DARAJAR 'YA'YANA PART 1

DARAJAR ‘YA’YANA PART 1

Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100

Darajar Yayana 1-03
Posted by ANaM Dorayi on 10:51 PM, 14-Mar-16
Under: DARAJAR ‘YA’YANA
_________________NA ___________HALIMA K/MASHI Duk da kasan cewar duhun magariba ba zai sa in kasa gane bacin ran sa ba.Gaba na ya fadi, irin wanda ban taba yi ba.A fili na furta na shiga uku!Aisha ta ce, me nene?Bakinta yayi shiru sakamakon ganindatayiwa abin da nagani.Kusan minti biyu yana kallo na, ko da banga fuskarshi sosai ba na san a daure take .Sai yaja tsaki sanan yayi babban titi abin shi.Muka kwashi sauri ni da Aisha inayi ina waiwaya shi, a zuciyata ina cewa yau na kade, Aisha ta ce muyi wa ni kin ga da sauki tunda mama ta san mun xo mun koma ne.Munyi sallama iya tana tsaye tsakar gida tana cewa, kai ni wadan nan yara ko ina suka shige ne?Kai Sadiya bata da hankali, ki fita tunda hantsi har magariba, to ko kasuwar kwari ta kano suka je?Ko jiran mu gama sallamar bata yi ba bare ta amsa ta hau fada, Aisha ta shiga jero mata dalilan mu, ta ce ku refa mun baki, ko kasuwar kano kuka je ya ci a ce kun dawo tadubi Aisha ta ce uwaki ta ganki hankalinta ya kwanta, masu shegen rawar kai.Ta bini ke kuma, sai ki jira xuwan gadanga don tun yamma yake shige da fice bai ganki ba, har dai ya kare ya ce ita wanan yarinyar ina tayi ne?Ina son ta hada mun abin shan ruwa ina azumi, na dafa kirji na ce, to me kika ce masa?Ta harare ni karya zan masa?Ce masa nayi kinje kasuwa sayan anko, yayita fada me yasa na barki don baya son xuwanki kasuwar ne yasa shi siyo ankon dakansa.Na ce, na kade.Na dauki buta dan yin auwala, a xuciyata inatuno yanda ya ganmu muna fitowa a motar, da nayi salla nayi addu’a Allah ya yayyafawa abin ruwan sanyi.Da a zamar sa ya shigo da sallama ga ba naya fadi da sauri, don haka ma ban iya amsa sallamar ba, dakinsa ya shiga bayan wasu mintina ya fito tsaf tsaf cikin shirin fita.Ban taba ganin dansanda da kaki yake masa kyau matuka ba irin ya Aliyu, kan cinya ta na dora fiskata ganin ya nufo dakin Iya.Ga zato na da ya karaso zai zabga min mari,ina jiyoshi yana cewa iya ya tafi sai da safe, ta ce, can zaka kwana?Ya ce eh, ta ce, Allah ya tsare mun kai, ya kuma bada sa’a ka yawaita adu’a.Ya ce to ina yi iya, zan kara kulawa.Ya sake wuce ni ya nufi fita, da kallo na bishia raina na ce, zaki na maza sarkin jin kai.Nan ya tafi ya barni da kamshin sa sai dai da dukkan alamu yana fushi dani.Da dare ina cikin daki kwance kan gado, juyi kawai nake zuciyata tana mun nazari a kan kallon da ya Aliyu zai mun, ganin da yayi mun a motar wani kamar in kira shi in bashi hakuri, sai na fasa.Na rubuta sako kamar haka:YA ALI DON ALLAH KAYI HAKURI IN NA BATA MAKA RAI. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ban jira amsa ba don nasan ba samu zanyi ba,
amma ga mamaki na sai naji sautin shigar
sako.Da sauri na bude na soma karantawa.KUL!
