GOJE

GOJE 37 and 38

Murmushi yayi yana sake jin kaunar yaron a cikin zuciyarsa, yace.” UMARU kenan addua kam zan cigaba dayi muku har karshen numfashina amma ba kaji bahaushe yana cewa (yaba kyauta tukwici ba) ba don kada nace na baka auran yarinyar nan ka dawo min da kyautata ba to dana baka ita sakamakon alkairin da kayi min.”

Fadar tayi shuru sakamakon maganar.

Kasa d’ago kansa yayi ballanatana ya nuna rashin amincewarsa da kyautar da akayi masa…………..Jin beyi magana ba yasa yace.” UMARU kodai baka kar’bi wannan kyautar tawa bane.”? Asp da sauri yace.” Aa haba dai! ranka ya dad’e wane mutum! kyautar mutum ba karamin al’amari bane sosai ni naji dadin wannan al’amari kuma kayi kyautar akan ga’ba domin dama bashi da aure a halin yanzu mungode sosai da wannan karamcin.”

Fuskarsa cike da annuri yace.” Asp ka ari bakinsa kaci masa albasa amma yanayinsa ya nuna kamar beyi na’am da wannan kyautatar tawa ba.”

Yayi namijin ‘ko’karin kawar da damuwarsa kansa ya dago tare da kokarin aro walwala da farin ciki yace.” Ranka ya dade farin ciki ne ya hana ni iya magana, tabbas abunda abokina ya fada hakane kayi min kyauta akan ga’ba kuma na kar’ba hannu biyu nagode kwarai da wannan karamcin.”

Ya sauke ajiyar zuciya a fili yace.” Alhamdullihi Allah abin godiya, lallai babu shakka ZINATU tayi dace da miji irin wanda yake da wahalar samu ina rokon Allah ya tabbatar da alkairin dake cikin wannan al’amarin.” Gabad’aya suka amsa da “ameen ya Allah.”

Free pege zai ‘kare a pege 40 masu payment kawai nake da bukata idan kin san na siyan littafin nan za kiyi ba kada kiyi min magana馃檹馃徎

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button