FITAR RANANOVELS

FITAR RANA 36-40

Kuka ta fashe da shi na fitan hankli tanajin zafin sunayen daya kikkirata dashi musamman ma munafuka makaryaciya dayace..ji take badadan shi yayanta bane da wallahy saita rafka masa cizo da yakushi mai zafi

Gani take ai ba laifinta bane ita kadai,kullum najaha tana nata munafurcin ba’a mata komi dan yau kawai
Itama tay nata sau daya shikenan sai akwashe duka laifukana dora mata?acikin zcyarta tace,gaskiya hakan bazai taba yuwa ba..inde zata bawa najaha hakri toh saidai in itama najahar zata toni asirin kanta sann ta fadi gaskiyar me take mata kowama yaji snn abata hkri.

A zuciye ta mike tana share hawayenta,duk dama tana matukar jin tsoro amma hakan bai hanata tsayawa agaban da ba,tana kuka tace ni fa ba inda zanje..ni banzanje ko ina ba…ai itace mai laifi bani ba..in bazata ban hakuri ba nima baza taÉ“a bata ba.

Idanunsa ya kankance akanta snn Yace wht?
Kikace mene?

Tsuke bakinta tay tana turoshi gaba hawaye na kin dena tsilalo mata acikin idanunta
Cikin muryan kuka tace “yaa fa wannan ba adalci bane,mesa zakace nice zanje na bawa najaha hakuri,ai ita ta fara munafurta ta,da batamin ba da nima bazan mata.
Dan kawai tana kawo maka abinci shine zaka wani bi bayanta..nide wallh babu inda zanje saidai a kasheni amma wallhy bazan ba najaha hakuri ba

Kafin tagama rufe bakinta taji saukar Wani wawan mari akan fuskanta, xubewa kasa tay arazane ta fasa wani irin rikitaccen ihu dafe da kuncinta tace wayyo Allah na na higga uku,a take Yahau kanta da masifa har yana diri dan bakaramin baci ransa yay akan taurin kan datake nuna masa ba, cikin ihu da tsawa yake cewa “Are u stupid… ina wasa dake ne da zakicemin haka wato ban isa ince miki kiyi abu kiyi bako? to maza kiwuce yanzun nan kije gidansu ki aikata abunda na fada miki yanzun nan, ya fatattake

Kin motsawa tay ta kife kanta akasa tanata kuka game da turjewa, sam taki ta tashi ta aikata abunda ya umarcetan

Kuka kawai takeyi kamar wanda ranta zai fita

hannunta ta ya ja zai mikar da ita cikin bori ta firgita ta turesa ta fizge hannunta cikin zuciya da taurin kai

Zai sake fizgota tay sauri taja da baya,yabita ya capko hannunta,kokawa ta somayi dashi tafara cewa”Nika sakeni ni kasakeni,yaya baka gani ne,aruwan sama fa za’ayi aruwan ne zanje inbata hkri yanzu,.. ni wallh bazanje ba…ni tsoro nakeji ai gidan su nada nisa nide bazan ce gidansu munafukan can ruwa ya daka ni ba,Ai itama babbar munafukace mesa toh baxaka ce taban hakuri ba saika mareni kuma kace inje inbata hkri…fincike hannunta anashi tay da karfi taja can nesa ta rakube da jikin bango tana kuka arikice, daga can yake kallonta muryan sa a hatsale yace “innazo wajen nakamaki Zan kara wnka miki wani marin, dont allow me to get der.. Kifiita nace miki kije kibata hakuri

Tsawar daya daka mata yasata ficewa a dakin agigice tana rusa kuka ihunta duk ya karade gidan.

Tsaye yay turus a tsakiyar dakin Yanajin kukan nata wani Lumshe idanunsa yay yana daga tsaye,shi kwata kwara ba lamarin najaha bane ya addabesa aransa,abunda ta aikata ne na makirci ya tunzirashi ya bakanta masa ransa sosai.

He love her soo much shiyasa baiy tsammanin ganin wani faults a halayyrta ba.

Ya zabi ya runtse idanunsa ne akan laifukan najaha just so dat he can purnish her akan abunda ta aikata
Cos He doesnt want his beloveth wife to posses this evil quality.

Gameda najaha kuwa bawai munafurcinta bai bashi mamaki bane,but he really dont care koda ace hakan bai faru ba dama aransa yana da niyyar dakatar da ita daga zuwa Gidan datakeyi tana damunshi,inba dan kwanciyar hanklin wasime ba da hala baxata taba samun sakin fuskarshi ba, rawan kanta da yarantarta sosai ya qundireshi.
Daurewa kawai yakey yana kulata amma har cikin ransa baso yakei ba.