BANA DAYA DAGA CIKIN MUTANEN DA SUKE
DAUKAR LOKACIN AIKINSU, SUNA HADA SU CIKIN
LAMURANSU NA DABAM.SAI KI RIKE WANAN DAN
GABA.Na lumshe ido ina son yin nazari a kan
kalaman nasa, na san dai kul! Dan gargadi ne ya
yi mun kenan ba ya bukatar a shigar masa
lokacin aikin sa.Nayi juyi ina mai yiwa kaina jajen
auran ya Aliyu, yanxu auren ya fi ban tsoro fiye
da birgeni.Washegari sukuku na tashi,Iya ta ce
jiya kuna can kuna gararin yawon ku mahaifinki
ya zo yayi ta jiranki har ya tafi.,na ce kash!Ko da
yake na san dole ya dawo kafin bikin.Ta ce ba
dole ne ba , kudi ne ya kawo sadakin ki da akayi,
sai gudumawar su dubu hamsin.Na ce hamsin
iya?Yaushe hamsin zatayi mun kayan daki?Ta ce,
ina laifi, mahaifinki fa yanxu ba aiki yake yi ba,
tunda yayi ritaya sai dai dan noma.Shi ko noma a
kasarnan yanxu dai ba a dauki maiyinsa da
mutunci ba, shine koma baya a gurin gwamna
ti.Su ba ga taki ba ba ga tallafi ba, dan
gurarenda suke nomawan ma kwanaki
yakecemun gwamnati ta ce zata amshi wurin.Na
ce iya gurin da ma ba nasu bane?Ta ce, Sadiya
kenan, dama talaka yana da guri ne a a wanan
karnin?Sai wanda Allah ya taimaka ya kuma tsaga
da rabonsa.Gurinka da takardu da komai za a
amshe maka,dubu hamsin ai yayi kokari.Na ce
haka ne Allah ya rufa asiri, duk abindaza ayi dai
dai karfinmu za muyi.Iya ta ce, in sha Allahu sai
kin zaba yata.Jugun nayi ina kallon Iya, baiwar
Allah nan tana sona fiye da yayan da ta haifa,
abin da take min ko ita ce ta haifeni sai
haka.Kusan duk dare sai bacci na ya katse, in yi
kiri kiri ni kadai cikin xullumi irin zaman da zanyi
gidan ya Aliyu.Na gama duk hashashen da zanyi
ban hango jin dadi ko kulawa a cikin auren ba, sai
yanxu na gane nufin iya ta guje mun wahala ne,
gashi lokaci ya kure mun bani da damar in ce
bana so.Kusan karfe uku na rana ina zaune ina
yankan farce na tare da gyarawa, sautin shigowar
sako naji, sharewa nayi amma naki dubawa don
nasn MTN ne.Sai kuma wata zuciyar ta ce mun in
duba, gaba na ya fadi ganin sunan ya Ali, na
duba cewa yayi.KI SAMENI A DAKI NA
YANXUN.Duk da cewa ina fargaba sai da na dan
sakemurza hoda tare da man lebe, sanan na
fesaturare.Iya ta kalle ni tana zaune gefe tana
gyaran goron ta da yayi tsutsa
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ta ce, to mai aljanun kwaliya don a sarar turare
ana zaune kin hau feshe feshe.Na ce, iya yaya
Aliyu ne yake kira na, ta ce ya shigo ne?Na ce ina
zato, amma ta waya ya turo min.Na suri hijabi na
na nufi dakin gabana na matukar faduwa.Nayi
sallama ya amsa, na shiga kallo daya nayi mashi
yana sanye da gajeren wando da(t-shirt) fara sol
na sunkuyar da kai sanan na tsugunna tare da
cewa gani yaya.Sam bai ko kalleni ba, hasalima
danna wayarsa yake abinsa, nayi kusan minti uku
sanan ya ce (ba tare da ya kalli inda nake ba).Ya
sunan saurayinki da na ganku jiya ya sauke ku a
mota?Ban san lokacin da na zauna ba don tsabar
tsoro.Sanan na ce, ba saurayi na bane.Lokacin ne
ya dubeni cikin wata irin harara da murya ta isa
ya ce, ba karamin zunibi ba ne wajen dan sanda
mai laifi yaki amsa laifinsa.Kar ki raina hankalina
kokaryata ni, sunansa kurum na tambaya.Murya
ta ta soma rawa alamun kuka zai kubuce min, ya
dora yatsansa dan manuni akan leben shi ta re
da cewa, shhhhhi!Kul!Kika min kuka, ko rawar
muryar nan bani son ji.Ya ci ga ba duk da
dadewarku da shi baki san sunan shi ba?Nayi
kokari na kalaci miyau na hadiye shi tare da
kukan da ke son kwace min.Na ce, yau ne na
soma ganin shi, yana ta binmu yana rokon mu
wai mu tsaya muka ki, toda muka ga duhun dare
muka yarda ya kawo mu, don ana wahalar mota
kuma kudin mu ba zai ishe mu mu hau achaba
ba.Ya maida kanshi ya kwanta rigingine, ya kuma
ci gaba da danna wayarshi.Kusan minti biyu
sanan ya ce, wa yake so cikin ku da yake ta
binku?Da dama yana ta binku ne kawai ya rage
muku hanya duk da dimbin jama’ar da ke jiran
mota a gurin?Tsoro ne da faduwar gaba suka
karu gareni, cikin in-ina na ce, am.. Em.. Haka ya
ce wai ni yake so.Da sau ri ya tashi zaune, cikin
daga murya ya ce, menene?Da sadakin nawa a
gurinki?Da sauri na ce, ai Aisha ta ce mashi aure
za ai min.Ya zuro kafafunsa kasa, oh, da ke baki
fada mashi ba?Na ce, ta rigani yin mga na ne
shine dalilin da ya tsareni da idanunsa.To me
yace da ta fada masa?Haka ya ce Allah ya sa
alkairi.Ya sake komawa ya kwanta.Jeki zan
