HALIN GIRMA 31-35

“Amarya barka da rana.”
“Barka dai, ai ban ma lura ba, ina wuni?”
“Lafiya lou wallahi, dama wannan gajiya da kuka kwaso, dama
munyi waya dashi ne yace na biyo ta makarantar taku sai mu wuce, zasu sauka da
karfi shida da rabi, sai mu dauko shi a airport, amma fa yace kar na fad’a miki
dan wai so yake yayi surprising dinki.”
Dariya ta saka
“Lallai, ina ta tambayar sa yaushe zai dawo yaki fad’a min,
so yayi kawai yanzu ma sai dai na ganshi kenan.”
” Ai irin wai surprise din masoya.”
Dariya kawai tayi, bata kawo komai a ranta ba, ganin Musaddik
ne, haka kuma sai taji wani yanayi na dokin ganin mijinta, wanda yau ya cika
sati uku da kwana biyar cif da tafiya. Hanyar airport din suka dauka, ta
kwantar da kanta a bayan da yake saramata sosai.
**A word of encouragement to All TTC mother’s (Trying to
conceive) do not lose hope, Allah yana tare daku, ku cigaba da addu’a, Allah ya
baku ‘yaya masu albarka da mu baki daya. Baa debe tsammani daga rahmar Allah.
[ad_2]