FITAR RANANOVELS

FITAR RANA 36-40

Nadama da tausayinta gaba daya sune karara acikin kwayar idanunsa

a lokaci guda sai ya kuma ya dawo mata tamkar wani soko yanata tsoron kada Allah yasa ciwon nata ya cigaba da azabtar mishi da ita

A yanzu ne ya gane
Duk laifinshi ne, da baimata hukunci ta haka ba da bata tsince kanta acikin wan mummunan yanayin ba, kuma yasan da wasimé zata fahimce sosai inda jan kunnenta kawai yay.

Jikinshi bakaramin sanyi yay ba,hakama zuciyarsa a matukar karye yake ganin yaddda take bacci so uncomforbly saboda shortness of breath da chest pain daya dabaibayeta,ga wannan kurman kukan datakeyi acikin bacci mai darsawa zuciyarsa tsoro da nadama mai tsanani.

Ya dade yana durkushe akan gwiwarsa agabanta Kirar sallah sallan la’asr shine kawai ya tayar dashi..alwala ya shiga bayi yay snn ya fito ya dan bude windonshi domin yaga yanayin ruwan,gani yy haryanzu ana yi amma bamai karfi kamar na dazu ba.

Acikin ruwan ya sauko ya wuce masallaci ya jona jam’i duk hanklinsa yana kanta agida..ana idar da sallah ya tattara kafafun sa ya dawo gidan ya samu tana kan baccin ta haryanzu…

Zama yay abakin gadon yay shiru,sai can da ya waiga yaga wayarsa na famar ruri,dauÆ™awa yy yaga sunan ogansa ne ke yawo akan screen,ajiyar zucy yyi har saida yy composing kansa sann ya dauÆ™a “Yace Good afternoon sir.

Ogan nasa yace afternoon doctor taheer,dama nakira ne in sanar dakai cewa union of military health council
Dake cameroun ta biyaka wasu kudade sabida aikin da kukaje kukay acan kwanaki,so be aware ur own share.
Which Will come along with ur dis month salary zuwa anjima ko gobe da safe,….

A hankli taheer ya lumshe idanun sa snn yace yes sir..thank you for this information sir..

Ogan baice uffan ba ya cigaba “Snn gobe kana zuwa schl after exams dinka na karshe kazo ka sameni a office akan takardun tafiyarka karatu US da nakeson kacika i hope am clear?
..nan ma yace yes sir..daganan basu kara cewa komi ba suka katse wayar.

Yana aje wayar ta fara wani sabon ringing, ya leka kadan sai yaga wani course mate dinsa ne yake kiran shi probably akan maganan kudin ne,yasan by now kowa yana zumudin samub makudan kudin which is upto 2million naira ga kuma karin salary,yasan abun murna ne mma bayajin shi zai iya wani zumudi ko murna musammn ma ayanayin dayake ciki yanzu,karar wayar ne ya razanar da wasime ta firgita acikin bacci ta farka tana kkrin hantsalowa kasa a gigice

bai iya daukr waya ba yabita kanta da sauri ya fixgota jikinshi ya rungumeta tsam yana mai rada mata subhanalla subhannallah acikin kunnenta ,rawa rawa jikinta yakeyi,haryan zu bata fasa fidda numfashinta ba..wani lamo tay akan kirjnshi yana famar shafa mata gadon bayanta ahankli cikin yanayin lallashi da son ya kwantar mata da hankli.

Iduwanta a lumshe ta lafe tana tuno duk abunda ya faru da ita yau acikon kwakwalwnta,

wani Shiru wajen ya dauka dashi,a tunanin shi nitsuwa ne yake son shigo mata yasatayi shiru, baisan sake sake kawai ta bige dayi acikin zuciyarta na yadda zata gudu ta rabu dashi ba

Motsawa ta shigayi dan ya saketa amma sai bai saketan ba,wani irin jan zuciyarta tay takaishi can sama snn ta mike zauna ta kwaco kanta ajikinshi da bala’in karfi…

Da mamaki ya kalleta ,sai yaga ta tashi tsaye a hargitse,shima tashin yay da niyyar kamo hannunta yana tabata ta callara masa wani gigitacccen ihu tamkar wacce taga dodo

A fusace cikin kuka ta shiga cewa ni wallh
Kadena taÉ“a ni..nika kyaleni…bana so..
Kabarni…ya matso kusa ta ja baya a borance tana kuka sosai..nakasshiyar ajiyar zuciya ya sauÆ™e
Snn ya rage sautin muryanshi ya sako dashi kasa kasa cikin lallashi
“yace …hey Please calm down..baki ganin bakida lpya ne?da sigar lallami da karya wuya ya dada cewa ‘infa bakiyi shiru kin dena kuka ba ciwon ki zai kara dawowa, kiyi hakuri mana kiyi shiru kinji.