bincika, in na samu zantukanki ba gaskiya sai kin
sani.Zaraf!Na mikexan fita sai ya sake cewa, me
ya fada miki lokacin da zaki tafi ya kiraki?Na ce,
ya ce ne ba godiya?Shine na ce mun
gode.Tamkar ba shi na bawa amsa ba, don bai
komotsa ba bare ya dubeni.Ina ta tsaye har
lokacin da ya kula dan kansa, sanan ya ce, kina
da wata maganar ne?Na ce, a a.Ya ce, to kin
tsaya min a kai.Na tabe baki a raina na ce,
masiffafen ikon ka zan dauke shi kuwa?Tsuntsun
dayaja ruwa……ANaM)Na fice, duk da ba lokacin
zafi bane jikina sharkaf da zufa, kan kujera na
zauna ina maida numfashi.Iya ta ce, me ya ce
miki ne?Ko abinci zai ci?Na ce a’a mun dai yi hira
ne.Ta ce, shine kika yi wujiga wujiga sai ka ce
kunyi dambe?Sakon da ya kara shigowa wayata
shi ne ya hana ni baiwa iya amsa, ko da yake
dama bani da amsar.Sunan shi na kara gani na
bude sakon, cewayayi.NA MANTA BAN
GARGADEKI BA, DOMIN KE TAWA CE TUN KAFIN
NA BADA SADAKI, BARE NA BIYA KUDINKI.Naaje
wayar a gefena, na zari buta zuwa ban daki ba
don zanyi wani abu ba sai dan inkaucewa tam
bayoyin iya.Sauran sati daya biki iya ta zauna da
duk yayanta, sun shirya yanda za su gabatar da
komai cikin tsari.Ina tsakar gida ina jiyo su, iya ta
kwala min kira sadiya!Na amsa, zo kije gidan
Hajiya Umma Rimaye matar Likita Hassan ki ce
mata tayi wa maiyin alkaki magana?In sunyi
maganar nawa ne kudin?Na ce to.Na shiga dakin,
kaina sunkuye dan harda ya Aliyu a gurin, ta ce
maza-maza ki dawo, dukkwanakin nan na kula
baki son aike.Ina shiga uwar daki na tura mashi
sakon cewa iya ta aikeni, ya bude ya gani amma
sai ya ajiye wayarsa, sanan bai ce mun kala
ba.Neko sai nayi zamana gefen gado, jin shiru
ban fito na ta fi ba iya ta ce, kin tsaya kwalliyarki
ta jaraba ko?Na ce, a a.Ya san shi nake jira, sai
ya ce ba aikenki akayi ba kina jiran menene?Na
fito na tafi.,ya Usman ne ya kawo mun katinan
bukin a ranar da dare.Lallai su na kula biki zasuyi
na sosai.Farko zasuyi walima bayan daurin aure,
sai kuma dinner, sanan akwai police day, shi
kuma washe garin daurin aure zasuyi shi,
damisalin karfe uku.Ni da Aisha da Fatiman ya
Sulaiman muka shiga rabon kati.Ana saura kwana
hudu biki, Anty Abida matar Usman ta kirani ta
waya naje, bayan mun gaisa ta ce, kina dan
gyaran jikinki ko?Na ce da me?Ta ce dan shirye
shiryen mu na mata.Na ce, a a ni bani da kudi
anty.Anty ta ce, baki tambayi ango ba?Na ce
anty, ni ba zan iya tambayarshi ba.Nan take ta
kira wayarshi ta sa handsfree, ya daga tare da
amsa sallamarta, ya ce madam ya akayi ne?Ta ce
ango, ango ka sha kamshi.Ya ce bansha ba
tukunna.Suka yi yar dariya, ta ce dama maganar
gyaran jikin amarya ne, ka san anayi.Ya ce ban
sani ba gaskiya wane irin gyara kenan?Ta ce
dogon bayani ne yanzu dai kudi muke bukata.Ya
ce nawa ne?Ta ce talatin ne kacal ba yawa.Ya ce
madan kuna so sai kun tsotse ni tas! Ya fadi? Ta
ce tashi muje gidan Hajiya Umma Rimaye.Na ce,
a a, ita ce mai gyaran jikin?Ta ce, eh.Nace na ga
iya gurinta ta aikeni in kai kudin alkaki.Ta ce, eh,
ai kawarta ke yin kayan buki, ita dai ke gyaran
jiki.Na ce gaskiya tana da kirki.An hada kayan
dilka masu kyau an lailaye ni da su, duk da
kasantuwata fara ba karamin kyau nayi ba,
kwana uku zanyi ina zuwa.Kuma ran na uku za
ayi mun lalle.Iya da kanta tayi ta yabon kyan da
nayi, haka naita zuwa ranar da na cika kwana
uku ta kira mai zanen lalle inda aka zuba min
fulawa.Abinka da fara, kowa sai tanka ni yake ta
ce,tunda gidan su yana da girma kawaye na suzo
nan a yi masu na su lallan na ce, to na
gode.Abida ce ta amso kudin ta bada, Usman
shine ya bamu kudin walimar mu.Wani abun da
ban gane ba duk dare sai iya ta dama mun wata
fura wace ita ta hada kayan hadin da kanta,
sanan ta va inno yar sokoto ta daka mata.Furar
tana da danko, furar sai kace magani gashi duk
yawanta in ta dama sai ta tsare nina
shanye.Sanan da safe ta xuba gero a turmi ta
surfe shi, wai zata tara na dama kunun safe
saboda yan buki, amma tana gamawa zata wanke
shi ruwan farko ta tsareni sai na shanye ina kuka
ina komai.Tun ana jibi daurin aure wasu suka
soma sintirin taya aiki, makota dangi duk sun cika
gidan, yan gefen su iya da na baba na.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
An yi mini kamu inda aka feshe mu da turareni
da kawaye na kamar yanda muke yi a nan
Kaduna.(Ina yan kadunan,yakukeyi kubamu
Labari,ANaM) Gidan matar yaya sani mukakwana.
