FITAR RANANOVELS

FITAR RANA 36-40

Musamman ma abinda ya afku atsakaninsu jiya akan kawarta najaha
Da wasu abubuwan dataji kamar ana mata acikin bacci.

Lumshe idanuwanta tay tana dada shaƙo daddar qamshin turarensa ajikin rigar data sakadin,ajiyar zuciya ta sauƙe ta dada lume kanta cikin rigar ahankli ta dingajin wani kasala na dirar mata.

Ita kanta acikin ranta tasan tana mutuwar son mijinta taheer,saidai bata san ko yaya soyayya yake ba azahiri, kuma tanajin baxata iya rabuwa dashi ba sann baxata taba yarda najaha ko wata Æ´a mace ta rabata da shi kota aureshi ba..

Juyi tay da wannan tunanin aranta tanajin kamar inya rabe jikin Æ´a wata mace hala ranar ne ranar mutuwarta.

Yanzu da hanklinta ya kwanta sosai babu abunda bata tuna acikin abubuwan da jiya ta dinga mishi,marinsa datayi shiyafi komi tsaya mata aranta..gani take kamar bazai manta ba kuma hala zaizo ya dauki wani mummunan mataki akanta.

Ayanzu ma kunyar yadda
Zata kara hade ido dashi takeyi, bacin ta tuttuno da rashin kunyar data dinga fetsa masa jiya har da guzurin marin data dora akan fusknsa..
Wani juyi tay tana tunanin ta yadda zata soma tinkarar lamarin
Duk kanta ya dore ta rasa mezatay su dawo daidai dashi..

Wani irin vibe taji agefen pillown data kwanta tana juyowa kuwa saita ga wayarsa akasar pillown shikadai yana famar ruri

daukawa tay domin ta duba mai kirar kafin ta sauka takai mishi tana duban screen din kuwa caraf sai idanunta suka sauka akan sunan BILTI …….

A hargitse ta tashi tazauna da wayar a hannu gabanta na tsananta faduwa tanajin kanta kamar mafalki takeyi,hannunta na rawa ta danna wayar,tana karawa a kunnenta ta jiyo muryan bilti,atake atake zuciyarta ya sukurkuce ya rasa setin sa bata san ya akayi ta fara kuka ba.

Dagata dayan bangare bilti najin kukan ta fahimce cewa ba taheer bane akan layi murmushi wanda ya fi ciwo ta sakar ahankli cikin sigar wasa tace mata “a’a wasime ce?gangariya yar autan mama da babanta maman salame da fatiti..
Cikin kukar wasime ta hau murmushi tana turo bakinta da wani irin shagwabbiyar murya.
Tace yo ai baki karasa kin kira Aminatu ba?
Dariya mai dan karfi bilti tay irin wanda ta dade batay ba Can snn tace
Mata agidan taheer kenan yar gudulle na an tashi lpya?.. hawaye nakan sauko mata tace lapiya kalau biltina yaushe zaki zo?
saita kuma ta kara fashewa da sakaltacen kuka..tace ya kamata kizo min..Allah yanzu na iya abinci zan miki tuwo harda miyan kuka da nama bashi kikafi so ba..kizo kigani wallh yanzu na iya abubuwa..
Kina zuwa ai zan miki kici kiji shegen dadi..toh zakizo din?wuyanta a langwabe ta karashe tambayar izuwa ga bilti.

Bilti dat was getting so emotional ahankli ta sauÆ™e wata nakasshiyar murmushi snn tace “Masha Allah..im pround of you da kika iya abubuwa amma waya koya miki? Shiru wasime tay,ta É“ace acikin shiru kamar wanda batajinta cos a duk sanda ta tuna najaha wani bakin ciki mai girma takeji acikin ranta.

Bilti tace wasime?yaya kuma kikayi shiru,au bazaki fadamin bane insassaka mata albarka?
Haba maman salame ban labarinta mana toh meya faffaru?

