FITAR RANA 36-40

..Najaha batace uffan dukansu suka fito a tare.
Najaha dake ta dau hudubar mamanta,da gwarin gwiwarta tayo kan wasime cikin sauri tana cewa “Wasime me ya kawoki gidanmu kukan me kike?nide
Dan Allah ki shigo ciki muyi magana mu fahimce juna,ruwa fa akeyi ni wlh bazan iya tsayawa anan acikin ruwa ba Kizo kawai
…tana fadin hakan ta wani jawo hannun wasime da niyyar kaita gida
Wani hatsallen Ihu wasime tasaka mata tana mai tureta a hargitse cikin wani haukataccen salon bori
Ja da baya najaha tay tana kallonta
…ni karki sake tabani
Munafuka kawai..kinje kinsa yayana yana cemin nayi mishi karya da munafurci bayan duk kece kika fara,dabaki munafurce ni ba nima ai bazan miki ba.
Allah ya isamin najaha
saita cigaba da kukanta
Ahankli tana kukan tace wallh bazan taba yafe miki azzaluma.
Cikin sanyin jiki da karyewar zuciya najaha tace” kai Wasime..
kuskure fa nayi dan Allah kidena fushi dani kiyafe min ,wallh Son da nakeyi ma yayanki ne ya jawo haka,Wasime ina matukar kaunar yaya taheer,ko mama na shitake sob in aura.
Nida ke fa kawayene meye na daukar abun dana miki da zafi,harda ramawa.Wasime yakamata ace kin fahimci uzurina,kinsan fa ance babu abunda so baya sakawa,Wasime Kin dau abun nan da zafi..ki dubi girman Allah….
Wani tayau taji an
tsinka mata wata gawaurtaccen mari akan fuskanta
Ahaukace wasime ta birkice mata tana cewa An dauka da zafin,an dauka din,kuma Banace karki kara kiran suna na ba?..Ke ni ba kawarki bane…Dan kinga kawai nazo nan shine zaki soma gayamin maganan banza wai kina son yayana? ni badan inji zancen banzanki naxo nan ba mahaukaciya kawai..
yayana ne yace ince miki nice na kara miki sugar a tea dinki,shine yace ince miki kiyi hkri baran kara ba..
Ni wallhi dakiyi hakri da karkiyi duk uwarsu daya ubansu daya, nide karki kara zuwa kofar gidanmu ni ba kawarki bace,karki kuma kara zuwa inda nake ko a makranta munafuka kawai…
Juyawa tayi zata tafi maman najahar ta karaso tana kwalla mata kira “ke wasime meye haka?kin haukace ne…
Kota kulata ta tayi wucewarta dan wani lungu ta je ta buya inda basa kallonta. Akan gwiwarta ta tsuguna ta dinga kuka mai tsuma tana tuna maganganun najaha datace wai yayanta take so,haka kawai taji wannan maganan ya birkita ta,wani irin ruwan kishi mai tsanani takeji mai kuma tukukin zafi tana jan zuciyarta sama sama tana kukan kamar ranta zai fita.
Nemanta suka dingayi har suka gaji suka dena
Cahn sannan ta fito ta zauna agefen dakalin gidansun ta takure kanta waje guda tadinga sheka kuka acikin ruwa.
Tun ficewarta taheer ya fito nemanta dan baiyi tsammnin da taurin kan tan nan data nuna masa dazu har zata rusuna taje gidan su najahan ba
Nemanta ya dingayi a wasu wajajen can anjima
kawai ya dawo ta gidan su najahar koda zai ganta,yana isowa daf ya dallara hasken motarsa nan da nan yaganta akofar gidan su najahar ta takure kanta waje guda acikin ruwan sama tana tikar kuka
Da hargitsatsen sauri yay parking ya taho cikin sauri ya fixgota tsaye
Ihu ta fasa masa mai kara tanacewa nika kyaleni nika kyaleni aina bata hakurin ba abinda kace bakenan?…nika kyaleni..ai ba sona kakeyi ba,najaha kawai kake so..ka kyaleni kawai nima bana sonka…
Kallon yadda ta birkice numfashinta yakeyin sama sama kawai yakei
Kan yace zaiyi wani abu jikin wasime har ya fara ragwabewa, kamar wacce dama jiransa take ya dan taba ta..yana kawo hannunsa jikinta ta firgita ta dauke numfashin ta,wani irin jan zuciyarta sama tay atake tayi luiii tay colapsing, with full force ciwon asthmanta ya tashi tafara numfashi mai matukar karfi da gigitarwa……
Na kudine 300₦ via 0152983148 GTB 08060712446….
7/25/22, 19:19 – Kawata: #SURAYYAHMSFR39.
Better path:my first nd last decison!.