Wasime data kankame jikinta ko jinshi ma batay ba..a fizge ta kama hanya cikin sauri zata barmishi dakin yay sauri ya jawota ta fada ajikinshi ya kankameta kallonta yakei hanklinsa tashe da sanyin murya yace “Ina zakije kuma,kizauna anan tare dani mana uhm?..bata amsashi ba ta kara fashe masa da wani matsanancin kuka acikin
Kukan ta tamke idanunta tashiga cewa “o’o o’o ni wa’lhy bazan zauna dakai ba..koma ina zanje ai babu ruwanka..leave me alone for godsake ni tafiyata kawai nakeso inyi..kkrin jawo hanklinta yake izuwa gareshi yaga ta dauke kanta da sauri tana mimmikewa ajikinshi tana naushin shi da iya karfin da Allah ya bata.

tun kafin ya hankara ya kamata subul ta kufce a hannunsa ta fado kasa snn tay saurin tashi tsaye da mugun gudu ta fice a dakin ta wuce nata dakin direct tasaka key taciki tanata kuka..
Sanda tay kukan ta ya ishe ta snn ta share hawayen da suka bata mata fuskanta

Jikinta a matukar sanyaye ta tashi tabar wajen bakin kofar tana tafiyarya a hankli harta karaso ciki ta tsaya a tsakiyar dakin,Daga ita sai yar towel din daya daura mata akirji.

zubewa tay a gaban wardrob dinta haryanzu bata dena gunjin kuka sai wani jan zuciyarta sama sama,sa hannu tay ta bude wardrob din snn tahau fidda dukkan wani kayanta dake cikin wajen

Jin ana buga kofa yasa kara rikicewa dan ko ba ‘a fada mata ba tasan taheer ne ya biyota yana son ya shigo ciki.

Muryashi ta tsinkayo kamar bashi ba,yana magiya yana cewa wasimé kiyi hkri please open d door nd listen..kinga baki da lpya
Dont hurt ursrlf anymore.
Wasime…wasimé..wasimé..

Tanaji yana kiran sunanta da zance kusan yafi kowa iya pronoucing dinsa with difrent disturbing tune,kuma tanajinshi amma haka tay shiru batako kulashi ba…

Kukanta ta cigaba dayi a hakli,jim kadan jin wajen ya dauka da shiru kwakwalwanta ya soma bata hala yaje dauko extra keys ne.

Batasan ta inda karfi ya zo mata, jin kanta kawai a tsaye hartay wani wuf ta tashi tana neman abunda zata kwashe kayanta aciki,da bataga komi nan kusa ba daya daga cikin hijabanta ta shimfida akasa ta tuttula kayayyakinta akai tayi sauri ta doresu,daga nan ko tsayawa saka wani kaya ko takalmi batayi ba,rungume kullin kayanta tma hammatarta ta bude kofar dakin tana dan lekewa waje,ganin ba kowa yasa ta fito tafara tafiyarta cikin sauri sauri da kayanta a damke a hammatarta kamar wacce zatayi gudun hijra
Ta koma kauyensu..

Harta sauƙo falo tana sauri gabanta nakan faduwa danji take kamar ba zata isaga bakin kofar tay waje ba.

Saidai ko tsakiyar falon bata isa ba taji takun mutum a bayanta kirjinta na bugu ta juyo a farge dashi, zata rafka a guje kenan ya daka tsalle ya jawo hannunta da karfi ya kamota ta dawo baya gameda fadowa ajikinshi

muryansa harna rawa yace “oh my god what r u tryn to do?kuka ta kara fashe masa dashi jin harya matsota ajikinshi batada wani ikonyin wani motsi…

Ta rufe idonta gam cikin fada tana cewa
“Kabanni kabanni..nikam kasake ni..

Hanklinsa a tashe ya juyo ta tana fuskantar sa da mamaki da tsoro a fusknsa yace”wasime Ina zaki da kaya?..
Wher did u think ure going..innalillhi wa inna ilahi rajiun..ohhh guduwa wai zakiyi?

Idanunta a rufe gam gam tana kicin kicin tace babu ruwanka da inda zanje
Nidai Kasakeni inyi tafiyata..bana kara zama anan..xaman ya ishe tafiyata zanyi ainasan hanyar tashar garinmu.

Yana kallonta baisan sanda ya sauke ajiyar zuciya mai rikitarwa ba,hannun ta yaja cikin basarwa yana cewa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button