Bakinta ta turo gaba cikin shagwaba tace a’a fa bilti bazafa kisa mata wani albarka ba ai najaha babbar munafukace makaryaciya ce

A mamakance Bilti tace ya subhanallh wasime lpya kike cemata haka?
Najaha ba babbar kawarki bace mekuma ya hadaku?wato dan bakida kai kinje kina fada da ita ko…wasime wai meya faru ne?fadamini inji

Fuskarta kamar zatay kuka muryanta na rawa rawa tace..bilti wallahy ba laifina bane ai ita tazo ta zalunceni ta saka mukayi fada da yayana,ba itace sai ta dinga zabga masa karya tana cemasa ban iya komi ba?bilti wallahy karya takemin..abinci na ne take daukawa ta bashi yaci sai kuma tace mishi wai ban iya komi ba kijifa?…nikuma shine naji haushi nace tunda ita munafukace ta dena zuwa gidanmu kawai ingaya miki bilti kawai saitaje ta sace lambar wayansa ta kirashi tace masa ai tay masa abinci,kumafa karyatake yi wallahi bilti abinci na ne nikadai dina na dafa a kitchen ran nan,shine har tasaka yaya yazo yamin masifa wai tafini iya komi wai inje in koyi irin nata..nikuma naji haushin munafurta ta datayi,toh datazo washe gari da safe sai na zuzzuba mata sugar a shayinta saita dauka ta bashi saiyasha saiya fara amai shine nikuma na ci mata mutunci na koreta agidanmu nace mata ita ba kawata bace..

hmmmm bilti yo akan dan wann abu shine har yaya zai wanka min mari ya koreni waisainaje na bata hakuri?..nikuma naji haushi nace masa bazanje ba, sai kuma naje aka fara ruwan sama,saiga mamanta ta fito nace mata kawai najaha nazo gani.. bilti kinji wani maganan banzan da najaha take gayamin kuwa?

Bilti dake cikin halin mamaki tay ajiyar zuciya tace mekuma tace miki?

Atake muryan wasime ya canza ya kuma raunana tafara maganan Kamar zatai kuka tace bilti cemin fa tayi wai tana son yaya na,ai sabida shima take zuwa gidanmu..tana furta hakan kuka ya kufce mata..bilti tace ehn inajinki,kukan ta cigaba dayi muryanta na rawa tace shine tace waima aure zasuyi, mene menenta ai mamanta tace mata wai zata aureshi..nikuma kawai sainaji fushi mai yawa ya kamani,inata kuka kawai sai nafara ciwo, yaya yazo ya kawuni gida shine mukayi fada dashi inata so in tafi kauyenmu..Shine ya hanani,shine nikuma na mareshi…saitay shiru taja wani gwauron numfashi…

Tanajin bilti tana doÆ™a salati tanacewa lahaula fi sha’ati wasimé?baki cikin hayyacinkine zakiyi fada da mijinki har ki daga hannu ki maresa?
Wasime da lpyar kuwa
Ahhh tohm randa nazo saidai nayidake asibiti a duba kwakwalnki dan ina tsammanin kinsamu tabo hankli..

Bilti wallhi banda tabin hankli,ai shiya hanani inyi tafiyata..

Bilti tace kinci kaniyarki kenan wasime waya koya miki hakan,ahaka zaki girma kenan har ki zama matar aure?daga kunsamu sabani kadan saiki daga hannu har ki mareshi,hau ya hauki ne? Toh waima me yay miki bayan hakan taheer baimiki dukan tsiya ba,meyake jira…?

A dame wasime tace a’a
Fa shifa bai bugeni ba,ai… ai…rarrashi yana dingayi aima yaban hakuri..Nikuma gaskiya haryanzu inajin haushi haushinshi nifa bana son ya aure najaha ne,bana son ta na tsaneta,kuma yana aurarta wallhy saina gudu na tafi garinmu bai isa ya kawomin najaha ba
Ni bazan zauna da babbar munafuka irinta ba

Gwalo ido waje bilti tay da mamakin jin hakn na fita daga bakin wasime snn tace kai wasime ashe haka kika dawo wata marar hankli?kai
,innalillahi wa inna ilaihi rajiun amma banji dadin abunda kikayi ba,kuma har ya baki hakuri kin gani ko?Kefa sam bakida saiti…yo kince najaha makaryaciya ce shine kuma kika yarda da zancenta? shin shi taheer din ne ya gaya miki yana sonta zai aureta?…shiru tay can bayan ta gama nazari.
tace a’a bai gayamin ba.
Saikuma taji wani iri aranta tay shiru cikin sanyin jiki sai bata kara cewa komi ba

Daga nan nasiha da fada tasha awajen bilti,sosai bilti ta babbata shawara masu kyau wanda zasu ficceta har anan gaba,ta gaggaya mata yarda zatana bi dashi acikin girmamawa musmmn ma intana cikin fushi,
Kaca kaca tay mata akan
Marin data wanka masa ta nuna mata hakan ne ma zatayi ya dena sonta har yaje ya auro najaha

tun jikin wasime nayin sanyi harta fara sauke hawayen nadaman mai tsanani,tana danasanin abubuwan data aikata masa acikin fushi

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button