Zariya za a daura aure amma an ce ni ba saina je
can ba, tunda ba tarewa zan yi ba.Na nufo gida
dan kwasan kayan da zanyi anfani da su in nayi
wanka.Su ya Aliyu na ta shirin tafiya gurin daurin
aure, an kawo motoci.Ya Aliyu ba ya gurin sai
abokanan sa sun taru a kofar gidan mu, kunya ta
kamani, na ja gefen hijabina na rufe fuskata.Ina
jin wani cikin su amaryarmu ki bude idonki kada
ki fadi mana.Sai naji muryar Usman yana cewa,
sarkin kunya kenan.Zan shiga soro (zaure) naji
mun zabga karo da wani, da sauri na bude
fuskata, gaba na ya fadi.Ya Alyu ne har wayarsa
da ya na magana tafadi.Da saurina tsugunna dan
dauke, tare muka hada hannu zamu dauki wayar.
Hannunshi ya taba nawa.Ba ni kadai ba, na kula
harshi yaji abin da naji, tamkar wutar lantarki ta
jamu.Shi ne ya janye hannunsa, na dauki wayar
na mika masa tare da furta kayi hakuri.Kala bai
ce ba, sai amsar wayar da yayi ya tafi, na bishi
da kallo yayi matukar kyau cikintsaleliyar shadda
mai ruwan suminti, tana tamaiko.Kamshinsa ya
cika zauren, a fila na ce na more muji, na juya na
nufi ciki.Sai tsiya ake min Amarya-amarya.
Munyi walimama inda nai ta canjin kaya, kusan
karfe hudu Aisha ta miko min wayata, sa ko ya
shigo na bude kamar yanda na zata ya Aliyu ne,
in da ya ce, “Alhamdulilla” na kalli Aisha dubi
abin da ya ce, ta karanta da murmushi ta dube
ni, kin zama tashi dole yayi hamdala ga
Allah.Nace, Allah ya sa haka yake nufi, wanan
danjin kan?Sakon shi ya sake shigowa musalin
karfe bakwai na safe, na idar da sallah ke nan,
ya ce kije gidan Usman da ga can za a dauke mu
ni da ke dan zuwa dinner, kawayenki kuma su
xama cikin shiri su tsaya a kofar gidan mu,
please, banda marasa hankali, bayan sallar isha’i
za a tafi.Na ce, Aisha kinji mutuminki ko?Ta da
fani, me ya ce?Na mika mata wayar ta karanta ta
dube ni.Ki dauki kayanki da zaki sa ki tafi can ki
shirya, ni kuma zan kula da sauran kawayenmu a
nan dan mu shirya cikin tsari.Kinsan su ya Aliyu
masu aji ne ba irin tarkacen nan suke so ba.A
gidan Abida nayi salar isha’i sanan na shirya da
taimakon abida da yake ita ma in dai kwalliya ne,
matirial ne na saka riga da siket ruwan madara
da ratsin kore.Sai nesa kore takalmi da jaka duk
koraye, sarka kuma ja sai muka yi anfani da ja a
kwalliyar fiska ta gashi ya sha gyara, da ta shiga
fesa mun turare sai da na soma atishawa, kaloli
ta samun masu kamshi.Da na kalli kaina a
madubi sai na ce Alhamdulillah ni ce haka?Ita ma
sai yaba ni take yi, ta shirya, sun zo daukarmu
Usman ya ja motar suna gaba shida Abida ni
kuma a ka bude mun baya ashe ya Aliyu na cikin
motar.Sanye yake cikin lallausan yadi ruwan
madara, kalar kayana ke nan hular kube ce kai
yayi kyau matuka, sam bai kalleni ba.Waya ma
yake yi motar tana tashi wutar motar motar ta
dauke dai dai lokacin kuma ya gama wayar.A
hankali motar ke tafiya motar shiru sai sanyin
(AC) da wani dan sauti dake tashi a raidiyon
motar mai sanyaya rai, ban san ko wacce zabiya
bace mai wakar ba, tunda ba sauraran wakar
turanci nake ba.Sai dai wakar tamasoya ce,
kalamar zabiyarsun haddasa min shiga wani irin
yanayi, na lumshe ido tare da jingina baya na a
kujerar motar.Kamar daga sama naji saukar tafin
hannunsa a saman nawa, da sauri na ware
idona, a zatona bayanan zabiyar ne suka sani
dan karamin mafarki.hhhhh,kujita da shiririta..
Amma sai naji yatsunsa suna ratsa tsakiyar nawa,
lokaci guda kuma ya matsatse su tsam.Na dube
shi da sauri sam ba zaka ce shi bane.Don har
yanxu yana fuskantar inda dama yake fuskanta,
na kalli hannuwa na ma duk da cewa a kwai
karancin haske bai hana ni ganin sarkakun
hanuwan namu ba.Na sake mai da baya na jikin
kujerar tare dasauke yar karamar ajiyar
zuciya.Lumashe ido nayi ina tuno karon da
mukayi dashi da zun, goshi na da hanci na suka
dakikirjinsa.Na tuna hanuna da nasa suka hadu
wajen daukar wayar.Hannuwa na farare sun sha
lalle, na lura da yanda ya tsurawa hannuna ido
na yan sakwanni a lokacin. A raina ina ta mamaki
da tam bayar kaina, shi wanan ya canza daga jin
kan ne?Koko isa ce tasa shi yin haka?Wata zuciya
ta ce koma me nene mijinki ne a yanzu.Tsayuwar
motar ne yasa ni bude ida nuna.A zatona in zai
fita dole ya sakar min hannu,amma har muka fito
hannuwan mu sarke, a haka yayi ta daga waya
na kalli gurin da muka zo, an rubuta Cristal
Garden da wani rubutu mai yi kala kala na
wuta.Usman ya shiga ciki ya fito sanan muka
shiga tare.Dam gurin ya cika da mutane an
wadata ko ina da kayan ciye ciye da na shaye
shaye, naga muta ne manyan mutane da banyi
tsammani ba.
