HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 31-35

“Tashi ki shirya akwai dinner da Chief of Army Staff, da
sauran manyan soldiers na k’asa, a madadin wanchan event din kawai aka hada
wannan dinner din kowa da family nasa.”

 

” Owk.” Tace tana mikawa, ya nuna maya ledar da hannu
yana shigewa toilet. Daukar ledar tayi me dauke da tambarin wani babban Mall,
ta bud’e doguwar riga Abaya ta gani me kyau, ciro ta tayi tana ware ta, sosai
tayi mata kyau ta ajiye a gefe ta ciro sauran tarkacen kayan hadda wata kar
karamar jaka da tafi kama da purse sai takalmi hills amma ba chan ba. Shiryawa
ta hau yi tana yi tana kallon toilet din har ta gama be fito, ta matsa wajen
yar trolley dinsu da ciro perfumes ta faffesa sannan ta zauna tana dauko
wayarta da take haske alamun kira ne ya shigo, Mamma ce, tasan cewa zatayi taji
su shiru,ita kanta batayi tunanin nan din zasu zarto ba dan tasan an gama
shiryar su kada ma Mamma taji labari tasan ba zata huta ba har sai sun iso.
Dagawa tayi daidai lokacin da ya fito daga shi sai gajeren wando, faffadan
kafadarsa ta kalla da take a mummurde, ta sauke kanta tana jin wani yanayi da
bata san na menene ba, a gabanta ya tsaya yana rik’e k’ugu, yana, hannun sa
daya rik’e da karamin towel, ganin ta dauke kai kamar bata ganshi ba, ya saka
shi yarfa mata ruwan da yake hannun sa a fuska, yi tayi kamar zata tashi amma
da daure ta cigaba da wayar, ta bawa Mamman hakuri yana ji ta gama ta ajiye
wayar tana tashi da sauri.

 

“Kinyi kyau Matar Muhammad.”

 

“Nagode.” Tace a kunyace bubbude hannayen sa yayi, ya
ja baya yana tattare fuskar sa.

 

“Shirya ni…”

 

“Na’am?”

 

“Eh ki shirya ni, ki shafa min mai ki saka min
kaya…”

 

“Kamar dan baby?”

 

“Toh da mene? Ai babyn naki ne ni.”

 

Dariya ta saka tana sake gyara zaman ta

 

“I’m serious fa, kinga we are running late, kar suyi ta
jiranmu.”

 

Ganin da gaske yake, ya sakata tashi ta dauko man, ta shiga
shafa masa yana lullumshe ido, da gangan ya dinga sata komawa baya yana cewa be
yi ba, nan fa. Da dai daga alamun so yake ayi tayi sai ta tattara man ta mayar,
ta dauko masa suits din da ta gani tare da abayar ta, ta mika masa ya noke yana
sake bararrajewa. Girgiza kai tayi, ta shiga saka masa, yana sake narke mata
kamar wani karamin yaro a gaban mahaifiyar sa, sai data gama tas ya rage saura
necktie sannan ya karba ya karasa sawa a gaban mirror, ya kalli kansa yana
hango ta ta cikin mirror din,da hannu yayi mata alamar tazo, ta tako ta tsaya
daga kuibin sa, ya matso da ita jikinsa yana kara kansa a jikin fuskar ta.

 

“Perfect!” Yace yana dariya, wayar sa dake kusa da
wajen ya dauka, yayi musu hoto me kyau a gaban mirror din, sannan ya daga kiran
da George yake masa.

 

“We are on our way.”

 

Kawai yace ya katse kiran, ya rik’e hannun sa cikin nata suka
fito, duk da suka hauro reception din suke shan kallo, tana jin shi yana jan
tsaki k’asa-k’asa har suka shiga wajen da yake a cikin hotel din ne dalilln da
ya saka ma suka sauka anan din kenan saboda already an riga anyi booking dakin
tun kafin ranar ma. Duk in da suka wuce sojoji ne a tsaitsaye sun yi shirin ko
ta kwana, cikin girmamawa suke gaida su, har suka kai babbar kofar shiga wajen.

  

    Wata iriyar kunya ce ta dabaibaye ta lokacin da
suka shiga wajen, mutane ne masu yawa kai kace wani gagarumin biki ake, kowacce
kofar shiga wajen dankare take da jami’an tsaro, ji tayi ido yayi mata yawa,
gashi duk sun tashi da shigowar su. Mafiya yawancin su ba hausawa bane, sai yan
daidaiku da tayi hangowa daga in da take. Wajen zaman su waitress dake tsaye a
wajen ta nuna musu, basu wuce chan ba kai tsaye sai da suka je wajen manyan
kusoshin, suka kwashi gaisuwa in da taga yayi wata irin gaisuwa tasu ta daban,
sannan suka samu wajen zama suka zauna sai a lokacin ya sakar mata hannu.

