DARAJAR 'YA'YANA PART 1

DARAJAR ‘YA’YANA PART 1


Wata safiya Iya tana kwance ba lafiya dole na
fasa zuwa makaranta tunda mun riga mun hada
kullun waina, sai kuma ciwon cikin dare.Ya Ali ya
shigo da shirin fita, don bai san bata da lafiya ba
sai da ya shigo dakin, ya girgiza da ganinta
kwance cikin bargo dakyar take magana.Arude ya
ce, ya babu lafiya ne?Tace, eh, yace meyasa ba a
tashe ni ba a gida fa na kwana?Ita wacen
sakaryar ba sai ta fada min ba.Iya ta ce ni na
hanata ta ce bari ta taso ka, ya cire hula, bari
muje Asibiti, bari in samo mota, ta ce, a a naji
sauki.Fita yayi sai gashi da likita wani dan nan
unguwar ya duba ta sai gashi hadda ruwa a dora
mata.Ranar dai bai fita bahar rana, bai taba
birgeni ba irin ranar, duk wani abu sai yayi, hatta
bata magani a baki da abinci sai gurin la’asar
sannan ya fita.Su yaya Sulaiman,Zakari da Sani
duk sun zo da matan su, sanan makota na ta
zuwa.Da yaje gurin aiki ya bada uzirin shi sai ya
dawo kusan shabiyun dare, jikinta yayi sauki.Ina
jiyo hirarsu,rokonshi take yayi aure ta ce Aliyu
bani da wani burin da ya wuce inga auranka, kai
na fuskanci kafi son sai na mutu sanan zakayi
aure.Jikinshi yayi sanyi, dan ya kasa tuna ranar
da ta kira shi da Aliyu, cikin tautasar murya da
lallashi ya ce, zan yi iya, in sha Allahu kina
raye.Ta ce, kayya, gadanga kullun haka kake
cewa, ni dai ai tuni na cire rai ka tashi katafi na
yafe maka Allah yayi muku albarka kai dasauran
yan uwanka.Yarinyar nan sadiya dan Allah ko ban
tashi ba kada ku bari ta koma zaria ta zauna
gurin wannan yaron hardai ta sami miji kuyi mata
aure.Ya ce, iya ke ce da kanki zaki aurar da ita
insha Allahu, ta ce shi kenan tashi kaje ka


kwanta.Hankali tashe ya fita bayan ya tai maka
mata ya kawota cikin daki, na tashi idona
naxubar da hawaye, na taimaka mata muka
kwanta.Ina kuka kasa-kasa ta ce,Sadiya lafiya?
Tace iya bana so inji kina cewa zaki mutu ki barni,
ta ce in fada ko kar in fada sadiya ba zan kara
lokaci ba sai dai in ajalina bai zo ba.Da kyar bacci
ya daukeni, lokacin iya tayi nisa da bacci.Shima
Aliyu tun da ya koma dakin shi fa ya kasa ko
zama, lallai dole ne ya nemi mata, sai dai
matsalar shi ta ina zai fara?Bai taba yin budurwa
ba, bai taba soyayya ba, shi kuma yana ganin
kamar raini zai ja masa in yaje kofar gidan su
yarinya.Amma bari gari ya waye yaje wajen
usman amininshi.Kafin ya wuce masallaci sai da
ya fara lekowa dakin mu ni da iya duk muna
sallah, sanan ya wuce,dan Allah ya kawo mata
sauki a cikin daren daga masallaci gidan Usman
ya wuce, ta wya ya kira shi cewa gashi a kofar
gida,Usman ya ce, lafiya?Aliyu ya ce, lafiya ba lau
ba, fito kaji.Da sauri usman ya bude gida ya fito,
sama sama suka gaisa.Usman ya ce, aboki lafiya?
Aliyu ya ce ina fa lfy, jiya tsohuwa ba lafiya, ta
fara bar mun wasiya, sannan tayita jaddada min
burinta kawai nan duniyar shine inyi aure.Usman
yace aboki ba ita kadai ba, ni kaina buri na
kenan, to tunda kaga tsohuwa ta tsananta gara
kayi ko kwa rabu lafiya.Aliyu ya ce, ai baka sani
ba, tunani na yanzu ina zanje nemo mata?Na
rantse maka banda budurwa…

Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100

DARAJAR YAYANA1-02
Posted by ANaM Dorayi on 08:55 PM, 09-Mar-16
Under: DARAJAR ‘YA’YANA
__________________NA ___________HALIMA K/MASHI Usman yayi yar dariya sanan ya ce, ni da zakaji shawarata wanan sadiya ta gidanku?Aliyu yace, ah haba?Usman yace, naga yanda ake yabon hankalin yarinyar, ko a gida tana da matsalane? Aliyu ya ce, sam ko a gida bata da matsala gaskiya, amma ban taba jin koda alamar sonta ba, to wanan yarinyar ma ina ganin ta tsaida wanda take so, in ma ba ta tsayar ba sai inga ta yi mun yarinya.Shekarunta sha bakwai fa yanzu in ban cika ma ba, usman ya ce, dai dai.Nafi son wacce ta shiga makarantar gaba da scondary a kalla ta mallaki hankalinta, ta san yadda zata kula dani sai nine zan koma in kula da ita.Usman ya ce, ba yaran yanzu ba, tunda kaga bata yiba in kaga wata da tayi maka ko a unguwarku ko a kafatanin unguwar mu’azu ka fada min yanxu anjima sai muje, kaga yanxu sai kaje wa iya da kwarin gwiwa.Aliyu yayi shiru yana tunani can ya ce, aboki kasan Allah?Nifa ba wai ina