Anci ansha kuma anyi wasa da kudi, sai dai duk
yanda abokan ya Aliyu suka so muyirawa yaki ko
mikewa tsaye.Dan haka duk wanda ya matsu da
ya yi mana liki sai dai ya ishe mu a kan kujerar
mu, abokan shi da kawaye na sun sha rawa.Sai
kusan sha daya a ka tashi, mu kam sai sha biyu
sanan muka tafi don sai da aka kwashe kowa.A
kofar gidan mu motar ta tsaya, na yunkura zan
fita, sai naji ya dafa hannuna, wato ya dora
hannunshi a kan nawa.Na kalleshi shima ya kalle
ni, dai dai lokacin Usman ya fita, da ma mun
sauke Abida a gida.Aliyu ya ciro wayarshi ya
haska fiska ta, ya cire hannunshi da ke kan
nawa, ya dora a kan kuma tuna ya shafa har
zuwa dokin wuya na.Sannan ya juya bayan
hannunshi ya shafi haba ta, dole na lumshe
idanuna abin sai kace a mafarki.Ya tsansa dan
manuni ya saka ya gewaye lebuna na, na bude
ido ina kallonshi, murya kasa kasa ya ce, ki bar
wayarki a kunne zan kira ki.A jiyar zuciya na
sauke, sanan na amsa a kasalance to.Tsakar
gidan mu cike da mutane duk sunyi shinfida sun
kwanta, kasancewar lokacin damina ne amma
anyi kwana biyu ba ayi ruwa ba.Don haka gari
duk ya dauki zafi.Na nufi uwar daka, nanma duk
jama’a ne kwance, gado na dai ba kowa.Na cire
kayan jikina nai daurin kirji sanan na fada kan
gado.Iya can na varo ta a falo tana yin sallar
nafila, a rai na na ce iya koda biki ba a daga
kafa.Filo na dauka na rumgume ina tuno
abubuwan da suka faru yau, tamkar almara ji
nake yau na zama mace sosai.Karar ringing din
waya ta shi ne ya dawo dani cikin hankali na, na
dauka cikin faduwargaba na ce salamu a
laikum.Muryarshi can kasa kasa ya amsa sanan
yace ke da waye ne a nan?Na runtse ido dan
yanda muyarshi take ratsa dodon kunnena, na ce
ni da mutane amman sunyi bacci sunyi shinfida
ne a kasani a gado nike, ya ce ok, kin san me
yasa na kira ki?Na ce a a ya ce, saboda mu
fahimci juna…
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347.
A raina na ce abin da ya kamata a ce shine a
farko ya koma karshe.Tamkar ya shiga raina.Ya
ce kila kiga abun babu tsari ko?Kafin na bashi
amsa ya ci gaba.Ni irin nawa tsarin kenan, kina
jina?Na ce eh.Yace to yanxu sai ki fada mun
dokokinki kafin kiji nawa.Da sauri na ce ya Aliyu
ai bani da wata doka sama da ta Allah da
manzonsa, wada suka tsara ita ce abin bina doka
ta ni kadai in bika.Gud to me kike so me bakya
so?Zan so in soma jin naka yaya, tunda kaine
babba.Ya ce, to da farko dai bana son kazanta,
duk inda zan shiga a gidan bana so in shaki wani
wari.Kuma bana so in ganki babu tsafta ko in
shaki wani wari daga jikinki, sannan ina son
komai a kan lokaci.Na san kin fi kowa sanin ni
dan oya oya ne, komai cikin hanzari bani son
kasala, bana son musu ko gaddama.Abu na kusa
da karshe bana son duk wani abu da zai shiga
lokacin aiki na, ina fata kin fahimta?Na ce eh.Ya
ce yan zu sai inji naki.Na ce, ni dai bai wuce uku
ba, duka da zagi ne bana so.Sai nayi shiru.Ya ce,
ina jinki, saura daya.Na ce imm…. Bashi kawai
ma.Ya ce a a, ki fada in nayi maki cikin rashin
sani fa?Bana son mu munafunci juna,fadamin
duk abinda ke ranki da xuciya daya.nace
amm…dama kishiya ce bana so dai,kuma bamuyi
sabo daxan fada maka ba.shi kanshi shiru
yayi,nasan yana mamaki ne don bai zaci jin haka
ba,a zuciyarshi shi kamshiru yayi saidai bai ji
wani mamaki ba saboda yasha samun case din
mata akan kishiya.ganin kishiya ce abu na karshe
da mata suka tsana.nima shiru nayi gabana yana
ta faduwa,tsai din dana ji araina na raya cewa
magana xai dankaramin mara dadi,can yace ba
