HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 31-35

“Na zata zai barni na kwana.”

 

“Kul… Dududu yaushe akayi auren? Kar ma ki soma yi masa
maganar kina ji na? Watarana da kanki zaki zo ma”

 

” Wuce muje kar suyi ta jira.” Tace tana sakata a gaba
suka fito falon, uban kaya ne jibge a gefen falon dangin su shinkafa kayan
abinci dai masu yawa, Mummy na zaune tana juya kudi a hannun ta

 

” Kinga wahalar da yayi ko? Kiyi masa godiya nace ba za’a
karba ba amma ya dage dole.” Tayi maganar tana ajiye kudin a saman center
table, bin kudin Iman tayi da ido wanda a kalla zasuyi hundred thousand, sai
kayan abincin da yake a dankare awajen, jinjina kanta tayi cike da mamakin sa,
ko alama be nuna mata ba balle ta gane shirin sa, dadi ne ya kamata ta fito
bayan sun yi sallama da Mummy tana zuba masa ido ta cikin hasken compound din
gidan, duk da motar tint ce, amma tana iya hango inuwar sa, cike da karsashi ta
karasa wajen motar, dai-dai lokacin da kofar ta bud’e, ta shiga da sallama tana
dagawa su Iman hannu.

   Suna fita daga gidan ya matso kusa da ita cikin
lallashi yace

 

“I’m sorry na hanaki kwana, kinga gobe da wuri zamu tafi
amma next time da kaina zan kawo ki har sai kin gaji.”

 

“Laa ba komai fa, dama wasa nake yi, su Mamma ma ba zasu
barni ba ai, wai dududu yaushe akayi auren?”

 

“Haka suka ce ko?”

 

“Eh…”

 

“Yawwa kin gani.”

 

“Babu komai fa, ni nama manta ma ma na tambaya, I’m
sorry.”

 

Ta kama kunnenta, zare hannun nata yayi yana jawo ta jikinsa.

 

” Thanks dear.”

 

****

Washegari suka dauki hanyar Kano, tun kafin su isa an gama gyara
musu gidan su, dama dai ba wani baci yayi ba saboda akwai masu aiki da kula da
gidan banda sojojin da suke waje suna gadi, suna isa ya fice tare da Musaddik,
anan ta tarar da uban kayan lefen ta, tayi zaman kallon su cike da mamaki, idan
kaya na yawa toh ita dai sun mata mugun yawa, ya zatayi dasu? Shine kuma har da
siyan mata wasu kayan saboda dai ba’a san wahalar kudin ba. Gajiya tayi da
kalla ta saka masu aikin suka kwashe su, suka maida su wani daki guda kafin ta
kira Mamma taji abinda ya kamata tayi dasu da mutanen da ya kamata a bawa.

   Slippers ta zura ta zazzagaya gidan nata, wanda
yasha kaya na alfarma, har da wani babban garden a baya da pool daga chan gefe
shima, gidan yayi kyau amma yayi girma ace mutum daya kwal dan ma ma’aikata
masu yawa wanda yawanci daga masarauta suke sai wanda aka turo su daga adamawa.
Daki ta koma ta haye gado tayi kwanciyar ta dan bata jin yunwa tasha cornflakes
suna zuwa sai kawai ta kwanta da niyyar ta tashi wajen azahar ta dafa masa simple
dish dan wata gajiya take ji na nukurkusar ta.

   Ta jima batayi irin baccin da tayi ba, ga sanyin
AC da kamshin fresheners masu dadin kamshi da ya cika dakin, hakan ya kara
taimaka mata jin dadin baccin sosai har sai da taji ana mata knocking sannan ta
tashi bakin ta dauke da addu’a ta yane kanta ta fito ta bud’e kofar, daya daga
cikin masu aikin ce Atine, ta russuna ta gaishe ta sannan tace tayi baki ne a
falo. Ok tace ta rufe kofar ta koma ta gyara fuskar ta, ta fesa turare ta dauko
wayarta ta fito. Yan mata ne su biyu kyawawa dasu masha ALLAH, suna zaune suna
kallon TV ta fito,

 

“Sannun ku da zuwa.”

 

“Yawwa.” Suka amsa a sake, suka gaishe ta sannan suka
gabatar mata da kansu

 

“Fulani ce ta aiko mu, kayan gara ne dangin su alkaki dasu
bakilawa da dublan, sai gireba da sauran su, tace gashi nan zaku iya tayin baki
tunda kun dawo.”

 

“Kai mun gode sosai, Allah ya saka da alkhairi.”

