HALIN GIRMA 31-35

***Tare suka shigo da Musaddik, wanda kallo daya zaka yi musu
kasan a gajiye suke sosai, babu wanda yayi magana sai da suka huta sannan ne
Musaddik ya mika masa wayar sa da ake ta faman kira tun suna hanya, karba yayi
ya daga yana kishingid’a a saman kujerar
“Ya akayi? Kun duba yadda abun ya samu kansa a cikin part
din?”
“Mun duba dukka CCTV footage na gaba daya area din, bamu ga
kowa ba a kusa da wajen ma, har zuwa kofar shiga shashen, falon kuma babu CCTV
kasan, time da za’a saka kace baka so. “
” Na sani, shikenan ba damuwa. “
Yace yana zare wayar daga kunnen sa, ya ajiye yana murmushi
wanda ya saka Musaddik kallon shi
” Akwai wanda yake so yayi wasa da hankali na, ko ma waye
yasan babu cameras a ciki, target din su iya na wajen ne kawai. “
” Me kake tunani? “
” I can’t say exactly, amma dai akwai wani abun daban ba
sarauta ba, ko ma waye yana da matsala da aure na, ba sarauta ba. “
” Laila fa? “
” Ba ita bace. “
” Toh me zasuyi benefiting anan, ban gane komai ba. “
” Guy, baka san wanne irin mutane ne suke zagaye da gidan
nan ba, da kuma kudurin kowa, zaka sha mamaki amma. “
“Ka sansu? “
” Almost.. “
” Then why are you allowing them to walk over you? Bayan
kana da duk damar da zaka yi musu abinda zakayi to get rid of them. “
” Ba zai yiwu ba, this is not a military war, wannan fad’an
ba ma makami bane, ko na gwajin kwanji ba, sai ka zama very very careful da duk
moves dinka, akwai bakin ciki a gidan sarauta, akwai kyashi, da hassada. Masu
son kujerar ba mutane bane yan kad’an, suna da yawa kuma kowa zai iya komai
domin ganin ya samu abinda yake so”
Gid’a kai Musaddik yayi yace
” It’s harder than i thought. “
Murmushi Moh yayi, ya hade hannuwan sa waje daya, suka fitar da
sauti me dan kara, ya mike yana zuba hannayen sa cikin aljihun sa
“Muje naga Takawa.”
“Owk.” Yace ya mike suka fita
***Be samu ganin Takawar ba kamar yadda ya saka rai, ya zauna
zaman jiran sa dan yana so ya nema masa alfarma akan tafiyar da za’a yi akan
wani aiki gashi har da sunan sa, baya son yayi nisa da gida dan a kalla zasuyi
wata guda cif, yasan idan ya samu Takawar ya kira waya za’a iya cire sunan sa,
duk da tun daga last yace ya daina nema masa alfarma, tun da shi yaji ya gani
dole ne yabi dokar aiki, sai gashi ya dawo yanzu be kuma san yadda zata kaya
musu ba, shi kansa kunyar neman alfarmar yake amma kuma baya son tafiya ya bar
Iman ita kadai bata gama sanin komai ba.
  Har sukayi la’asar suka dawo Takawan be dawo ba,
cigaba da zaman jiran sa sukayi Muhammad har da dan baccin sa,ya bar Musaddik
yana kallo dan dama shi mayen kallo ne. Sai goshin Magriba sannan suka ji
dawowar sa, alwala suka daura suka fita zuwa masallaci aka yi sallah,.
  Yadda ya dawo da irin wannan lokacin dama babu
wani zama da zai kara direct ya wuce gida dan yana bukatar ya huta sosai.
  Shawara sukayi akan kawai su dawo gobe da wuri
kafin ya fito zaman fada. Da wannan shawarar sukayi amfani suka tafi, suka wuce
kai tsaye gidan su Iman daukota. A ransa ya kuduri zai kaita ya nuna mata dakin
da ya zauna har ya kwana aciki saboda ita!