xan yi miki alkawari ba in na duba cewa komai
na rayuwata rubutaccene tun fil’axal kamar
yanda yake ga kowa.kifahimta,baxan taba yi miki
karya ba,don kawai kiji dadi.sai dai shawara daya
xan baki,kiyi kokarin tsare duk hakkokina,ta yiwu
in kinyi hakan bazaki rage gurbin wata ba
Kuma kila baxan ji sha’awar karawa ba.(Lallai
yaya kazama abokona,muna da ra’ayi daya
dakai, dan haka me sona nima namiki nasiha
makamanciyar ta Yaya Aliyyu,kiyi kokarin
kyautatawa,tayanda zaki rufe idanuna daga ganin
dukkanin wata mace da matsayi irin na soyayya
bayan ke. ANaM Dorayi)
Nayishiru tabbas nasan gsky yafada,amma kishi
ne daninasan wanan tundaga ranar da kunnena
yaji ya Aliyu ya furta yana son aurena.can kasan
xuciyata tunani ne kada wata rana yace xai so
wata har ma ya aureta.duk sauran samarina da
duk wanda yaxo da niyyar aurena nakan fada
mishi koda na aure ka banason kishiya fa.Toh shi
xakin nawa ina naha fuskar fada masa,shine sai
yanxun…ya katse tunanina da cewa,nasan baki
fahimce ni ba akan batun kishiya,don haka a aje
zancan gefe muyi mai amfani.nima naji abinda
bakiso zan kuma kiyaye insha Allahu.kiyi baccinki
sai dasafe kar ki manta gobe akwai ranar yan
sanda.bikin da suka shirya mana,ina fatan zakiyi
shiri?muryata sarke nace Allah yakaimu goben.
shine ya katse wayar sannan nakashe tawa na
kwanta,kalamansa ne ke yawo cikin kaina na
damu da bai min alkawari cewa baxai min
kishaya ba har bacci yayi gaba dani.(kabwata duk
lokacin da saurayi yace bazaimiki kishiyaba to
kisani hakan mafificiyar karyace a hasashena,pls
kabwata karkisa saurayin yayimiki wannan
alkawari kawai dan gudun bacin ranki,ANaM)
Ya aliyu ya iya magana cikin natsuwa,kai inason
gayen sosai.
Dasafe kin fitowa nayi ina yin sallah asuba dama
komawa nayi nacigaba da bacci. da Iya ta tashe
ni sai na langabe nace mata kaina ciwo yake yi
nan ko banason tashine in ta aiki ga mutane. sai
kusan sha biyu sannan na tashi nayi wanka na
karya.Aisha taxo muka sha hira anan ma muka
xabi kawayanmu da zamu je bikin anjima
dasu.yau kam shigar Green da Golding nayi
nawani leshi mai kyan gaske,abinka da farar
mace kayan sun dauke ni duk da cewa wai farin
ne yacece injiwasu
Duk yau ban sa shi a idona ba sai yanzun da za
mu tafi., yau kam gadanga kusar yaki kakinsa
yasha na yansanda, ya iya aje hularsa a kai
tamkar sai da ya yi course din sata,wani dan
sanda ne ya jamu zuwa wajen, guri yayi
guri,Usman shi ya taho da sauran kawayena,
Police band sai tashi take ga wasu yan sanda
suna ta bin kida fareti. gurin zamanmu na
musamman muka nufa înda masu kidan suka
dafo bazanmu da kida. ya Ali da abokansa da
fareti suka yi tafiyar har zuwa gurin zaman har
wani yana cewa yakamata matar dan dan sanda
ta îya fareti itama . sun yi wasa kala kala har
wani wasan su wai lokacin suna makaranta suna
cin garin kwaki,anci ansha anyi rabon
abubuwa.sai bayan magriba muka dawo
gida.karfe sha biyun dare dai dai wayata ta soma
ruri da sauri natashi nadaga yace xo mana
natashi xaune na kalli shashin da Iya take, tadan
rumtsa kafin lokacin sallarta ya karato,Na tashi
sadaf-sadaf tamakar munafuka nafita, a kofar
daki nayi sallama, ya amsa na shiga.Kwance
rigingine na same shi yana danna wayarshi,
jikinsa sanye da farar singileti tareda gajeran
wandonta.Nayi saurin dauke kaina don kunnyar
ganinshi a haka.Na rusuna kaina a kasa ga ni
yaya ba tare da ya dube ni ba ya ce, tun cake
din da kika bani a baki dazu gurin party nan ne a
ciki na,yun wa nake ji.Na dube shi me zaka ci?
