DARAJAR ‘YA’YANA PART 1

maka.Ya matso ya damki kunne natamkar zai cire
shi.Ba na ce kada ki kara yi mun hausa ba?Nayi
shiru dan ina tsoron yi masa turanci ya ji ba dai
dai ba ya ci uba na.Ya sake matse kunnan, cikin
turancin da zaniya na ce yayi hakuri.Ya saki kin ci
sa’a daga yanzu ba hausa tsakanina da ke.Duk
cikin turanci yake maganar.Ni dai nayi daki ina
Al’ajabinshi, mutum kamar na Allah ashe dan
iska ne, ya tasa hotunan batsa yana kallo.Shi
kuma da ya shiga dakin sai yaga kamar an jawo
mujarlar daga inda ya ajiyeta, a ranshi yace wato
dai yarinyar nan ta bude mujallar nan kenan,In
ko haka ne ban ji dadi ba, amma sai wata zuciyar
ta ce, kada ka zargeta, domin bata da rawar kai,
tsoranka ma takeji ba zata taba maka komai ba,
sai kurun ya samu natsuwa tare da gaskata
hakan.Kwana biyu yaya Aliyu yayi ya tafi, niko
cikinkwana biyun nan binshi nake da kallon
mamaki.Bayan tafiyar shine na samu ci gaba da
karatu na a makarantarmu ta maimuna
gwarzo.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta
Littatafai masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Kwanci tashi su yaya Aliyu an kammala wanan
karatun, buki sosai akayi ko na ce walima dan su
yaya Sulaiman su har can suka je nan gidan mu
kuwa mun aikatu.Anyi wainar shinkafa, da su
zobo da kunun zaki, daga can suka turoshi
kaduna (headquarter) a matsayin A. S. P Aliyu
Tukur.Ranar da ya zo gida na jima a uwar daki
ina tunanin fitowa saboda tsoron maganar da zan
masa da turanci, gashi a fallon iya suna fira.Na
zauna ina bitan abin da zan fada masa da turan
ci, can iya ta kwalo mini kira na amsa, ta ce me
kike yi?Na fito, ya kalleni dama tana ciki, kin wani
kunshe kamar wani munafiki?Na ce, sannu da
zuwa. Cikin turanci na yi maganar, shi sai lokacin
na tuna mai da batun wani turanci.Ya kalli iya
sanan ya kalle ni ya amsa, na ce ina taya ka
murna, ya ce ya gode.Ya tambayi nawa karatun
na ce lfy lau.Da sauri nayi waje ina tsoron kada
ya daukowani zancen da va zan iya amsawa ba, a
rai na na ce, baka sanan wannan ba na fi sati ina
haddar su.Bayan na fita ya cewa iya, to kin ga
dai yarkita soma zama baturiya, iya ta ce, eh, ai
hakan yana da kyau.Tunda ya dawo kullun
zancen shi da iya ba ya wuce kayi aure gadanga,
ka fito da mata sai dai in bai zo gidan ba,
kokuma bai zo mata fira ba.Har ta kare ta ce yaje
gidan hajiya talatu ya nemi diyarta Jamila, yace
iya kiyi hakuri har inga wacce ta yi mun da idona,
bana son cushe cushe.Ta ce, duk fadin unguwar
Mu’azu har yau baka ga wacce kake so ba?Sai ya
ce, ina nan dai ina binkitawa, har dai ta hakura
ta zura mashi ido.Daga baya naji suna hira da
yaya sulaiman wai ta sama mashi magani tana
ganin kamar bashi da lafiya, niko da naji wanan
xancen lokacin cewa nayi a raina, ras yake kila
ma neman matan shi yake yi a waje tunda mai
ya hada mara lafiya da hotunan tsiraici?Kuma
bayan nan ina zaton yana kalon fina finan tsiraici,
don lokuta da yawa in yana kallon in nayi sallama
dakin zai kai abinci ko wani abu sai yayi sauri ya
kashe, sanan ya ce in shigo.In kaset din arziki ne
menene na kashewa?Amma na sa a raina wata
rana sai na kama shi.
