GOJE

GOJE 37 and 38

Ad

_____


Washe gari da wuri suka shirya tafiyar, bahaushe yace sabo turken wawa, ‘yan kwanakin da tayi a tare dasu ya sanya duk jikinsu yayi sanyi har dashi Asp din kawai ya daure ne domin ya san dole watarana yarinyar zata bar hannunsa, Madam dai kasa hakuri tayi sai share hawaye take a fakaice.

Al’amarin ya bata mamaki mutuka! ta rasa wane irin so matar take mata, gabadaya sai jikinta ya mutu ta rungumeta da fadin.” Mommy kiyi hakuri ba mu rabu da juna ba insha Allah zan dinga ziyartar ki, bayan haka kuma zamu dinga gaisawa ta waya ki daina kuka.” tana maganar tana share mata hawaye.

Hannunta ta rike da fadin” Idan kin isa gida lafiya kice ina gaishe da mamanki kuma insha Allah idan an kwana biyu zamu kawo muku ziyara dani da Nabila.”

A sanyaye tace.”To shikkenan in Allah ya yarda zan sheda mata sa’kon ki daga zarar na isa .”

Nabila ta fito daga daki ta same su cikin damuwa, a sanyaye ta zauna kan kujera tana kokarin magana ya k’araso gurin yana duba agogon dake hannunsa, ya kalleta da fadin.” Tashi muje ko.” Ta mike tana gyara mayafin jikinta, Nabila ta kalleshi da fadin.” Dady zan je nima.” kai ya girgiza da fadin.” Ki bari idan an kwana biyu zaku shirya zuwa keda Madam.” Kamar za tayi kuka tace.” Dady ni nafi so naje yau.” be saurareta ba ya kama hanyar fita, itama da sauri tabi bayansa domin bata so ta tsaya dogowar magana zuciyarta ta karye, gabadaya suka bita da kallo cike da alhinin rabuwa da ita.

Wayarsa ya kira ya sheda masa cewa sun fito suna jiransa.

Da yake tuntuni ya shirya tafiya sai kawai ya fito daga gurinsa kai tsaye bangaran su Uwale ya nufa domin yi musu sallama.

Fitowarsa ta dauki hankalinsu daga ita har Asp din……Yana sanye da kayan mu na hausawa shadda milk colour dinkin tazarce har kasa, sai yayi amfani da hula zannar bukar mai duhun zare, kafafunsa sanye da bakin takalimi mai gidan yatsa, agogon dake d’aure a hannunsa ma baki ne, yayi kyau sosai fuskarsa tayi kar! sai fitar da annuri take.

Kasa janye idonta tayi daga kansa suna magana da Asp yana tsokanarsa cewa yayi kyau a cikin dogwayen kaya, murmushi kawai yayi kafin ya fara duba cikin motar, sai suka had’a ido da sauri ya janye nasa yana gyara yanayin fuskarsa, babu fara’a a fuskarsa ya kalleshi da fadin.” Ya za’ayi tafiyar ne.”?

Asp din na ‘ko’karin magana direban da zai jasu ya iso gurin, gaisuwa ya mi’ka kafin ya bude motar ya shiga Asp din yayi saurin zama a kusa dashi, ya kalleshi cike da mamakin abinda yayi wato yana nufin shine zai zauna kusa da yarinyar.

Ad

Ba tare daya shiga motar ba ya kalleshi da fadin.” Ni yafi kamata na zauna anan gurin.” Ya kalleshi da murmushi a fuskarsa yace.”Akwai dalilin da yasa nayi hakan kai dai kawai shiga mota mu, tafi.”

Ya jima yana kallonsa gami da hasaso dalilin da yasa zai ce dole ya kusanci yarinyar, ajiyar zuciya ya sauke bada son rai ba ya bud’e motar ya shiga da bisimillah a bakinsa.

Duk maganganun da suke tana jinsu, itama taji haushin abinda Asp d’in yayi kome yake nufi oho! dalilin da yasa kenan yana shiga motar ta kawar da kanta tana ya mutse fuskarta.

Shima bai ce mata komai ba ya mayar da hankalinshi gurin tasbihin da yake ja da carbin dake yatsan shi a ma’kale.

Jefi-jefi suke hira a tsakaninsu kafin Asp din ya juyo ya kalleta da fadin.” ZINATU yau sai kwanan gida ko.”?

Baki ta ta’be kafin tayi masa wani irin kallo mai kama da harara! kamar wanda yayi mata laifi, ta d’auke kanta uffan ba tace ba.

A maimakon hakan da tayi masa ya ‘bata masa rai sai kawai ya fashe da dariya yana kallonta da fadin.” Ke kam kin zama hukuma! sai rarrashi abu kad’an ke tunzura zuciyarki kamar ba d’azu ki ka gama kuka ba okey mu yanzu dai ba za kiyi kukan rabuwa damu ba kenan.”

Ta kalleshi still dai bakin ta tabe kafin tace.” Ranka ya dade meye had’a ni daku da zan zauna ina kukan rabuwa daku ni burina ma nayi nesa daku.”

Ya dinga girgiza kanshi yana mamakin furuncinta, yace.” Ni dai na san a’iya zaman da mukayi dake banyi miki wani abu ba ballanatana ki k’ullaceni, meye duniyar ma da kuke gaba da junanku dalilin da yasa na shirya zamanku a kujera daya domin ku gaisa da junanku duka ku yafi junanku, duk da ba wani laifi kukayi wa junanku ba amma duk kun tsangwami kanku da kanku, ke ZINATU kece ‘karama ya kama kiyi wa abokin zamanki sallama ki gashe shi sannan kiyi godiya akan alkairin da yayi miki wannan shine zaman duniya.”

Ta dinga kallon Asp din tana jin takaicin maganarsa, a maimakon tayi abinda ya umarceta kawai sai ta juya tana galla masa harara! wacce ta sanya shi juyowa yana kallonta ido suka hada hakan besa ta daina hararsa ba………..Yanayin fuskarsa kawai ya gyara ba tare da yace mata komai ba ya janye idonsa.

Hakan da yayi ya ‘bata mata rai sosai! wato ya ma mayar da ita mahaukaciya, tsaki taja mai tsayi ta kawar da fuskarta.

Beyi niyyar kula taba amma tsakin da tayi masa yasa ya kalleta cikin shan mur! yace.” Wa kikewa tsaki.”?

Kallon gefen ido tayi masa ta sake jan wani tsakin! ba zato! ya matseta jikin motar! lebunan ya kama ya shiga ligwigiwitasu! hawayen azaba! suka fara sauka saman fuskarta, Asp ya kalleshi da fadin.” Ka kyaleta haka mana.”

Ad

_____

Previous page 1 2 3 4Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button