Shima sai lokacin ya dube ni, me kika ga ya dace
in ci?Na ce, ko za ka fara shan ruwan zafi tun da
ka jima baka ci abinci ba, saboda cikin ka
yawarware?Ya ce to yaya za ayi, na samu ruwan
zafin?Na ce sai na dafa maka, na mike tare da
ajiye wayata a gefe na nufi kicin, ina kunna risho
naji takun tafiya, sai ga iya tsaye a kaina ta ce,
na farka ban ganki ba lfy kika kunna risho?Na ce,
yaya ne ya kirani a waya wai yana jin yunwa shi
ne zan dafa mashi ruwan zafi , ta ce, hum!Ki dai
kiyayi kanki, kuma ri rage wanan barin jikin,
sanan kiyi maza ki dawo daki na ce, to.Ina
komawa dakin dauke da dan flaks dinsa na
ruwan zafin na same shi yana danne danne cikin
waya ta, na juyo na jawo kofi zan zuba masa ya
dube ni baki da numbata a she?Na ce ina da ita
mana.Ya ce in gani.Ya ciro number ya miko min
wayar, na amsa na danno sunansa inda na sa ya
Ali, ya ce ok, bani ruwan zafin, na zuba a kofi na
hada masa sanan na mika masa.Sai da ya amsa
ya kurba sanan ya ce, amma na zaci cewa na
wuce wanan matsayin na yaya.Na kalle shi eh
haka ne.Ya dauko wayarshi ya danna ya nunu
min numbata a wayarshi.Yayi saving dinta da
suna my choice, a fili nafurta my choice, ya ce
nima sai a canja min suna ko?Muka kalli juna
cikin ido sannan na soma danna wayata, ya ce
zauna sosai mana, sai kace ba dakin mijinki ba?
Na zauna sannan na soma rubutawa na sa
honey, sai na goge na sa darling, shima na goge
sai kuma na rubuta sweet Aly.Zan goge yayi zaraf
ya amshe wayar ta re da cewa in gani me kike
rubutawa kina gogewa?A fili ya ce sweet Aly.Yayi
dadi ki barshi haka.Ni kuma tuni na sunne kaina
cikin cinya ta don kunya.
Ya ce ai babu wani sauran kunya tsakanin mu,
kinyi alkawarin za ki rinka kirana sweet dinki har
gaban kowa?Na dubeshi cikin kunya sanan na
sunkuyar da kai ina wasa da gefen hijabina na ce
ba dai ga ban muta ne ba, yace to ni gaban kowa
zan ce maki my choice, sunan ya da ce?Na saka
yatsa a bakina ina dan wasa da shi,na ce me
yasa ka zabi ka sanya min zabin ka?Ya dan kara
matsowa, dan duk duniya ke kurum zuciyata ta
zaba har mamakin ki tai lokacin da muka taya
wai saida kikaimana yanga kafin ki amsa.Na
yunkura bari inje in kwanta, ya ajeye kofi bakya
jin dadin firar tamu ko?Ya ci gaba, kiyi hakuri
dani ban taba fira da mace ba shi yasa, na dube
shi tare da dan zare ido ya ce baki yarda ba ko?
Nace naga kana dan sanda ka ce baka taba fira
da mace ba?Amma ba wai ban yarda bane yayi
dariya gaskiya bana yi, tsakanina da mace sai dai
in matsalar da ta shafi aikina ne ta hada ko har
yanzu baki yarda ba?Na ce na yarda na mike
tsaye ya ce, firata ba dadi ko?Na ce, da dadi
mana.Ya ce to shi yasa kike so ki gudu? Iya ta ce
kar na dade,yace ta manta ni mijinki ne ya ce ok
sai da safe?Na ce tam, har na kai bakin kofa
yace, gaki dai baki son kishiya sai ina ganin ba
zaki iya kula dani ba.Ina tsoron kada hakan ya ja
maki kiashiya. Cak!Na tsaya cikin wata murya
wacce ban san ina da ita ba na ce, sweet Aly,
Allah zan iya kula da kai fa ka ji?Kasa amsa ni
yayi don jin irin muryar da nayi anfani da ita.Na
ruga da gudu cikin kunya shi kam shiru yayi yana
mama kin mata.Lallai mata abokan nishadi ne,
dubi yar hirar nan da yayi da yarinyar nan ya
shagaltar dashi ya koma kamar sakarai, yayi
murmushi sanan ya kwanta.Nima kwanciya nayi
ina tuno abin da ya faru tsakaninmu duk da
kallon da Iya ta bini da shi, da na shigo sai dai yi
nayi kamar ban lura ta ji haushin dadewar da
nayi a wurin yayan ba.Washegari ban tashi da
wuri ba sai wajen tara lokacin baki suna ta shirin
tafiya gida jen su.Sha biyu kowa ya kama gaban
shi, sai mu munata aikin gyaran gida ni da
iya.Kusan karfe uku na yamma ya kirani wai a
kwai fura ko?Don anzowa iya da fura da nono
lokacin biki, na ce masa nono yayi tsami, sai dai
in ya siyo yogot ya shigo da shi ya ce to.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Tunda na idar da la’asar na zauna zaman zabar
kayan da zan saka iya dai tana kallo na na sauke
akwatuna na zabo atamfa cikin kayan aure na.Da
na idar da sallar isha’i kuwa na shiga zabga
kwalliya ina ta feshe jikina da turaruka.Iya ta
shigo ta zauna bakin gado ta tsareni da idanunta
ko da bata fada ba nasan abinda kallon nata
yake nufi.,don haka nakoma nima bakin gado na