Haka kuwa watara na xan kai masa abinci darana
lokacin aikin dare yayi da safe ya dawo,Iya kurun
ya gaisar muna aikin waina ya shige daki ya
kwanta.Sai kusan sha biyu sanan ya farka,
lokacin Iya ta tafi gurin sabo mai shikafar waina,
ta ce in ya farka in kai masa ruwan zafin shida
waina in kuma bredi zaya ci to in kai masa.Ya fito
ya shiga wanka, da sauri na dauki dan flask din
sa na ruwan zafi na nufi dakin, ko mai a kashe
yake amma na san zan kunna in gani tunda
wanka ya shiga saboda shi mutum ne mai
dadewa a wanka.In dai ya shiga tamkar zai canza
fata, don haka ina lokacin sallah ya katato xai
shiga ban daki iya kance bari muyi alwala dan in
ka shiga sai lokacin salla ya fita baka fito ba.Na
jona komai ya kawo na ce oji bulumme can kasa
dan muna funci aikuwa CD yana gama login sai
ga mata da maza tsirara suna aikata masha’a.Da
sauri na kashe na fita naje na ci gaba da aikina
abin da na gani ya girgiza ni kuma naji haushin
kaina da karan bani na.Na fito na dauki waina da
bredi naje nayi sallama ya ce in shigo na shiga na
ajiye xan fita ya ce tsaya, me kika shigo yi nan
dakin?Gaba na ya fadi na ce ni flask na kawo, ya
ce daga nan sai kika yiyi me?Cikin in ina na ce,
banyi komai ba ya Ali.Ya tsareni da idanu, bashi
da tabbacin nayi wani abu amma yana shigowa
yasan an shigo.Ya kalleni, jiki.Na fita sanan na
harari dakin na tafi.A raina na ce dan iska, amma
wani lokaci sai ya kure wa’azi sai kace na Allah.
Kwanci tashi ba wuya, muna cinye kwanakinmu
har mun kammala (SS3) mun zana jarabawa
kuma lokacin ya zo dai dai da saukar karatun mu
na alkur’ani.Munyi komai cikin nasara, kuma nayi
walimata a gidan mu inda iya ta matsawa ya
Aliyu sai ya buga mun memo wanda zan rabawa
kawaye na.Sauran yayyansa ma sun taimako,
baba na kuwa da naje zaria na fada masa dubu
biyarya bani wai inyi hakuri da yake ina zuwa
danhutu can wani sa’in iya tace inyi sabon dinki
da kudi na.Dangi kam sun xo babu laifi, har yan
uwa na na zariya, babanmu ya zo da su komai
na yayi babu laifi.Da yamma ni da kawata Aisha
muna kwashe kujerun da muka zauna akai
mukayi walima a waje da kawaye na.Mun hada
su guri daya sai naga guda biyu wanda ya Aliyu
da wani abokin sa suka zauna su na hira.Ta ce,
kije ki amso wadancan cikin zolaya tayi maganar,
don tasan ina jin tsoron shi.Na ce, ke kije ki
amso.Tayi yar dariya bari inje.Tayi tamkar zata
nufi gurin sai ta fasa.Muyarshi ta katse maganata
da zanyi lokaci daya kuma gaba na ya fadi, Ke!
Na wai waya, zo nan.Naje na rusuna na gaida su
cikin in ina ya ce, ke daga jin maganar ki baki da
gaskiya ko?Na ce, a a.Ya ce, to me nene nayin in
ina din?Nayi shiru, ya kalli abokinsa ga ta.Abokin
ya ce, ina yi muki murna da yin saukar alkur’ani
mai girma, Allah yasa anyi na tsoron Allah.Na ce,
amin.Ya Aliyu ya ce, jeki dama murnar zaiyi
maki.Ina tafiya ya kalli Aliyu ya ce, kanwar nan
taka tayi fa.Ya Ali ya ce, ok, iskancin naka har
agida ma zaka yi?Auwal ya ce bada wani abu na
ce ba, cewa nayi tana da kyau.Kai da ma ka
shiga kayi yar gida tunda duk matan dake sonka
baka kallon su.Ali ya ce don me zan tsaya kallon
yayan mutane, alhalin na san cewa ba auran su
zanyi ba?Auwal ya dan yi masa dukan wasa a
kafada tare da cewa, ko jiya munyi gulmarka da
Sajen Bello, wai ina ma shine mata keyiwa wanan
shishshigin, da sai ya more kuriciyarshi son
ranshi, amma kai kullun cikin Azumin dole, in
kaga mata sai kace kaga Abokanan gaba.Aliyu ya
ce, ban ga anfanin zina ba, koda ba haramun
bace mutum ya gujeta, ya kyamace ta, dan kare
kansa daga cututukan zamani.Ina fada maka ina
da kyama ba zan iya hada jiki da wayan can ba,
kuma dole in naga mata in hada rai tun da ba
halali na bane, kuma ba muharramai na
bane.Kullun dai ina adu’a Allah ya bani mace ta
gari mai kamun kai, kuma da kuke bin matan