***Akwai Yayar su Abba da take turai tare da iyalin ta, sukan
dade basu zo ba yawanci sai dai waya suke yi, akwai dan ta Mahfuz zai yi sa’an
su Habib ko ya dan d’ara su da kadan, duk ciki shine me zumunci me son dangin
sa, tun da ya girma idan ya samu lokaci ya kan zo yayi wata biyu ko daya ya
koma, karshen zuwan da yayi ya jima sosai be dawo ba, sai wannan lokacin da
yazo. Yaso ya samu bikin da aka ce masa za’a yi, duk da ba wani sanin su yayi
ba saboda yawansu sai kuma aka samu yar matsala da ta dakatar da zuwan sai
yanzu. Yana da wasa sosai da sakin fuska , abu daya yake hada shi da kowa shine
yadda dabi’un sa da al’adun sa suka sha banban da na Malam bahaushe, gashi dama
bahaushe ko yaya ka kuskure wajen al’ada wadda ba irin tasa ba be kuma karbe ta
ba,toh fa zaka samu matsala dashi. Hakan ce ta kasance ga Mahfuz, yadda yake
mu’amular sa tasha banban da tamu, dole ne za’a ga banbanci wanda shi tsakann
sa har ga Allah ba da wani abu yake ba
 Tun da ya shigo falon ya dora idon sa akan Iman ya kasa
daukewa, be kawo matar aure bace sam, gefen ta yaje ya zauna daf har sai data
dan matsa, suka gaishe shi dukka ya amsa idon sa na kanta.
“You are beautiful.” Yace mata kan sa tsaye, gabanta
ne ya fadi, ta kalli Yaya Maryam ta kalli sauran yan dakin, sai kawai ta mike
tana tattare jakar ta.
“Bari naje wajen Gaji kafin ya zo.”
Bata jira amsar su ba tayi gaba, ya tashi da sauri ya bi bayanta
ya jera da ita yana yi mata surutu, da hausar sa da ba wani ganewa take ba,
tana shiga part din Gajin text din Moh ya shigo wayarta,
“Muna waje.” Yace a text din kawai, sallama tayi wa
Gaji kawai dan kuma babu zama, ta juya zuwa nasu gidan ta tarar da Zeenat a
zaune tana cin tuwo, nan ma tayi wa Maman sallama tace ta gaida gida. Fitowa
tayi rik’e da hannun Marwan, ta koma wajen su Yaya Maryam tayi musu sallama,
suka firfita zasu rakata, anan suke ganin ana sauke kayan abinci a irin motar
da Iman din ta gani dazu a gida, ranta ne ya bata lallai aikin sa ne, tana jin
su Maryam suna maganar sai dai idan shine ya aiko dan cikin surukan gidan babu
wanda zai aiko da kayan abinci haka masu yawa. Har gate suka rakata sannan suka
juyo, Mahfuz na ganin zata bita ya tashi ya sake bin ta suka rankaya
zuwa waje, kamar tace masa ya koma amma sai ta kasa tana jin nauyin sa. Tun da
suka fito idon Moh akan su, ya gama tabbatar da ba Habib bane, ba kuma Khalil
bane dan ba zai kara gangancin da yayi a baya ba. Ransa ne ya baci,
ganin yadda suke jerawa yana mata magana da yanayin yadda yake maganar. K’asa
hakuri yayi, ya balle murfin motar ya fito daidai lokacin da Mahfuz yake
kokarin kai hannu ya bud’e mata kofa, gashi yayi kusa da ita sosai.
“Dalla malam baka da hankali ne?” Ya daka masa tsawar
da ta saka Iman sakin yar jakar hannun ta, tsayawa Mahfuz yayi yana kallon sa
yace
“Pardon?”
Wani banzan kallo yayi masa, ya zagayo ya kama hannun ta, ya
jata zuwa dayan side din motar ya turata ciki, be lura ba sai data bigi ya rufe
kofar da karfin sannan ya dawo wajen Mahfuz din dake tsaye rik’e da jakar Iman
din da ta fadi cikin mamakin abinda ya harzuka gayen.
“Wannan shine last warning dinka akan matata, ko waye kai
komai alakar ka da ita, kar na sake ganin ka haka kusa da ita, idan ba haka ba
wallahi sai na balla kafarka, nonsense.”
Be jira abinda zai ce ba, ya bud’e motar a fusace ya shiga ya
rufo, Musaddik dake gaba ya juyo zai magana yaga yanayin sa, sai kawai yayi
shiru, yace ma driver ya ja, jan motar yayi suka bar wajen.
_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI’AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