zauna tare da ajiye dan kwalin da na dauko zan
daura.Ta ce sadiya ni ba wai ina hanaki ki lura
da mijinki bane ko ki shige masa a ana fi so ki
bari sai kin tare, shi fa namiji babu ruwan sa da
zancen kunya, in baki ji nauyi na a matsayin
mahaifiyar Aliyu ba ai kyaji kunya na a matsayina
na uwarki.Saboda iya shege ko watsewa yan biki
basu tafi ba kin tafi dakin miji kin raba dare
saboda rashin kunya?Na sunkuyar da kaina rai
bace a zuciya ta na ce, har ga Allah shi yasa na
so in tare a daki na, ta ce daina bata rai, daraja
nike nemamaki da kima in kin tsare kanki har sai
kin tare kifi kima a idonsa, ga dai misali a gidan
ku.Kiji tsoron abinda ya faru da yar uwarki ta
zariya Harira ya faru dake, kan ta tare tayi ciki a
gidan mijin nata ya shiga yi mata wulakanci.Kin
manta banda ubanku tsayaye ne ai cewa zaiyi
cikin ba nasa bane, shi yasa in andaura aure ba
a tare ba mace ta mika kanta ba karamin so
mijin keyi mata ba za ya daraja ta.Wani dama
sha’awa ce ta kawosa gurin mace da ya biya zaiji
baya sonta, amma in tana gidansa fa?Ai yasan da
kunya ya ce yayi aure sati daya ya kori
matar.Jikina yayi sanyi, tabbas babu ja a batun
iya,kuma haka ne batun Harira, tayi goyon ciki a
gida ta haihu a gida ba ta tare ba.Kuma ya
saketa da kyar ya amshi cikin amma har yanzu
dan yana hannun uwarta agidan mu ita kuma
tayi aure a Hunkuyi.Na saka kaya a sanyaye na
zauna ina kara nazarin abubuwa.Har dakin iya ya
shigo suka gaisa ya ce, ina yarinyar nan?Ta ce,
tana ciki.Kamar daga sama sai naji ya ce, my
choice.Na fito da sauri tare da amsawa, duk da
nasan iya bata san me yake nufi ba.Amma tana
da saurin dago abu, zata san cewa suna ne na
musanman ya sa min, na amsa sannu tare da
gaishe shi.Ya miko min yoghot din in kin gama ki
kawo min.Na ce to,ya dubi iya bari nayi wanka.
.Na shiga da sallama, yana zaune kan sallaya da
alama salla ya idar, na ce baka sami jam’i bane?
Yace, shafa’i da wutiri nayi.Zan tsugunna ya ce
zauna a bakin katifa mana.Kina yi ya ce, sai kace
ba dakin mijinki ba.Ya gyara zama kan sallayar,
sanan ya dauko wata laide dake gefe ya bude ya
ciro kunshin takarda ya warware yana fadin.Kin
ganni da son kilishi shi yasa na saimuku
Balango.Ya dauki daya ya saka a bakin shi, zo in
baki a baki. Nace na koshi ni na ci abinci tun
dazu.Yace wanda kika ci da ban nawa nama ne,
matso kiji.Na dan sunkuyo ban sauka daga kan
katifarba, shima ya matso ya miko nannu ya sa
min abaki, na amsa tare da rufe fuskata cikin
tafukan hannaye na.Ya ce fada min gaskiyarki, ni
dake yanzu ba wani batun jin kunya. Kin kosa ko?
Na daga kai alamun eh, yayi yar dariya kinyi kyau
da wanan kwalliyar ta wace?Nasake makale kaina
cikin cinyoyi na, na ce eh.
Ya matso sai kurum naji ya kama ka fada ta, ya
saka dan yatsansa yana bin zanen fulawar, jikina
ya dauki bari don ji nake tamkar susa yake
min.Shima nasan yaji abin da naji don naji
muryarshi ta dan sarke.Ya ce wata gwana ce ta
zana maki wanan fulawar?Na ce wata yarinya
ce.Ya ce, yayi kyau.Ina son farar mace na dan
ware ido ina duban shi.Me yasa?Ya saki kafada ta
Ra’ayi nane kawai ba dan komai ba, ke fa?Na
sun kuyar da ka, kalar ka nafi so a cikin
maza.Yayi yar dariya, wace iri ce kala ta?Na ce,
wankan tar wada baka cikin farare kuma fara
cikin bakake.Ya tashi daga mazaunin shi ya dawo
kusa dani kan katifar.Kina nufin duk mun dace da
zabin mu?Ban iya amsawa ba saboda yanda ya
kusance ni, jiki na da na shi har suna haduwa.Ya
saka hannun shi a kafada ta ya manno nijikin sa,
fada mini gaskiya can dama kina sona?Duk da
halin da nake ciki na faduwar ga ba sabo da irin
yanda ya makale ni, bai hana ni tunanin wanan
mutimin ya cika tam baya.Ko yana zaton nima
mai laifin ce?Ya dago fuska ta, kalli cikin ido na ki
fada mun. Zan gane in kinyi karya kwa yar idonki
xata nuna mun.Naji mamakina lokacin da nake
furta can dama ina son ka kai fa kana sona?Cikin
wata ma yaudariyar murya nayi maganar.Kurum
sai na fuskanci le bunan shi a kan nawa yana yi
mun sumba, lamarin ya zo min sabo, ko na ce
bako.Ya dinga yi mun wasu abubuwa masu
firgitani har na zama bani da karfi.Tsoro na daya
kada ya gota daga haka, saboda ina tsoron
Iya…..zandakata Anan,muhadu a lokaci nagaba
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Leave a Reply

Back to top button