Atiku AbubakarLabarai

Daga ƙarshe an bayyana wanda Atiku Abubakar ya ɗauka a matsayin mataimaki

Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, zai bayyana wa al’umma wanda ya ɗauka a mataimakin sa a yau da rana a birnin tarayya Abuja.

Zaa sanar da zaɓin Atiku Abubakar yau da rana

Na kusa da kamfen ɗin sa sun bayyana cewa zaa gabatar da sanarwar da misalin ƙarfe 12 na ranar yau, sannan daga bisani kwamitin tantancewa da aka kafa zai tantance wanda aka zaɓa ɗin.

Hakan ya biyo bayan kammala tarurruka da dama da su ka gudana a daren ranar Laraba tsakanin ɗan takarar da kuma shugabannin jam’iyyar akan lamarin.

Ifeanyi Okowa shine zaɓin Atiku

Jaridar PREMIUM TIMES ta samu cewa gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a safiyar ranar Alhamis, shine zaɓin Atiku na ƙarshe.

Indai ba wani sauyi aka samu ba daga ƙarshe, Okowa shine wanda zaa bayyana da safiyar nan. Wata majiya mai ƙarfi ta shaidawa Premium Times.

Amma kamar yadda kuka sani, a siyasa minti ɗaya lokaci ne mai tsawo wanda komai na iya faruwa a cikin sa.

Paul Ibe, kakakin ofishin sadarwa na Atiku, ya ƙi yayi magana akan wanda aka zaɓa a matsayin mataimakin, inda yake cewa a jira har sai an bayyana a hukumance.

Abinda zan iya cewa kawai shine Atiku ya ƙosa ya kammala zaɓar mataimaki domin tunkarar aikin da ke a gaba na korar APC daga kan madafun iko. Tabbas zaɓin sa zai faranta ran ‘yan Najeriya

Jam’iyyar PDP dai ta kafa wani kwamiti domin nemo wasu da ake tunanin tsohon mataimakin shugaban ƙasan zai zaɓa daga ciki.

Duk da rahotanni da su ka fita a ranar Talata cewa kwamitin ya bayar da shawarar a zaɓi gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, shawarar ɗaukar ta sa ba ta samu ƙarbuwa ba sosai a wajen da yawa daga cikin shugabannin jam’iyyar.

Shugabannin na jin cewa Wike bai cancanci samun muƙami a kusa da kujerar shugaban ƙasa ba.

Da yawa daga cikin su sun yi ƙorafin zafin rai irin na gwamnan, kama karya da kuma saurin takalar faɗa ciki kuwa har da abokan ƙawancen sa.

Wasu na ganin Mr. Okowa yafi ƙwarewa da sanin makamar aiki kuma zai yi abin a zo a gani idan har ‘yan Najeriya su ka zaɓe su.

Hakan ya sanya hankalin Atiku ya tafi wurin ɗaukar Mr. Okowa wanda dama tun asali shine zaɓin sa.

Mr Okowa ya marawa Atiku baya a zaɓen fidda gwani inda Wike ya zo na biyu a zaɓen.

Bayan an bayyana shi ga al’umma a ranar Alhamis, Mr Okowa zai bayyana a gaban kwamitin tantancewa na jam’iyyar.

Jam’iyyun siyasa suna da wa’adin daga nan zuwa ranar Juma’a 17 ga watan Yuni, 2022 domin miƙa sunayen ‘yan takarar su a zaɓen 2023 ga hukumar zaɓe mai zaman kanta ta INEC.

Asali LabarunHausa

 

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button