 

“Sannu Amarya!”

 

Wata bahaushiya a kusa da ita tayi mata magana, amsawa tayi tana
maida mata murnushin da tayi mata, sai kuma suka gaisa da sauran matan wasu
hausawa wasu ba hausawa ba, kafin kuma a fara gabatar da abinda ya hada su.

  Captain Is’mail ne a gaba gaba akan komai shi da George,
su ne ma organizers din event din shiyasa ko zama sun kasa yi, har sai da
lokacin cin abinci yayi sannan suka zauna shima na wucin gado,ana gama ci aka
cigaba da gudanar da event din. Sun sha kyaututtuka sosai har sai da Iman ta
gaji da karba, idon ta yayi nauyi kwanciya take so kawai yayi, yana lura da
ita, yasan ba karamin aikin su bane su kai fiye da biyu a wajen babu kuma wanda
zai damu, ita kuwa akwai rashin sabo, tashi yayi yana zura hannunsa cikin
aljihun wandon sa, ya nufi wajen da Is’mail yake ya jashi gefe, yayi masa
magana kana ya dawo wajen zaman sa ya zauna. Sai da aka kara kamar mintuna
ashirin sannan isma’il din ya bada sanarwar amarya bata jin dadi zata je ta
huta, da haka suka samu suka sulale daga wajen suka nufi masaukin su. Dukkan su
a gajiye suke dan haka babu abinda suka kara bayan sauya kayan jikin su sai
bacci, cikin kankanin lokaci bacci yayi awon gaba dasu.

 

    Da wuri ta tashi, ta shirya ta zauna tana duba
lokaci, baccin sa yake tsakanin sa da Allah tun bayan dawowar sa sallar asubah
gashi ta matsu ta ganta a gidan, gashi babu alamun zai tashi har past 10, an
kawo musu breakfast daga reception din taci kad’an ta ajiye masa sauran ta
cigaba da zaman jiran sa. Wasa wasa lokaci ya dinga ja, babu abinda yake sai
chanja kwanciya da juyi daga nan ya koma nan cikin jin dadin baccin. Ganin da
gaske ba zai tashi ba, ya sakata zuwa daidai saitin kansa, ta dan rankwafa da
niyyar tashin sa, hannu takai kan sajen fuskar sa, ta taba kadan, juyi taga
yayi ya sake maida kansa dayan barin, sake durkusowa tayi ta bayan nasa ta kai
hannun ta jikin sa, kam taji ya riko hannun ya makale shi tsakanin hannun sa da
jikin sa, ja tayi taji ya makale shi kam, gashi sauran kad’an ta fado kansa
gaba daya, dayan hannun ta saka ta taba shi,

 

“Please ka tashi zamu makara.”

 

“Uhum…” Yace cikin muryar dake cike da nauyin bacci,
ya sake kankame hannun nata a jikinsa wanda ta jawo mata fadawa kansa ta gefe
daidai saitin bayan sa.

   Sun jima a haka tana jin shi yana fitar da
numfashin bacci, kafin yayi motsi ya bud’e idon sa da suke cike da bacci sosai,
ya juyo bangarenta yana sakin hannun nata.

 

“Ka tashi dan Allah.”

 

“Um um…”

 

“Ka manta zamu fita?”

 

Da kai ya amsa mata da eh, kokarin tashi tayi zaune ya daddanne
ta, ta hanyar dora kafarsa a jikin ta

 

“Kinsan fa jiya bamuyi wani bacci ba, please muyi bacci
idan muka tashi sai mu fita.”

 

“Past eleven fa, please please please.”

 

“Ohhhh! Ni dai gaskiya, gaskiya bacci nake so nayi, anjima
sai muje idan mun tashi, bari kiga.”

 

Ya sake kadannade ta da kafafun nashi da sukayi mata nauyi ta
kasa janye su,gani tayi yana maida idon sa zai rufe tayi saurin rik’e fuskar sa

 

“Dan Allah!”

 

“Shikenan.” Yace yana sauke kafarsa, ta samu ta mike
tana murmushi

 

“Amma da sharadi, ke zaki min wanka ki shirya ni, ki kuma
bani abinci a baki.”

 

“Ahhhh.” Ta bud’e baki cike da mamaki

 

“Fine, bari na koma bacci na sanda na gama mun fita.”

 

Da sauri ta rik’e blanket din da zai sake rufa

 

“Zanyi.”

 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button