Labarai

Innalillahi Wainna ilaihirrajiun daya daga Cikin Fasinjojin Jirgin Kasan Abuja da aka Kubutar a Karshe dai Kan Hanyarsa ta Komawa gida Yan Bindiga Sun Kara Taresu Sun Kashe Shi

Innalillahi Wainna ilaihirrajiun daya daga Cikin Fasinjojin Jirgin Kasan Abuja da aka Kubutar a Karshe dai Kan Hanyarsa ta Komawa gida Yan Bindiga Sun Kara Taresu Sun Kashe Shi.

Jaridar Zuma times hausa ta ruwaito rahoton cewa: Kowa dai nada Irin Ta Shi Ƙaddarar a rayuwar duniya Ɗaya daga cikin fasinjojin jirgin ƙasa ɗin nan da su ka shafe watanni shida a hannun ‘yan ta’addan Boko Haram sannan aka sako su, an haɗa shi da dangin sa da su ka zo Kaduna ɗaukar shi.

Cikin farin ciki su ka shiga mota don tafiya gida, Jihar Kebbi. A kan hanyar Funtua zuwa Gusau, ‘yan ta’adda masu garkuwa da mutane su ka buɗe musu wuta inda su ka kashe shi wannan bawan Allah. Su ka kuma tafi da ɗan uwan shi da ke tuƙa motar.

Wato kwana uku kenan da fitowar shi daga garkuwar da aka yi da su fiye da kwana ɗari da casa’in a ƙungurmin daji, sai kuma wasu daban su ka kashe shi ba tare da ya sami damar ƙarasowa gida ba.

Allah Ya gafarta masa, mu kuma Ya kyauta namu ƙarshen.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button