kallon mata bane, na layinmu ma ban sansuba balle na unguwa.Usman ya ce, to aboki ka tsaya a Sadiyar mai hankalice,Sadiya tayi.Aliyu yace inda ta kaicin yake sai kuma in kirata ince ina sonta?Usman ya ce in baka iyawa bi ta sama mana ka samu iya ka fada mata kana son Sadiya, nasan zatayi murna.Aliyu ya ce, aboki daina cewa ina sonta, zadai ayi aure amma ba wai ina sonta ba, Aliyu yace kuma ba zanyi karya ba tunda banji cewa ina sonta ba,har Aliyu yaxo gida tunani yake anya kuwa zai amince cewa yana son auren sadiya? Lokacin da ya shigo dai dai na bare magani na mikawa iya, ta afa tare da kora ruwa, ya tsaya ya rike kugu yana kallon mu, tunaninshi a wanan lokacin lallai babu wanda ya dace ya auri irina, bisa hujjarshi tacewa ba zai sami matsala ba wace take tsakanin iya da matan yayanshi ba.Iya tana kuka cewa cikinsu matar yaya Sulaimance kawai ta san darajarta, kuma tabbas hakane domin sai suyi wata uku basu zo sun gaida ta ba.Ita ba wai tana kwadayin abin hannunsu ba ne, a a ko ba komai taga yan jikokinta yayi, amma Sadiya bata da uwar da ta wuce iya.Dan haka yana nan ko baya nan zata zamo a karkashin kulawarshi, burinshi yaga ya daukewa iya duk wani matsalarta, su kuma yayinshi suji da iyalinsu. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Tunaninsa ya katse lokacin da iya ta ce, gadanga
ka shigo ne?Yayi firgigit, na shigo iya.Na gaida shi
na fita, shima a ranar bai iya yi mata zancen ba,
karshe ma tunani yayi ya samu yaya sulaiman
suyi shawara.Haka kuma bayan sallar isha’i ya
nufi gidan yayan nasa bayan sun gaisa sai ya
sanar dashi abinda ke tafe dashi.Yaya sulaiman


yaji dadin zancen da Aliyu yazo dashi, sanan yace
sai ka samu yarinyar ku daidaita, Aliyu ya ce, ina
ga ba sai na sameta ba, indai iya ta amince shi
kenan.Yaya Sulaiman ya ce, iya ba zata ki ba,
yarinyar ce abinji, in ta ce bata sonka fa?Aliyu ya
ce, ai nima ba wai ina sonta bane, dacewar
auren kurum nake dubawa, shi yasa.Ya Sulaiman
ya ce, shirme kenan, to kai in kaje wajen iyar ce
mata zakayi ba sonta kake ba?Aliyu yayi
murmushi ce mata kurum zanyi ina so na auri
Sadiya, Sulaiman ya ce, Allah yayi mana zabi na
alkairi.Ka bari zanje gurin iyar, duk yanda mukayi
zakaji.Aliyu ya ce to.Yayi godiya yayi masa
sallama ya tafi..Sulaiman ya sami iya cike da
karfin gwiwa, ganinshi babu wanda zaikai iya
murna kai yasan har goron albishir zata
bashi.Amma ga mamakinshi yana gama labarta
mata dalilin xuwansa sai yaga tayi kicin kicinda
fuska ta ce kaine kaga sun dace ka bashishawara
koko shine ya sameka da zancen?Yace, a a dazu
ya zo mun da zancen sai kuma naga dacewar
haka.Ta ce, to ka koma ka fada mashi ban
amince ba, kace mashi ya nemo matarshi can
itama ta nemo nata mijin.Jikin Sulaiman yayi
sanyi ya sake tausasa murya ya ce, iya ban san
dalilinki ba, kokuma akwai abinda kika hango
wanda ba na Alkairi ba?Ta ce, na farko dai kasan
halin gadanga, zuciya ce dashi ga saurin fushi, ga
miskilanci tsiya, ga shegen jin kai.Sanan na sha ji
ko in ce ya sha fada min cewa shi yar jami’a yake
son aura.Niko tawa ko secondary din bata gama
ba.Sulaiman ya ce, iya in kin duba tunda shi din
ya ce ta mashi ai ina ganin ba za a sami wata
matsala ba.Fir iya ta ki zancen, duk ta inda
sulaiman ya bullo sai iya tabi ta wata hanyar,
haka nan yaya sulaiman ya hakura ya fita rai
babu dadi.Aliyu ya sunkuyar da kai yana
sauraron sakonshi a gurin yaya sulaiman, sam bai
zaci jin haka ba, amma sai ya ce, ba komai Allah
yasa haka shine mafi alkairi, na shi ganin ba zai
damu ba, tunda dama ba wai yana sonta
bane.Sai dai kuma yanda ya tsammaci abun yafi
haka, samun kanshi yayi da shiga damuwa, ko ba
ya son yarinyar hakika ya tsananta dason
aurenta.Ya samu iya da kan shi wata safiya yaxo
gaida ta bayan yayi shirin fita cikin dakin sa.Ya
ce, iya me yasa ba zaki bani auren sadiyaba? Ta
lissafo mashi dalilinta kamar yanda ta lissafawa
yaya Sulaiman takuma fada masayaje ya nemo
mata can.Ranshi ya baci amma bai nuna ba, sai
dai cikin sanyin murya ya ce, to shikenan iya na

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Leave a Reply

Back to top button