FITAR RANANOVELS

FITAR RANA 36-40

8:30am na bugawa ta mike tay wanka ta gyara kan gadonta ta tsaftace dakinta tsaf ya fetsa ma ko ina turaren qamshi

Wani Doguwar riga ta dauko ta saka na swiss atampa an mata dinkint’ A shape wanda yabi jikinta yamata shegen kyau as usual bata shafawa fuskanta komi ba ta bude kofarta ta sauko

A hankli take taka matakalan har yakawo ta kasa,wani shiru wajen ya dauka tamkar da babu kowa a gidan, face tv data ga an’ kunne anbarsa a tashar sport yanata yi shikadai,kalle kalle ta somayi can ta hango wayarsa da wallet dinsa akan dinning table da alamn har ya fito kenan yau yama manta da ita Tabe bakinta tay da dadin jin haushin sa dabaizo ya dubatan ba.

Shi bazai tsaya ya saurare ni ba shida daukar zafi?

Tsaki taja tasan hala haushin ta yakeji,kitchen tay niyyar shiga sai caraf idanuwanta suka ci karo da shayi da aka riga aka hada aka barshi akan table..turiri yake alamar yanzun nan aka ajeshi.

Cikin sauri har kamar zata fado kasa ta ci da bakinta tay hanyar kitchen jin motsi aciki yasata dakatawa cikin sanda ta dan leka ciki kadan…

A Can ta hango najaha tanata famar kada kwai da whisker zata soya ganan slice bread agefe shima harta fito dashi.

A sudade wasime ta juya ta koma kan dinning table din ,tuni taji idanuwanta sun rufe da baƙar kishi alokacin fushine kawai yake ingizata bata iyayin tunanin komi ba,abun da ake zuba sugar ta wafca ta loda spoon uku kwarara ta debo sugar ta zuzzuba acikin tea din sann ta gauraya tana kammala hakan ta kama hanyarta cikin sauri ta koma dakinta.

Kasa zama tay daga taje nan sai ta dawo,babu’ kalar tunanin da batayi ba acikin ziriya ba,ayanzu bata da wani babban buri aranta daya wuce ta Æ™ona zuciyar najaha tay mata ragaga ita ma taji yadda akeji in an munafurce mutum

Agogon bangon dake dakin ta daga ido ta kalla After like five more minutes ta waske kamar ba ita ta sauko dazun ba cikin takun nitsuwa ta sauko kasa,tun daga kan stairs take hango najaha dumu dumu ta wani tsaya agabansa ayayin da ta kawo masa bread da wainar kwai probably wanda zai hada ne da shayin sa..

Waskewa wasime tayi fuskanta bbu yabo ba fallasa ta karaso wajen ta rusuna a ladabce ta gaishe sa,kallon ta yadinga yi yanayin sai yaga basuce wa juna uffan ba ita da najaha,

Dauke kansa yay baiwani nuna ya fahimce wani abu a tsakanin su ba.

he was right afterall yasan recent behavrs din wasime na jiya tabbas da akwai dalilinsa..

Kowaccen su da position din da ta tsaya kowacce ta kauda kanta gefe cikin basar da juna.

Najaha jira take wasime ta tuhume ta dan ta gilla mata sharri mai zafi awajen taheer kamar yadda mamanta ta shirya mata tace in wasime ta nemi kawo mata wargi taje ta harharda makirci ta gayama taher cewa haushinta wasime takeji dan bata iya abinci ba

Unfortunately kuma sai wasimen batako daga ido ta kalleta ba

Tea din taheer ya dauƙa ya zai kai bakinsa yana satar kallon sa

A niyyarsa in yagama cin abincin zai tarasu danyaji abunda yake kkrin shiga tsakaninsu wanda bai gane ba.

Kai tea din bakinshi yay a nitse,ahnkli ya masa zuƙa daya ana biyun yay sauri ya tofar dashi waje

Daga nan wani mummunan tarine ya shake masa wuya atake suka juya suna kallonsa da mamaki ayanayin su…

Wasime ta daure batay komi ba jira take najaha tace zatay wani abu,aikuwa caraf saiga najaha ta dauki ruwa ta miko masa Da muryan damuwa tanai ta masa sannu. “Yaya ka ruwa ka sha”..amsar ruwan ya
Yana shan ruwan tarin nasa ya kuma tsanantawa.
.
Nan da nan komi ya rikice masa yanata tarin babu kakkautawa

Tashi yay ya haura sama dakinshi cikin sauri wasime tay saurin barin wajen tabi bayanshi

Najaha ma tana ganin hakan saita biyota cikin sauri, wasime tana shiga itama tana shiga..dukan su biyun suka shigo kusan atare.