Kuma Dalilin dayasa kenan jiya yay ma wasime fada dan ta nitsu ta koyi abinci,sai dazu dayakejinsu suna fada ya fahimci ashe ma duk karya najaha take shirga masa akan wasime..

Furzan iska ya saki ta bakinshi yana mai shafe kansa izuwa fiskan shi cikin nazarin matakin dazai dauka akan najaha

A bangaren Wasime kuwa da mugun gudu ta fita,not minding the heavy storm dake sama dan wani irin bakin haddari ne a sama yay baki kirin ga iska mai karfi yana kadawa sosai ,gudu take tana kuka bata tsaya a koina ba Har saida ta isa gaban gidan su najaha.

A fannin najahar kuwa ko dataje gidansu kuka ta dinga tana complain din abunda wasime ta mata dan abun bakaramin ci mata rai yay ba musammn ma abunda tay mata na kara sugar nan, mamanta ta ne ta dinga lallabarta tace tay hakuri wasar ma yanzu aka farashi,tace daga zarar angama ruwa ta shirya taje gidan ta bawa wasime hakuri,tace hakan ne zaisa taheer ya kara yadda da ita daga nan kuma zata gaya mata yadda zata rama abunda wasime tay mata,tace “akanki sai munsa ya tsaneta ya dena yarda da ita kwata kwata…kiyi shiru abunki autana ai dani takeja. Ba ita ta fara kawo wasar ba?to insha Allahu mu zamu kai mata wasan nata har karshe..kisa ranki a inuwa snn kisani
Aurenki da taheer kamar anyi angama,karamr yarinya kamar wasime bata isa tahana afkuwar komi ba. Najaha dole ki zage damtse ki nuna mata ke ba irinta bace.
Kinaji ko?

Najaha ta goge fuskarta tace “naji mama…can sai tayo wani jimmm kamarban cakuleta ta firgita ta Dada rushewa da kuka tanayi kamar ana dukanta,.. cikin kukar tace”mama dan Allah kitaimaka min wallhy ni shi kawai nakeso,yaa taheer ya hadu .wai baza’a iya daura mana auren mu tun yanzu bane..aiba dolene bane saina kara girma ko mama?..nide wallh ina mutuwar sonshi kuma shi kawai zan aura dan Allah mama kitemaka min rarrashinta maman ta dingayi tana bata baki.

Wasime tana tsayawa a kofar gidansun aka fara zabga ruwan sama kamar da bakin kwarya
Lokacin maman najahan ta fito kenan zata kulle kofar gidansu saitaganta

Da balain mamaki a fuskarta tace”Wasima ?wann ba wasima bace meya faru meya kawoki nan cikin ruwan nan,sauri tay ta karaso tana kkrin janyeta daga cikin ruwan

A hatsale wasime ta Fauce hannunta cikin fushi tace”ni kije kice ma najaha tafito kawai…ni wajenta na zo..ba wajenki ba..inta isa sunanta najaha tazo ta fuskance ni.

Turus Mamar najaha ta tsaya da wani irin azabar mamakin zuciya irinta wasime..taga babu alaman tsoro ko razana atattre da ita.

Ruwa nakan dukanta’ tana bari kar kar kar amma bashi yahanata tsayawa tay kyam cikin masifa ba,ranta ya mugun baci,kirjinta bakaramin tafasa yakeyi
Ba.

Maman najaha dakejin bazata iya tsayawa da ita acikin ruwan sama ba tace “To kishigo ciki mana kya tsaya a acikin ruwa snn kice lallai sai najaha ta fito ta ganki ahaka?

Tace eh dolenta ne ta fito,kuma Ni Bazan shigo cikin gidanku ba,Allah ya kiyayemin…kice mata kawai tafito..

Maman najaha bata kara cewa komi ba ta koma cikin gidanta tahau dokawa najaha kira

Najaha tana fitowa tace
Toh ga marar kunyar kawanki can awaje tazo nan wai lallai saidai ace miki kifito

Da Baya baya najaha ta ja tay can gefe Tana girgiza kanta a tsorace tace”Uhm uhm mama ni wallh bazanje wasime ta kashe ni ba…shegiyar karfi ne gareta..cewa ma tay zata min lilis ni gaskiya kije kawai kice mata bana gida.

Maman dake cikke da jin takaicin ruwan ciki irin na yarta take tahauta da fada tana cewa ke wallhy kin cika tsoro shiyasa ma zata rainaki,ai dolenki kuwa kije kiji mezatace miki,aida abunda zatace miki yanzu zamu san ta indaa zamu kama bakin zarenmu,kedai dakikiyace najaha..sam baki da wayo,kekan tir kamar ba acikina kika fito ba?..inma tsoron dukn kikeji to shikenan muje tare ni zan rakaki ai intasan wata bata san wata ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button