AFRA KO AMRAH HAUSA NOVEL

AFRA KO AMRAH 9-10

Ranar wata litinin Hajiya Zarah ta tashi da wata matsananciyar naquda,wanda cikin gaggawa Alhj Sadiq ya kaita asibiti, sae dai tasha wahala sosai kafin ake samu ta haifu.
Cike da murna Alhj Sadiq ya shiga dakin da aka kaita domin hutawa,murnar sa ce ta qaru ganin har ‘ya’ya biyu kwance kusa da ita.
Sae dae d’ayar tafi kama da Hajiya Zarah da kuma kyau da qiba ga shiga rai hakan yasa ya kai hannu had’e da bissimilla ya dauke ta yayi mata addu’o’in neman tsari.
Da ya gama ne ya ajiye ta zai dauki dayar,sai wayar sa ta shiga qara yayi saurin barin dakin domin kar ya tashi Hajiya Zarah da ke bacci.
Bai san cewa wayar na fara ringing ta farka ba, wanda binshi kawai tayi da ido har ya fita daga d’akin.
Takai hannu ta shafi kan ‘ya’yanta hade da basu kiss a goshi,d’agowar da zatayi ne ta had’a ido da wata mata da ke leqen ta ta window, matar sae kallon jarirran take tana murmushi yayinda hawaye ke sauka a kumatun ta.
Hajiya Zarah tace “baiwar Allah lafiya? murmushi kawai tayi ta share hawayen ta da gefen zanin ta da ta yafa sannan tace”ba komai ‘ya’yanki ne kawai suka bani sha’awa,Allah ya raya miki su akan sunna,sae da ta kalli yaran kafin take cewa “amin”
Ta dago domin sake kallon matar sae wulgawar ta kawai ta gani.

Alhj Sadiq ya d’an jima kafin yake dawowa,
yana shiga d’akin ya shiga tsananin rud’u ganin wuqa da6e a cikin Hajiya Zarah kuma babu jaririya d’aya.
“Innalillahi wa inna ilahi raji’un shine abinda ya shiga maimatawa”yana ja da baya yayinda miyon bakin sa ya tsinke gabadaya sae wani irin gumi da ke keto masa ta koina.

En uwan sa ne sukayi kici6is da shi a bakin qofar dakin wanda sae yanzu ne shigowar su asibiti.

Sosai sukayi mamakin ganin abinda ya faru da Hajiya Zarah wanda har ba a iya fahimtar farin ciki sukayi ko baqin ciki.

Gun Alhj Sadiq kuwa kallo d’aya zakayi masa kasan ya shiga tashin hankali sosai.

Bayan wasu kwanaki da faruwar hakan anyi iya bincike na ganin cewa an gano wad’an da suka kashe Hajiya Zarah da kuma sace jaririya d’aya da akayi amma ba a gano komai ba.
Sae wani shirme da yaji a gun nurses d’in da suka kar6i haifuwa cewa wae Hajiya Zarah ba ‘ya’ya biyu ta haifa ba d’aya ce,bai ce da su komai ba domin tunda aka binne Hajiya Zarah bai sake cewa da kowa komai ba sae jimami da yake fama da shi, kuma zancen su ya dauke shi a shirme da kuma rashin sanin wacce suka kar6i haifuwar ta.

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button