A can Bakin toilet suka tsince shi yanata kwaza aman tea din daya zuka

wani bangaje kafadun najaha wasime tayi ta kutsa kanta Cikin toilet din ta tsaya akan shi,aciki kulawa ta isa gareshi cikin salon makircin dabata san daga ina yazomata ba tahau tsugunawa tayi kusa dashi tasaka lallausan hannunta agadon bayansa gently tana patting din bayansa tanai masa sannu cikin sanyin murya mai nuna ta damu dashi sosai
Bata dena ba harsaida tarin yadan tsagaita masa.

Debar ruwa tay ta tsaya akanshi tana zubo masa ya amsa yana wanke fuskarshi da bakinsa.

Yana kammalawa tarin ya soma dawo masa kadan kadan,kan gadon sa ya nufa ya dan kwanta baice musu komi..

wasime ta wani harÉ—e fusknta tayo kan najaha game da jan hannunta a fusace kamar waccce zata figeta,a mugun fusace ta wurgo ta har can izuwa bakin kofa..

Harde hannunta tay akan kirjinta tace ke wai mikaka saka ma yayana ne acikin shayin nan naki

Najaha datay mugun tsorata da lamarin kirjinta na bugu tace wasime wallhy bansama sa komi ba.

Juyawa a hargitse najaha tay ta koma falo taje ta dauko tea din ta mika mata tace gashi kisha kiji ni wallahi ban sakamai komi ba.

Fauce tea din wasime tay a hannunta takai bakinta ta zuka kadan snn ta wani tofeshi da karfi
Akan fuskar najaha

Makaryaciya kawaiz azzzalumi najaha meye haka wannan wani irin sugar kika saka masa haka? innalilihai wa inna ilaihi rajiun najaha ashe kashe shi kikazo yi?..

Najaha dake krin yarce shayin da aka fetso kan fuskarta tun anan taji yawan sugar abakinta sai taji ta kara tsorata

Wani cakomo wuyarta wasime tayi ta dana mata maruka masu kyau akan fuskarta, cikin wani masifafyar diri tace
toh wallh tallahi sainaje na gaya masa kece azzaluman da kike so ki kashe shi.

munafuka kawai annamimiya…karbi tea dinki nikam Allah ya toni asirinki

Jiki na rawa Najaha ta amsa tea din ta kurba
Dan bazata iya tuna yaushe har ta loda ma taher suga a tea dinsa har yay yawa hakan ba

Ta inda wasime take shiga bata nan take fita
Sai diri take cikin masifa tana cewa”munafuka Ai kinsani sarai wallh dagan gan kikai,tun farko saida na fadamiki cewa baya son sugar amma saida kika saka masa danke azzalumace toh banda mugunta meyesa zaki loda masa yay yawa haka wato anga na banza ko?

Matsiyaciya kawai annanamiya Ai wallhi munafurci dodo ne maishi yakeci

Cikin kuka sosai najaha tace “ya isa haka wasime ya isa haka..ni wallahy bansaka mai wannan sugar ba,karya kike min..saidai in kece kika zago kika saka bansani ba.

Tureta wasimn tay ta fada har kasa cikib zafin rai tace kikace mene?
Dan ubanki sharri zakiy min..yaushe kika ganni ina aikata hakan?ko angayamiki ni makira makaryaciya irinki ce.,koda shike abunda ka sabayi ma wani aidole kay tunanin shi za’ayi maka…kin dauka bansan ke munafuka bace..
ubanwa ya baki lambar wayar yayana?in dafa abinci na dan ubanki ki kirasa awaya dan kin raina ni hardace masa ke ce kikayi?wallh akan haka saina miki shegen duka anan najaha inkin isa ki tambayeni

A fusace najaha ta tashi suka soma cacar baki kamar zasu daga gida suke haura kan juna da zage zage.

“Inke ba munafuka makira bace meye na boye ma yayana gaskiya
Kullum saiki karbe min abinci na kice za kikai masa,ashe makirci da sharrin ki kawai kike kullamin awajenshi
Toh Allah ya toni asirin ki
Na ganoki..duk wani abunda kikemin nasani
Kuma dagayau ke ba kawata bace dan bazanyi kawa da munafuka irinki ba.

Acikin haka kowa yake fidda abunda yake boye acikin ransa gabaki daya wasime saida tay kaca kaca da sirrikan najaha datake boye wa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button