Na kudine 08060712446…
Jin sauÆ™ar marinta akan fuskan sa yasashi yay wani irin runtse idanun sa,atake kuma ya budesu ya zuba raunatacun kwayar idanun sa akanta yanata kallonta da fuskar mamaki ayayin da ta sunkuyar da kanta can Æ™asa tana famar fidda wani sassanyar kuka marar kara…
Wani mummunan tsoro ne ya dabaibayeta duk jikinta na rawa kar kar kamar mazari duk sai ta rasa yadda zata aje kanta tsabar yadda kirjinta yake bugu
magana yay mata acikin tausashiyar murya mai sanyi sabida baison ya mata tsawa balle ya Æ™ara jefata acikin wani mummunan halin irinta dazu Yace “wasimé marina fa kikayi..?
A tsorace ta dago ta kalleshi hawaye taf idanunta jikinta na rawa sosai ta kara fashewa da wani matsanancin kuka.
Bata iya amsa shi ba
Gudun karta amsashin yace zai rama marinsa
Tsoron dukansa takeyi itakanta ayanzu bazata iya tantace abunda yasata ta mareshin ba
Batasan daga ina ta samu wann karfin gwiwar ba,data mareshin saitaji kamar an dawo da itane cikin hayyacinta.
shanyewa yay cikin karkada kansa bainuna yawani damu ba.
matsowa yay kusa da ita yazauka daf da niyyar kara lallanshin ta,yana taɓata ta firgita tafara kai masa hatsallen duka akan kirjinshi shiru yay ya barta harta gaji ta dena dukanshi tayi shiru
A sulale ta koma baya ta sauke kanta ajikin kujera
Gameda kife fuskrta awajen tanata kuka sosai.
Yanata kallonta shide baisan wani irin zazzafar zuciya da kishin tsiya Allah ya bawa wasime ba…shiduk a tsorace yake da yanayin jikinta shiyasa bazai taÉ“a iya mata komi ba face yabita da lallami da lallashi.
kukan ma da yasan yadda zaiyi ta dena da tuni yay mata hakan dan harynzu baimanta da kalar wahalan datasha da ciwonta ya tashi dazu ba…
Hannunshi ya ziraro ta bayanta abaxata,firgita tay dan Bata san sanda zuciyarta ya daka wani tsalle zaiyo waje ba ayayin da taji ya tabata a hankli cikin tattausar yanayi mai kashe lakar jiki yana shafa mata gadon bayanta acikin sigar lallami da rarrashi
Ji tayi kamar ma ta rude
,magana yake mata da wani irin sassanyar murya wanda daga ita sai shi kawai suke iyajin meyake furtawa abakin nashi,kwayar idanunta yake kalla Yace “I knw i was wrong to slap u nd send u away a cikin ruwan nan But am sorry”!…yadda yay maganan yasa taji wani sanyi na ziyartan zuciyan ta,tana ta kallon kwayar idanun nasa koda zataga wani alaman karya aciki sai bataga alaman hakan ba, duk da haka batafasa kukanta ba dan duk sanda ta tuno da maganganun najaha akanshi saitaji kamar wuta a ke hurawa akan kirjinta, daf da ita ya zauna a Æ™asa game da nannade kafafuwan sa snn ya dafa kafaduna kadan cike da kulawa yace
“kinga baki da lpya yanzu
Muje ciki man ki kwanta
I promise you inkin tashi a baccinki zamuyi magana ko?…
sassanyar muryan nashi dayasa yana bala’in ratsa mata zuciya,Gaba daya saita ji ta firgita dan tay tunanin data mareshin hala zai mata mummunan duka ne ya ya tattaka ta.
ganin duk abunda tay masa bai mata komi ba yasata ta dingajin rudani acikin kwakwalwanta
Wani abu ta dingaji acikin ranta mai kama da tausayi tausayin shi, jin yadda yake mata magana da tausashiyar muryansa da yadda ya saukar mata da kanshi yana lallabata,hakan yasata ta dingajin wani kasalar na dirar mata tanajin kamar ba ita bace take aikata masa dukkan wayannan rashin da’ar.
..hanun sa ya kawo kusa da ita kamar zaijawota jikinshi, firgita tay ta dago kanta tana kall’lon fuskarshi a tsorace.
Hawaye tafara sauke masa mai sanyi
Acikin rudani muryanta ma rawa tace yaya dan Allah Ka kyaleni nayi tafiyata ta,nifa babu ruwanka dani yo mai ruwanka dani?Yaya baka so na..ni inda ake sona zan koma acan kauyen mu…yo Akan najaha saika dinga marina?yaa banfa taba maka karya ba, ai kasan ba halina bane,. kuma Nima banso na mata haka ba ai itace take munafurta ta kuma kaima kaki ka fahimci hakan sai bin bayanta kakeyi,hmmm ai yanzu na ganoka..kaima ai
Sonta kakeyi ba har tace min wai zaka aureta ba?kara fashewa da kuka tay ta rufe idonta tanajin tsananin kishinsa a zuciyartaa musamman ma data furta masa hakan,acikin kukan tace “Toh ai sai Kaje ka same najaharka kuzauna tare amma ba dani ba,ai ni ba matarka bace ai itace matarka..Gaskiya ni tafiyata kawai zanyi bazan iya zama da munafuka irinta ba..
Kaima ai watarana saita maka munafurcin kuma ni wallhy babu ruwana.
..bakana bin bayanta ba?
Maganan nata cike da yaranta takarashe shi.