GOJE

GOJE 37 and 38

Ad

_____

Be kalleta shi ba ballanatana yaji maganarsa ya cigaba da ligwigwita leban! hannunta tasa kan nasa tana kokarin cirewa ya rike sosai! yace.” Yau zanga karshen rashin kunyarki.”

Asp yace.” Ka janye haka tayi kuskure tana neman afuwa.”

Yace.”Da bakinta nakeso ta nemi afuwar idan ba hakaba to zamuje a haka ban damu ba.”

Asp din ya kalleta tayi wujiga-wujiga! ta shiga hannun maza! hawaye harda majina!! dariya ta kusa kubce masa ya danne ya kalleta da fadin .” Ni zan zama sheda idan zaki bada hakuri.”

Kanta ta d’aga alamun ta yarda. Ya kalleshi da fadin.” Ta yarda zata bada hakurin ka saketa.”

Ba lokaci guda ya saketa ba sai da ya niyya tukkuna sannan ya saketa! kawai sai ta kifa kanta jikin motar tana wani irin kuka na tsantsar takaici da bakin ciki.

Asp ya kalleshi da fadin.” Baka kyauta ba, nida na had’a ku zama guri daya nayi hakan ne da kyakykyawar munufa dana san abunda za kayi kenan da ban zaunar da kai a kusa da ita ba.

Ta’be baki yayi bece komai ba ya cigaba da jan carbin dake hannunsa.

Motar tayi shuru na ‘yan mintina ‘kasa-‘kasa sautin kukanta yake tashi tare da ajiyar zuciya.

Asp yace.” Kiyi hakuri kinji ki bar kukan kada mu sauka a haka wasu su dauka wani abu ne.

Ad

Hannu ta dora saman lebanta da yayi tudu ya kumbura saboda ligwigiwatar daya sha ta kalleshi da fadin.” Asp ni zaku yiwa haka ko? shikkenan yau zaku ga gatana.”

Asp yace.”Aa ni meye laifi na babu ruwana wanda yayi laifi ai ya san kansa duk hukuncin da ya kamata kiyi masa daidai ne amma kema ki kiyaye ki dinga girmama na gaba dake.”

Bata iya ce masa komai ba taja mayafin jikinta ta rufe fuskarta dashi, gabad’aya jikinta laushi bakinta sai zafi yake, bata tsammanci rashin imaninsa ya kai hakaba ya ligwigwice mata le’be saboda tsabar mugunta har sai dai ya kumbura! wallahi ko za’a mutu ba zata bashi hakuri ba.

Shima ganin yanda ta galabaita yasa beyi wata magana ba, yana dai jin yanda take sauke ajiyar zuciya dalilin kukan da taci, har suka isa masarautar bata sake magana ba, a maimakon tayi farin cikin dawowarta mahaifarta, kawai sai ta shiga kumbure-kumburen kiris take jira ta fashe da kuka.

Maimartaba da kanshi ya fito domin yi musu barka da zuwa, direba yana parking ta bude motar ta fito, ba tabi ta kan kowa ba ta wani fashe da da kuka kamar wata kan’kanuwar yarinya taje ta rungumeshi tana shashshaka! shi kam fuskarta ya dago yana goge mata hawaye tare da rarrashinta, Aunty Maijidda ce ta jan hannunta suka nufi sashenta tare, hakan beyi wa Safah d’adi ba, ganin yanda yarinyar tayi kamar bata gansu a gurin ba, koda yake daman dole hakan ya faru tunda ita din ta kasance mai yi mata fada gami da nuna mata kuskuranta.

Bata iya barin gurin ba sai da ta tabbatar da cewa an sauki bakin a guri mai kyau da kuma dukkan abun bukata.

Gimbiya Aysha kuwa kunya da kawaici ya hana ta fitowa tarar su, amma tana zaune labarin abinda yarinyar tayi ya isa kunanta daga bakin ‘yan uwanta Hassana da Husaina wanda su d’in ma ta nuna tamkar ba jininta koda yake inda sabo sun saba da halinta amma dai abunda tayi musu a yanzu ya ‘bata musu rai mutu’ka!

Sosai suka samu kulawa mai kyau kafin maimartaba ya bukaci zama dasu sai da sukaci abinci suka gabatar da sallar la’asar tukkuna sannan suka sameshi a fada shi kad’ai domin akwai maganar da yake so suyi a tsakaninsu.

Gaisuwa suka sake mikawa a gareshi kafin shi da kansa ya mika godiya a garesu akan alkairin da sukayi masa.

Asp yace.”Ranka ya dade ai babu godiya a tsakaninmu da kai, domin kai uba ne a gurin mu, ka cancanta da abunda yafi haka, bayan hakan kuma kulawar da mukayi akan yarinyar nan hakkinmu ne tunda aikin mu ne kare rayukan al’umma.”

Ya girgiza kanshi da fadin.” Tabbas maganarka haka take Asp amma dole nayi godiya domin samun irinku masu tsoron Allah da kishin ‘kasa zaiyi mutukar wahala wannan dalilin yasa na jima ina nazari da tunanin irin alkairin da zanyi muku.”

Kafin Asp din yayi magana ya riga shi da fadin.” Ranka ya dade kada ka damu kanka akan wannan al’amari wallahi ni abunda nayi akan yarinyar nan don Allah nayi bana bukatar komai a gurinka face addua.”

Murmushi yayi yana sake jin kaunar yaron a cikin zuciyarsa, yace.” UMARU kenan addua kam zan cigaba dayi muku har karshen numfashina amma ba kaji bahaushe yana cewa (yaba kyauta tukwici ba) ba don kada nace na baka auran yarinyar nan ka dawo min da kyautata ba to dana baka ita sakamakon alkairin da kayi min.”

Fadar tayi shuru sakamakon maganar.

Kasa d’ago kansa yayi ballanatana ya nuna rashin amincewarsa da kyautar da akayi masa…………..Jin beyi magana ba yasa yace.” UMARU kodai baka kar’bi wannan kyautar tawa bane.”? Asp da sauri yace.” Aa haba dai! ranka ya dad’e wane mutum! kyautar mutum ba karamin al’amari bane sosai ni naji dadin wannan al’amari kuma kayi kyautar akan ga’ba domin dama bashi da aure a halin yanzu mungode sosai da wannan karamcin.”

Fuskarsa cike da annuri yace.” Asp ka ari bakinsa kaci masa albasa amma yanayinsa ya nuna kamar beyi na’am da wannan kyautatar tawa ba.”

Yayi namijin ‘ko’karin kawar da damuwarsa kansa ya dago tare da kokarin aro walwala da farin ciki yace.” Ranka ya dade farin ciki ne ya hana ni iya magana, tabbas abunda abokina ya fada hakane kayi min kyauta akan ga’ba kuma na kar’ba hannu biyu nagode kwarai da wannan karamcin.”

Ad

_____

Previous page 1 2 3 4Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button