki’
Sum sum Mujaheed ya fita a dakin Yana turo baki ,,ranshi a mugun bace..
Mujaheed na fita’ husna tasama kofa key ta zuba nijlah ido..
Sosai nijlah Tasha jinin jikinta ta safke kanta qasa lokaci guda jikinta ya dauka karkarwa sabida tsoran aunty husna da taji ya ratsa dukkan jikinta..
Comments & share
*MOMN SULTAN CE*✍✍✍
???????? *YAR SADAKA..????????*
*STORY & WRITING…*
*BY*
*MOMN SULTAN.*
*DEDICATED TO…*
*MOMN AMATULLAH.*
*SPECIAL GIFT To…*
*ALL MY FAN’S…*
????????????????????????????????
*KARSHEN ‘YAR SADAKA BOOK 1….*
*COMING SOON*
*YAR SADAKA BOOK 2…*
*Bayan sallah in Allah ya aramana Rai da lafiya…*
8⃣0⃣…
Kallan Nijlah aunty husna takeyi da tsananin mamaki,, Bata damu da yadda jikin nijlah ke karkarwa ba ta Sami guri kusa da ita ta zauna’ cikin dauriya husna ta kama hannun nijlah duka biyu ta riqesu cikin nata,,ta Kuma kafeta da Ido tana kallanta.
A hankali nijlah ta Dago tana satar kallan husna take kwayar idonsu ta sarqe Dana juna’ dasauri nijlah ta dauke kanta tana zumburo baki gaba.
Murmushi husna tayi ta saki daya hannun nijlah ta Dago kanta dashi tana cewa’
Kina Jin kunyan kika Bari wani qato Yana tabamiki jiki?
Saurin zaro ido nijlah tayi’ cike da shagwaba,dajin kunya tace wallahi aunty…
Karki qarasa nijlah’ nafa gani da idona,, ashe baki da wayo?
Shiru nijlah tayi tana qoqarin fara hawaye aunty husna ta zare Mata ido tana cewa’ idan kikamin Kuka saina batar miki’
Hadiye kukan nijlah tayi ta sunke da kanta qasa gabanta Na tsananta faduwa’ jitayi inama kasa zata tsage ta shige ciki Dan kunya’ cigaba da Magana aunty husna tayi”
Haba nijlah banyi tsammanin haka daga gareki ba,,nayi tinanin kece Zaki tayani kare.kanki,,Amma kina kallo kinyi shiru kin zuba ido Saima dariya kike,,kinasa Rai ni husna nizan tsawatar kome?
Shiru nijlah tayi,,husna tace’ Magana nake.
Bakin nijlah Na rawa tace ah ah.
Tam yayi kyau aunty husna ta fada tana cigaba da magana’
Nijlah Mujaheed da kike gani kanin daddyn Ayman ne uwa daya uba daya,,duk da baki da shakaru nasan Zaki gane irin soyayyar da Dan uwansa yake nuna masa’ ko rantsuwa nayi bazan kaffara ba Akan soyayya daddyn Ayman Akan Mujaheed tafi Wanda yakemin’ kema shaidace sabida a gabanki yayi wasu abubuwan.
Duk da Mujaheed ya girmeni Amma Hakan be hanasa girmamani a matsayina Na matar wansa ba,, Kuma Nina riqe Mujaheed tin Bayan da mahaifansu suka rasu.
Nijlah nasan halinsa idan yanasanki Babu abinda baze Miki ba’ Mujaheed betaba soyayya da wata ‘ya mace ba Sai akanki,,Mata da yawo Suna kawo masa Hari da tayin kansu Amma yaqi amsasu gaba daya hankalinmu a tashe yake sabida rashin aurensa..
Kwatsam Allah ya kawoki cikinmu ya Kuma Yaba dake harya zabeki a matsayin Wanda zai aura,,
To meyasa Zaki saki jiki dashi Yana tabaki yadda yakeso?
Dasauri nijlah ta Dago tana kallan husna sedai wannan Karan batayi yinqurin Magana ba tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya.
Amsa Zaki bani bawai kisani a gaba kina kallo ba..