HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 31-35

“Good girl.”

 

  Yace yana mata murmushin mugunta. Janye blanket din
tayi, ya zuro kafafun sa k’asa yana mika mata hannu, kama hannun tayi ya tashi,
yayi kamar zai fadi ya fado jikin ta, nauyi sosai taji, amma ta daure dan taga
take taken sa zai iya cewa ya fasa, a haka suka isa toilet din, ya zauna a
gefen bathtub din ta hada ruwan, ta dauko masa brush da toothpaste ta matsa
masa ta bashi, kin karba yayi ya bud’e mata bakin wai tayi masa, sake mika masa
tayi ya noke yana tashi alamun zai bar toilet din, da sauri ta riko shi, ya
koma ya zauna ta fara yi masa, dariya ce take kamashi amma ya kanne, yadda ta
daddage kawai zai baka dariya, hannun sa ya dora a saman nata ya karbi brush
din, ya karasa, ya bata ta cilla shi a dustbin din toilet din daga nan tayi
hanyar fita

 

“Kina fita zan fito nima.”

 

Tsayawa tayi ta dawo tana tura baki, ya hau cire kayan sa a
gaban ta, tayi saurin juyar da kanta, murmushi yayi ya shiga ruwan da yayi masa
daidai da yadda yake so, sai data tabbatar ya shiga ciki sannan ta juyo tana
cigaba da dauke kanta ta dauko sponge da sabulu ta bud’e ta ajiye a dan wajen
da aka tanada, zama tayi a gefen bathtub din,  taki kallon gefen sa ta
juyar da kanta gaba daya hanya, bata yi aune ba taji ya jawo ta cikin ruwan, ta
saki kara, ya hade bakin su waje daya ya hana karar tata tasiri.

 

   Sai da suka bata lokaci mai tsawo a ciki sannan
suka fito, ta dinga turo baki tana jin kamar tayi masa kuka, ta riga ta gama
shiryawa tsaf har kayan da ta saka dama su tayi niyyar sawa amma ya jawo sai ta
sake sabon shiri, a wajen shiryawar ma haka tayi ta fama dashi da ya janye mata
towel ta nan sai ya janye mata ta nan haka dai yayi tayi har sai data gama cika
fam, zata fashe kafin ya kyaleta su shirya a nutse.

   Kasancewar ciki da falo ne dakin, sai tayi
ficewar ta, ta barshi a ciki yana karasa shiryawa ta hada masa breakfast din ta
ajiye da yazo ci kawai zai yi su tafi. Da waya a makale a kunnen sa ya fito,
yayi zaman amsa wayar da ta fuskanci da Musaddik suke magana, sai da ya gama
wayar tsaf sannan ya jawo abinci ya soma ci a yangace kamar ba jiran sa take
ba, bata dai ce komai ba, ya gama duk bata lokacin da zai yi, sannan ya tashi
yana goge bakin sa da tissue. Tashi tayi itama dama tayi ready har da jakarta a
kusa da ita, gaba yayi ta bishi a baya, ya murda kofar sojan da yake jiran sa a
wajen ya karbi Notepad da wayoyin sa, shi kuma ya zuba hannuwan sa a aljihu
suka shiga takawa zuwa wajen da aka tanadar domin parking motoci.

   Bud’e mata kofa yayi, ta shiga ya rufe sannan
shima aka bud’e masa nasa bangaren ya shiga suka fita daga harabar hotel din!

 

Bashin Jiya….so sorry banajin dadi ne

 

_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

 

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*

_SO DA ZUCIYA_

 

*_SAFIYYA HUGUMA_*

_DABI’AR ZUCIYA_

 

*_MAMUH GEE_*

_DEEN MARSHALL_

 

*_HAFSAT RANO_*

_HALIN GIRMA_

 

*_BILLYN ABDULL_*

_TAKUN SAKA_

 

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇

D’aya 300

Biyu 400

Uku 500

Hudu 700

Biyar 1k

 

*_Zaku tura kudin a_*

 

6019473875

*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*

*keystone bank*

 

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

 

08184017082

 

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

 

09134848107

2/12/22, 11:07 – Buhainat: Halin Girma

      32

 

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

 

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

 

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

 

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

 

*******�

 

Address din drivern ya dinga bi har suka isa gidan, tun kafin
motar ta gama daidatuwa a harabar gidan take kokarin fita, chapko ta yayi yana
bata fuska

 

“I’m jealous!”

 

Da mamaki dake kallon sa

 

“Yes I’m jealous, I want my share of love too, inaso naga
same action na murna anytime mukayi nisa da juna, inason soyayya, inaso a
gatata ni, aji dani sannan a damu dani please.”