Allah ya shiryeku, kai gashi kayi auran ma amma
ba ka daina ba.Kayi hattara duk abin da ka shuka
shi zaka girba, kana kallo wani can zai bata
rayuwar yayan ka yadda ka fada ta yayan
wasu.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta
Littatafai masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Auwal ya ce , ka samu cikin adu’a abin ne
dawahalar bari, mata ne nishadin rayuwa, hira
da su ma a kwai dadi ne.Tsaki Aliyu ya ce in kaso
kaji dadin ba?Ni kuwa bana fatan in ji dadin fira
da mace wadda ba tawa ba, ina nufin
halalina.Auwal ya mike, bari ni in tafi kai dama
malami ya kamata ka zama ba dan sanda
ba.Sam Aliyu be mike dan raka shi ba, daga nan
suka yi sallama.Shi kam tunani ya shiga, shima
yana sabo wajen kallon fina finan batsa da
karantar mujallan batsa, duk da cewa bai taba
aikata zina ba ya san wanan laifi ne babba.Kuma
in mutum bai daina ba wata rana zai kai ga
aikata zinar, kuma tunda Allah ya rufamini asiri
tsawon lokaci yana yi ba wanda yataba ganinshi,
ya kamata ya daina.Ya tuna lokacin da ya fara,
wata rana yaje dakin su Auwal da rana lokacin
suna jami’ar Ahmad Bello ta Zaria, ya ga wani
novel a dakin ya dauka ya karanta, ashe na batsa
ne.Daga lokacin sai yaji yana so ya gani, ya ko je
wani shago a kasuwa ya siyo kaset din tare da
mujallar tun daga nan lokaci zuwa lokaci sai ya
siya ya kalla, sanan ya kona su ya sake siyan
wani.Shi da kanshi ya sha fada wa kanshi cewa,
yanda yayi Imani zai tsaya gaban Allah haka yayi
imani za a tambaye shi yanda yayi ya sami kudi
da kuma hanyar da yabi gurin kashe su.Me zai ce
game da wanan kudin da yake sawa yana siyan
batsa?San nan baya karanshi da komai sai karata
da masu hankali?Lallai wanan abune da ya
kamata yayi makansa tun kafin ya mutu.Ya mike
tare da kudircewa daga yau ya tuba,ba zai kara
ba.
Dai dai gwargwado ba xa a ce bani da kyau ba
tunda Allah bai halicci mumuna ba matsawar
mutum yana da kyan hali, balantana a ce mutum
musulmine.Aina ya ga kyau sai dai kuma in ba
tsafta, ni fara ce sol amma bani da dogon
hanci.Wanan baisa fuskata muni ba, haka
idanuwa na matsakaita ne, ni mutum ce mai
tsananin kwalliya ko alwala nayi sai na sake
sabuwar kwalliya.Haka nan iya bata gajiya da
siyan mun kayan kwalliya, sanan bata ganin
bekena duk lokacin da zan bata gurin kwalliya.A
cewarta ya mace doki ce sai da kwalliya, abinda
kawai bata yarda da shi ba shi ne, ayimini dinkin
da zai nuna surata, nan ne zata ce ba zata bada
kwamasho ba gurin yada zina.Ta ce, shigar da
yawancin mata keyi ita ce ke haifar da zinace
zinace sannan zata zuba ko nawa ne ta yankan
mini yadin hijabi amma mayafi dai sai dai inyi
asusu in siya.
Shima din ban isa in siya karami ba sai babba,
kuma mai kauri ban taba jin haushinta ba dan
nasan tana kare nine daga afkawa cikin
shaidan.Dai dai misali ina da farin jinin samari
masu sona, dan ma iya bata bari in fara fita
zance da wuri ba sai da na kai SS2 duk masu
zuwa gurina da aure suke sona.Sai dai ni cikinsu
banga wanda yayi mini ba irin injishi kane kane
cikin raina din nan ba, fada haka iya take cewa
maza ki tsaya ruwan ido daga karshe kowa ya
gudu kizo kina nema.Ai yanxu lokacin ya mace
mai hankali ake dubawa wanda yake da hali mai
kyau sanan ba jahili ba kuma ya kasance yanada
yar sana’ar da zai rikeki, to ki kamashi.Allah
shine mai azurtawa, in da rabo sai kuyi arzikin
tare, ke in ma baku samu anan ba to ya baku na
gobe kiyama.Yawan yi mun wanan nasihar yasa
nake ganin zan iya tsaida Idris kuma zan iya
auransa amman sai mun zauna da kawata
aminiyata Aisha.Mun zauna da ita ita ma tace,
gaskiya duk cikin masu sona babu kamar Idris a
hankali.Mun yanke shawarar in tsaida shi ita
kuma dama akwai makocinsu Bello dake sonta.Ku
ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347