 

Ta tashi ta bubbude, ta dawo ta zauna tana murmushi ta sake
godiya, aikin gidan mace ne kayan gara amma basu bari anyi mata ko daya ba,
dama tasan dai ko za’a yi sai dai a gayawa su Mamma suyi mata sai gashi sunce
ba sai anyi ba,itama yar su ce kamar Muhammad din.

   Hira sukayi sosai tun tana nokewa har ta saki
jiki dasu dan suna da hira ga faram faran kamar sun saba. Tare suka ci abincin
da suka zo dashi alkubus da miyar taushe, suka bita kitchen da zata yi ma Moh
dan abincin sa, suka tayata sai yamma suka tafi, bayan sun mata alkawarin zasu
dawo basa so ya dawo ya same su dan tsaf zai kore su, jin su kawai tayi dan
batayi tunanin zai aikata ba, bata san yadda yake tsare musu gida da daure
fuska bane shiyasa har yake mamaki dan sun ce ba zasu zauna ya same su ba.

   Suna fita kuwa sai gashi ya shigo, yaga fitar
motar su amma basu tsaya ba suka kara mai. Bud’e hannun sa yayi ya tsaya daga
jikin kofa, ta tafi a sanyaye ta fad’a jikin sa, ya rungume ta yana shafa
kanta.

 

“Sannu da zuwa yallabai.”

 

Ta karbi rigar hannun sa suka rankaya cikin falon, sai da ya
zauna sannan ya amsa mata sannun ya dora da

 

“Baki kikayi?”

 

“Su umaima ne, daga chan gida aiko su.”

 

“Yan rawar kai, tun yaushe suka zo?”

 

” Wajen twelve din rana.”

 

” Ah kice kin samu yan hira ko nace yan surutu dan bakin su
sam baya shiru.”

 

” Naji dadin zuwan su kuwa, sun tayani hira ai.”

 

” Sun kyauta da suka tafi kafin na dawo, dan tsaf zan saka
yarinya frog jump ba abinda ya damen.”

 

Ya fad’a yana kai cup din ruwan da ta zuba masa bakin sa,

 

” Da gaske wai?”

 

” Da gaske mana, suma sun sani ai, kila ma sun fada miki
ko?.”

 

” A ah.” Tace tana dariya

 

” Ya yau din? Ya gidan naki?”

 

” Alhamdulillah, komai yayi Masha ALLAH, Allah ya kara
arziki, thanks for everything,

 

” Amin Amin, I’m glad you like it.”

 

Yace cikin jin dadin addu’ar ta

 

” I love it!”

 

” Masha ALLAH.”

 

***Tun ranar farko da Bashir ya samu damar shigowa dakin har
yayi abinda yayi, tun daga lokacin duk dare sai ya lallabo, ranar farkon tana
jin su suka haura sama da uwargidan tasa suka fado, sai da k’yar suka daidaita
dan shima jan wuya yayi mata ganin idan ta biye masa zai iya cewa su rabu yasa
ta kyale shi, taga kansa rawa yake ya samu yarinya karama shiyasa ta kwantar da
kanta ta cigaba da bin sa tana so taga iyakar limit din iskancin nasa, tasan
sarai yana zuwa dakin da dare amma ta share bata taba nuna masa ba, wani zubin
ma akan kunnenta komai yake faruwa amma ta daure dan plan dinta akansa ba na
yanzu bane, shigo shigo babu zurfi tayi masa sai ya gama sakankancewa zatayi
maganin sa.

   Ranar ma kamar yadda ya saba kawo mata waya suyi
magana da Mama haka ya kawo mata, ta karba tana daga kwance da babu wani aiki
da takeyi yanzu matar gidan ta rage takura mata, dattijuwar me aikinta da ta
tafi gida ta dawo shiyasa aikin ya rage mata sai dai taci ta kwanta ga uban
kasalar da take fama dashi ga shegen nacin Bashir da yake hanata sakat, tana
shan wuya sosai a hannun sa dan baya daga mata kafa ko kad’an, tun tana masa
rashin kunya har tazo ta kyale shi yayi uwar da zai yi, ranar da zata samu
hanya kawai take nema wallahi ta tafi ba zata dawo ba ko me za’a yi mata kuwa.

  Wayar ya mika mata bayan ya gama amsawa da toh, suka
gaisa da Mama ta take fad’a mata haihuwar Aunty Bilki, tayi murna sosai ana
take jin gobe suna kuma a gidan su za’a yi sunan saboda akwai fili sosai

 

“Ki lallaba shi ya kawo ki na dai gaya masa.”

 

“Toh shikenan, zan kira.” Ta katse wayar ta mika masa

 

“Dan Allah ka barni naje suna gidan mu gobe.”

 

“Ki shirya da safe zan mika ki sai na wuce garari na, idan
na gama sai nazo mu dawo.”

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button