 

Dariya ma ya bata, ya saki hannun ta yana sake bata fuska shi a
lallai yayi fushi, girgiza kanta tayi cikin muryar lallashi tace

 

“I’m so sorry toh, kawai I’m eager ne, ban wani zauna dasu
sosai ba, shiyasa kawai.”

 

“Shikenan reason din?”

 

“Shikenan, ko baka so naga Mama ta? Kullum fa kai kana tare
da Ammi fa, nifa?”

 

“Ba haka bane, banda Mummy ai nake nufi, Mamma, Amaani,
Amaan and rest, su nake kishi dasu.”

 

Dariya ta sake yi, ta rik’e kofar ta bud’e, ya zuba mata ido kamar
bashi da niyyar fitowa, sai da tayi masa alamar da hannu sannan ya bud’e ya
fito ta dayan side din, yana karewa gidan kallon.

   Kofar shiga part din suka nufa, yana biye da ita
a baya hannun sa sakaye a cikin aljihun sa, daf da zasu kai kofar ta bud’e,
Amaani ce a gaba da shegen gudu, tayi kanta tana ihun wallahi itace, kamar zata
kada ita, sai da k’yar ya nutsu tana numfarfashi, hango shi da tayi a baya sai
kawai tayi wajen sa , ta rik’e masa hannu ta fara zuba masa surutu kamar tayi
shekara da sanin sa. Cike da sha’awa yake duban ta, ta rik’e shi gagam har ciki
tana bashi labarin da be gane kan sa ba.

  Mamma ce ta fito daga wani corridor, tana sanye da
lullubi akanta, fuskarta cike da farin cikin ganin su,

 

“Sannun ku da zuwa.”

 

Tace sanda ta karaso falon, idon ta akan Iman dake zaune da
Amaan a kusa da ita. Russunawa yayi cikin ladabi ya gaida Mamma din, a daidai
lokacin Mummy ta fito itama, ya gaishe ta a kunyace dan kallo daya yayi mata
yaga tsantsar kama da Fatin sa, amsawa tayi ita din ma a yanayin kunya irin
tamu wadda aka gada tun iyaye da kakanni. Iman ce ta gaishe ta,  ta amsa
daga tsaitsaye ta juya ciki, murmushi kawai Mamma tayi dan tasan yadda ta matsu
da zuwan nasu, amma ba zata taba nunawa ba, yadda tayi zaka dauka ma bata damu
ba sam,nan kuwa tsantsar kara ce irin tata da har take nema tayi yawa.

   Abinci aka shiga jere musu, yayi mata alama da
ido akan tafiya zai, ya dauki bottle water guda daya ya mike yayi musu sallama
akan zai dawo, mamma ce ta hau korafin me zai sa ba zai tsaya yaci abinci ba,
hakuri ya bata akan zai dawo akwai wanda yake jiran sa ne. Shikenan tace ya
fice ta harari Iman

 

“Haka ake wa miji? Tashi mana kije kiji.”

 

Tashi tayi tana dariya, ta bi bayan sa ta same shi har ya kai
wajen mota, tsayawa yayi ganin ta fito ya choge jikin motar sai data karaso
sannan ya shiga, ya sauke glass din motar yana kallon ta

 

“Kwana zanyi ko?”

 

“Inji waye? Da yamma zan dawo zuwa magriba.”

 

“Dan Allah…” Girgza mata kai yayi tun kafin ta
karasa.

 

“Zaki dawo next time, sai na dawo bye.”

 

Ya daga glass din ta dan ja baya tana kallon motar har ta fice
daga gidan, kamar zatayi kuka haka taji, taja kafarta a hankali ta koma ciki ta
samu Mamma ta zuba mata abincin mummy kuma ta dawo falon ta zauna tana wa
Amaani fad’a akan rawar kanta.

   Taji dadin zuwan ta gidan sosai, kamar tayi ta
zama haka taji, amma tasan tun da yace zai dawo toh zai dawo din, amma taso ya
barta ko zuwa da safe ne sai yazo su tafi ko ya turo a dauke ta.

  Ta idar da sallar magriba kenan a dakin Mummy, Amaani ta
shigo tace ya dawo, har ga Allah taji babu dadi, ta tashi ta nannade sallayar
ta ajiye a gefe ta zauna a saman sofa tana ciro wayarta. Tana zaune har wajen
minti talatin babu wanda yazo kiranta, har ta kishingida sai ga Mamma ta shigo,
tace ta tashi su tafi yama fita,

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button