BAKINA YA JAMIN
★★★
Jinsu aka ɗiba su dukansu a cikin labaran ɗin, kana aka bawa Alh gado , ita kuwa tayi zaman jiran result.✍????✍????✍????✍????
More comments more typing????????♀️.
~alƙalamin????️ Doctor maryamah.~
~tabbas alƙami????️ yafi takobi????.~
#Comment
#Vote
#Share
Plx
~ƳAR MUTAN {BUBARE}CE!✍????.~
????????????♀️BAKINA YA JIMIN????????????♀️
{ƙalubale garemu mata}.
????????????????????????????????
STORY & WRITING BY DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.
marubuciyar.
TAWA ƘADDARAR KENAN!!!.
AUTAR MATA
{tikitacciyar yarinya}.
And now????????.
BAKINA YA JAMIN
{ƙalubale garemu mata}.
????????????????????????????????
AREWA WRITER’S ASSOCIATION
????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????
بسم الله الرحمن الرحيم.
PAGE 9️⃣6️⃣ ↘️ 1️⃣0️⃣0️⃣.
????????????????????????????????
_____Kwance yake a saman gadon marassa lafiya, shigowa nurse sukayi riƙe da’ita sai faman tsiyayar hawaye takeyi.
Yana ganin anshigo da’ita yayi maza ya fincike ƙarin ruwan da’ake yi masa yayi gunsu da sauri awa wani tsohon zaki.
Sakinta nurse ɗin sukayi da sauri suka fice daga cikin ɗakin da gudu, domin kuwa sun zaci gunsu yanufa.
Maƙuro wuyanta yayi , Muryarsa cike da ƙaraji da alamun ɓacin rai ya fara magana kamar haka “ke dan gidanku ashe idan bananan yawon sha_shanci kike zuwa ko¿.
Yanzu ga shinan kinje kin kwaso mamu cutar datafi ƙarfinmu.
To wallahi bazan zauna dake ba!.
Yauɗinnan saikin barmin gidana , cuta ce dai kinriga kin cutan Allah saiya sakaman wallahi.
Don haka kije na sakeki saki ukku!.
Be saketa ba, saida yayi mata jina_jina kana ya turata wajen ƙofa.
Likitocin da sukazo kawo a gaji, sune suka dauketa a kaje a kayi mata treatment ɗin gurin daya jigata ta.
★★★★★
Kai tsaye gidansu ta nufa hankalinta a matuƙar tashe domin kuwa bata san irin tashin hankali da mahaifiyarta zata shiga ba, idan har taji irin cutar da take dauke da’ita.
Sallama tayi a cikin gidan haɗi da cusa kanta a cikinsa kai tsaye, ba tare data jira komai ba ta faɗa ɗakin mahaifiyarta.
Ɗago kan da zatayi sai kawai taga mutum tsaye saman kanta tana faman share hawaye.
Boyar Allah daga ina¿.
Ƙara rushewa da kuka tayi kana tace “mama kina nufin baki ganeni ba¿.
Salallami tahauyi haɗi da tasbihi zuwa ga Allah.
Kamo hannunta tayi kana tace “Nana Khadijah lafiya kike kuwa¿.
Meya sameki haka shine kikayi jinya ba’azo a ka gaya mamu ba¿.
Rungume mahaifiyarta tayi , tana ci gaba da ɗarzar kukan da batasan ranar ƙarewar saba.
Sai bayan ta nutsune kana tahau bawa mahaifiyarta labarin halin da take ciki a gidan Alh kana ta daura mata da cewa “mama Alh ya sakeni har saki ukku, dalilin anyi mamu test dani dashi duk an samemu dauke da cutarnan me karya garkuwar jiki.
Kuka mahaifiyarta ta fashe dashi kana daga bisani ta saussauta ta dubi khady tace “a haƙiƙanin gaskiya Nana Khadijah na tausaya maki na tausaya wa , ni kaina mahaifiyarki da mahaifinki.
Cutuwace Alh ya cucemu, ubangiji Allah yasaka mamu.
★★★★★★★★★★★★★★
Zaune take a bakin titi , tasa ce ajiye a gabanta yayin da talula duniyar tunani.
Wata hatsabibiyar mota ce, ta gifta ta gun, sai Kuma gata ta dawo da baya da baya, haɗi da zuge glass ɗin motar, tabbatar da tabbas ita ɗince wacce yake zargi ya sanya shi fitowa daga cikin motar kana ya leƙa cikin motar yace “Habibah zo muje dan Allah.
Cike da mamaki wacce aka kira da habiba ta fito daga cikin motar hannunta janye da wani yaro mai kimanin shekaru 3 a duniya.
Gunda take zaune yanufa , tabbas ita ɗince kuwa yaƙara faɗa cikin zuciyarsa.
Ƙamshin hatsabibin turarensa ne, ya fargar da’ita duniyar tunani data shige.
Miƙewa tayi a matuƙar razane ganin ko waye a gabanta yayin da bakinta ya kasa furta kalma ko ɗaya.
Kallonta yakeyi cike da mamaki da al’ajabi haɗi da ƙarajin tsoron Allah a cikin zuciyarsa.
Hameed!!!.
Tafaɗa cike da tsoro.
Mamakine ya kamashi jin ta ambaci sunansa kai tsaye.
Tabbas Allah ba’abinda ya buwayesa , yau naƙara gasgata cewa ɗan adam bakomai bane a cikin duniyarnan tamu ba, face dana sani dake tattare dashi.
Bazan so jin komiye a dangane da rayuwarki ba Nana Khadijah, domin kuwa ko miye bayada daɗinji anan gurin.
Juyawa yayi gun matarsa kana yace “Habibah kinga wannan itace Nana Khadijah dana ke, baki labarinta a kwanaki, itace mace ta farko kuma ta ƙarshe data taɓa ɗaga hannu ta mareni taciman mutuncin da haryau ba mahaluƙin daya taɓa yiman shi ba.
Ya juya gun khady yace “Nana Khadijah kinga wannan itace matata wannan kuwa ɗanane, sunansa Muhammad.
A haƙikanin gaskiya lokacin da kikayiman wulaƙaci naso na dauki mummunan mataki a kanki, saidai Allah benufa ba.
Amman na yafe maki duniya da lafira, Allah yayafe mamu.
Yasanya hannu a cikin aljihun wandonsa ya zago kuɗin da koshi besan adadin suba kana yace “ga wannan kije ki samu sana’a kiyi , domin kuwa a haƙiƙanin gaskiya bara bekama ceki ba.
Hannu na rawa tasa hannu ta amsa haɗi da godiya.
Batare daya ƙara cewa komai yaja hannun matarsa ya duƙa ya dauki ɗansa suka nufi motarsa.
Da kallo tabisu cike da sha’awar kalar tasu rayuwa.
Daukar kwanon bararta tayi tanufi hanyar gida , tana tafe tana share hawaye, haɗi da cewa ” tabbas BAKINA YA JAMIN dukkanin abinda ya faru dani.✍????✍????✍????✍????✍????✍????
TAMMAT BI HAMDALLAH.
ANAN NAKAWO ƘARSHEN WANNAN ƊAN TAKAITACCEN LABARIN , INA ROƘON UBANGIJI ALLAH YASA MUYI AIKI DA DARASIN DA WANNAN LITTAFIN YA ƘUNSA, AKASIN HAKA KUWA DAFARTAN ZAMUYI FACALI DASHI.
SAI MUN HAƊU A SABON BOOK NAWA ME TAKEN……. !
~ƳAR MUTAN {BUBARE}CE!✍????.~